Tambaya (68)❓
Shin wanne sahabi
ne ya rawaito hadisin: Ar-Rahimun yarhama humurrahman
AMSA❗
Alhamdulillah
Abdullahi Ibn amr
bin al-As shi ne sahabin da ya rawaito hadisin; "Ar-Rahimun". To
amman ta yaya zamu tabbatar kuma mu gasgata cewar shi ne ya rawaito wannan
hadisin ?
Anan zamuyi duba
ne zuwa ga abinda Ahlul Hadis, Muhaddisun (Malaman Hadisi) suke kira da
Musalsal Hadis ma'ana hadisin da za'a zayyano sunayen wadanda suka karbo
hadisin tun daga wannan zamanin har zuwa shekaru 1,400 can baya da suka wuce,
wato tun daga yanzu zuwa zamanin Tabi'ut Tabi'un, zuwa Tabi'ai, zuwa Sahabbai,
kai tsaye daga bakin Annabi SAW
Shaikh Muhammad
Alyaqoubi, sharif daga kasar Syria, ya kasance jinin Annabi Muhammad SAW ne
Al-Yaqoubi
tsatson Mawlay Idris al-Anwar ne, (founder din birnin Fès), jikan Sayyadina
Hasan ibn Ali, jikan Annabi SAW. Kamar dai yanda Sarkin kasar Jordan na yanzu
(mai shekaru 61) wato Sarki Abdullah II Bin Hussein ya kasance bahashime, jikan
Annabi SAW na 41 (Kamar yanda Hashemite Kingdom of Jordan wato Masarautar Bani
Hashim ta Jordan kasar Jordan ta fitar a shekarar 2020 a cikin Magazine dinta
mai taken: 500 Most Influential Muslims In The World In 2020, ma'ana: Musulmai
500 masu ikon fada a ji a shekarar 2020)
Al-yaqubi ya
kasance yana karantawa mutane wannan musalsal hadis din. Wanda shi ne hadisi na
farko da a al'adance masana hadisi suke koyarda dalibansu domin fa'idantuwa da
sunayen marawaita hadisin. Haka kuma ana kiran hadisin da suna; Musalsal
haqiqatan bil awwaliyya
Ga sunayen
marawaitansa kamar yanda Shaikh Hamza Yusuf Hanson (Mai Zaytuna College,
California, Amurka) ya sanar damu;
Ana haddasani,
abul huda Muhammadul yaqubi, al-hasani, al-idrisi, ad-dimishqi, wahuwa awwala
hadisi sami'tahu minhu, qala haddasana, bihi shaikuna, al-allama, muhammad
al-makki, bin muhammad bin ja'afar al-kattani, al-hasani, al-idrisi, alfasi
ad-dimishqi, mufti al-malikiyyati, bi biladish sham, wahuwa awwala hadisin
sami'tahu minhu, qala, haddasana, as-said ahmad bin isma'il al- barzanji,
al-husaini, mufti shafi'iyyati bil madina almunawwara, wahuwa awwala hadisin
sami'tu minhu, qala, haddasana, waridi, isma'il bin zainul abidin albarzanji,
mufti shafi'iyyati fil-madinatil munawwara
Wahuwa awwa
hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, muhaddisil madinatil munawwara ash-shaik
saleh bin muhammad al-umari, al-fullani, al-maliki, wahuwa awwal hadisin
sami'tu minhu qal, haddasana shamsuddin muhammad bin muhammad bin abdallah
almagribi, al-madani, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana musnad
al-hijaz al-imamu abdullah bin sal al-basri al-makki, wahuwa awwal hadisin
sami'tu minhu qal, haddasana, alhafiz shamsuddin muhammad bin ala'addin salihal
babiri al-masri, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana shihabuddin
ahmad bin muhammad, ash-shibri al-hanafi, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu
qal, haddasana, jamaluddin yusuf bin shaikhal islam, zakariyya bin muhammad
al-ansari
Wahuwa awwal
hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, burhanuddin ibrahim bin ali bin ahmad
al-qalqashandi, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, shihabuddin
ahmad bin muhammad bin abi bakar al-wasati al-maqdasi, wahuwa awwal hadisin
sami'tu minhu qal, haddasana, shadruddin abul fath muhammad bin muhammad bin
ibrahim al-maidumi al-hambali, wahuwa awwal sami'tu minhu qal, haddasana,
musmilu masra abul-faraj abdallatif bin abdul-mun'im bin saiqal al-harrani
al-hambali, wahuwa awwal sami'tu minhu qal, haddasana al-hafiz ash-shahir abul
faraj abdurrahman bin ali al-ma'aruf bin aljauzi al-hambali
Wahuwa awwal
hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, abu sa'ad isma'il bin hafiz ahmad bin
abdulmalik an-naisaburi al-wa'is, wahuwa awwal sami'tu minhu qal, haddasana,
al-hafizul musnad abu salih ahmad bin abdulmalik bin ali an-naisaburi ash-shahir
bin mu'azzan, wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, musnid
naisabur abu-dahir, muhammad bin muhammad bin muhammad bin mahnish az-ziyadi,
wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, abu hamid ahmad bin muhammad
