Shawara Ga Amaryar Gobe

    TAMBAYA (56)

    Assalamu alaikum wa rahmatullah. Barka da wannan lokaci Mallam. Ya ayyuka, Allah yayi jagora ya Bada Lada Aamim. Mallam ba tambaya nikeda ita ba face Neman shawara, ni budurwace ansaka bikina Nanda wata Daya. Ina bukatan shawarwari zaman aure dareda addu'oin dazan kare aurena na kare mijina sannan na kare yarana idan Allah ya bani. Nagode Allah ya Kara basira

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

    To yar uwa, ina roqon Allah yayi miki albarka

    Sannan ina roqon Allah ya baki zaman lafiya dangane da zaman ibadar da zakiyi

    Allah SWT yace;

    ( وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ )

    الروم (21) Ar-Room

    Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.

    Haqiqa dukkan aure idan babu nutsuwa, soyayya da rahama to akwai lam'a a tattare da ma'auratan. Ana samun wadannan ababe 3 ne kadai idan aka yi koyi da yanda Annabi SAW ya mu'amalanci iyalansa

    Shawarar da zan baki anan itace; na farko dai ki ji tsoron Allah SWT, na biyu kuma ki qudurce a ranki cewar wannan aure da za ki yi akwai daruruwa ko ince dubunnai gwauraye maza da mata wadanda suke ta neman irin wannan damar amman Allah bai ba su ba, ga shi ke a yau kin samu

    Na uku, akwai wasu littattafai na addini guda 3 wadanda zan so ace kin karanta su a cikin nan da kwanaki 30 dinnan, kafin ki tare a dakin mijinki

    Sanin kanki ne cewar komai da zamu aikata saida musulunci ya koyar da mu, hatta shiga bandaki to ina kuma ga rayuwar auratayya wanda wallahu a'alamu a nan ne za'a samu shugaban kasa ko gwamnan gobe wanda zai jagoranci miliyoyin al'umma. Kinga kenan komai zaki gudanar sai an koma ga hadisai da suka yi bayani akan yanda Annabi SAW ya koyar da matan gidansa a lokacin rayuwarsa tare dasu

    Littafi na farko shine;

    1) Sifatu Salatin Naby PDF (Siffar yanda Annabi SAW yayi sallah, wallafar Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany (Rahimahullah)

    Ya suffanta tare da kawo bayanai daki-daki akan yanda Annabi SAW ya koyar da yanda ake sallah dogaro da hujjar hadisin "Sallu kama ra'ayta muni usalli" bi ma'ana: "Kuyi sallah kamar yanda kuka ga ina yi". Don haka ya zama dole ki mallaki wannan littafin kuma ki koyi sallah irin yanda Annabi SAW ya koyar. Kamar yanda kika sani cewar kowa yana cikin dayan biyu ne: immadai kana sallah ne a al'adance (kamar yanda ka taso ka ga ana yi) ko kuma kana sallah ne a addinance (yanda Ma'aiki SAW ya koyar)

    2) Guidelines to intimacy in islam (Shiriya akan alaqar auratayya a musulunce, wallafar Mufti Ahmad Ibn Adam Alkautary)

    Yayi bayani sosai kuma daki-daki akan yanda Annabi SAW ya koyar da al'ummarsa yanda ake rayuwar auratayya. Akwai makarantun da ake koyarda rayuwar zamantakewar aure a addinance irin makarantar: ZADUZAUJJEN. Ana koyarda (1) Yadda ake neman Aure a muslinci (2) Sanin Hakkin muji (3) Shagwaba ga miji ki mayar dashi kamar Jariri (4) Koyan Halayen da miji zai maida ke madubin sa ya zame miki kamar rakumi da akala (5) A koya Miki Yadda mahaifansa da Danginsa zasu Soki Babu Boka ba Malam (6) iya Tattalin Miji da Dukiyar sa da kuma Abubuwa masu matukar Amfani  Sannan ki zama Abin Alfahari mijinki duk bazaki San su ba sai kinje Zaduzaujjen. Registration: N4,000. Karkashin jagorancin Shaikh Prof. Umar Sani Fagge. Makarantar MANARU ISLAMIYYA FAGGE SPECIAL PRIMARY SCHOOL IBRAHIM TAIWO ROAD. (Kamar yanda naga sanarwan a group di na