bin yahya bin bilal al-bazzaz al-mutawaffas sana salasa mi'atan wasalasina
Wahuwa awwal
hadisin sami'tu minhu qal, haddasana, shaihul fuqaha bi makkata abu muhammad
abdurrahman bin bishir bin al-hakam al-abdi wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu
qal, haddasani, amirul mu'umin sufyan bin uyaynata mutawafas sanata mi'a wa
samaniya wa tas'in wahuwa awwal hadisin sami'tu minhu qal, anat tabi'iyal jalil
abi muhammad amr bin dinar anat'tabi'il jalil abi qabusal mutawaffa ba'ada
mi'ati mawla sayyadina abdallah bin amr bin al-as anas sahabiyal jalil,
sayyadina abdullahi bin amr bin al-as qala, QALA RASULULLAHI SAW: AR-RAHIMUN,
YARHAMAHUMUR-RAHMAN, YARHAMU MAN FIL ARD, YARHAMIKUM MAN FIS-SAMA" wafi
riwaya: "YARHAMU MAN FIL-ARD YARHAMKUM BISH-SHARJ, YARHAMKUM MAN FIS-SAMA"
Sadaqa Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam. Alhamdulillah
A ruwayar
Tirmidhi kuma yazo kamar haka: An karbo daga Abdullahi Bin amr Bin al-As yace:
Manzon Allah SAW yace; "Ku nuna rahama a duniya, wanda yake a saman bakwai
zai nuna muku Rahama"
Jami' at-Tirmidhi
1924
Haka ma Muhammad
Nasiriddin Albany ya ingantashi a cikin; Jami' at-Tirmidhi hadisi mai lamba ta
1924
Jan Hankali; Ya
zama wajibi idan har muna son ganin daidai a al'amuranmu to mu fara saka Allah
SWT a gaba, muyi komai da ikhlasi mu nesanta daga riya, musamman yan kasuwarmu,
la'akari da sauran kasa da kwanaki 50 mu shiga watan azumi mai albarka. Kowa
yasan halin da muka tsinci kanmu na tsadar rayuwa kuma la shakka duk hakan na
faruwa ne silar munanan bayyanannu da boyayyun ayyukanmu
Taliyar Spaghetti
ta gida ta doshi N500, yayinda na tambayi ta kasar waje sai mai kantin yacemin
N700, a maimakon kayi raki, to anan kamata yayi ka roqi ar-Razzaqu ya azurta ka
da dukiyar da zaka siyawa wasu cartons
Dole sai mun
sauya sannan ne Allah SWT zai shigo lamarinmu, mu samu sauqin komai. Da ace
yanda muke complain akan tsadar rayuwa, haka muke complain akan zunubbanmu to
da munyi qoqarin hobbasa wajen gyarawa. Allah SWT ya fada a cikin Qur'ani mai
girma cewar;
( لَهُ
مُعَقِّبَاتٌ مِّن بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِ يَحْفَظُونَهُ مِنْ أَمْرِ
اللَّهِ ۗ إِنَّ اللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُوا مَا
بِأَنفُسِهِمْ ۗ وَإِذَا أَرَادَ اللَّهُ بِقَوْمٍ سُوءًا فَلَا مَرَدَّ لَهُ ۚ
وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِ مِن وَالٍ )
الرعد (11) Ar-Ra'd
(Kowannenku) Yana
da waɗansu mala'iku masu maye wa
juna a gaba gare shi da baya gare shi, suna tsare shi daga umurnin Allah. Lalle
ne Allah ba Ya canja abin da yake ga, mutane sai sun canja abin da yake ga
zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azaba game da mutane, to, babu mai
mayar da ita, kuma ba su da wani majiɓinci baicin Shi.
Don haka idan har
da gaske muna son shiga Aljannah to sharadin shi ne mu koma ga Allah SWT kamar
yanda ya fada;
( يَا
أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا تُوبُوا إِلَى اللَّهِ تَوْبَةً نَّصُوحًا عَسَىٰ
رَبُّكُمْ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَيُدْخِلَكُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي
مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ يَوْمَ لَا يُخْزِي اللَّهُ النَّبِيَّ وَالَّذِينَ
آمَنُوا مَعَهُ ۖ نُورُهُمْ يَسْعَىٰ بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَبِأَيْمَانِهِمْ
يَقُولُونَ رَبَّنَا أَتْمِمْ لَنَا نُورَنَا وَاغْفِرْ لَنَا ۖ إِنَّكَ عَلَىٰ
كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ )
التحريم (8) At-Tahrim
Ya ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku koma
zuwa ga Allah komawar gaskiya. Mai yiwuwa Ubangjinku Ya kankare muku miyagun
ayyukanku kuma Ya shigar da ku a gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu a ranar da
Allah ba Ya kunyatar da Annabi da wadanda suka yi ĩmani tare da shi.
Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, "Ya Ubangijiumu! Ka
cika mana haskenmu, kuma Ka yi mana gafara. Lalle Kai, a kan dukkan kome, Ya
kai Mai ikon yi ne."
Wallahu ta'ala
a'alam
Subhanakallahumma
wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.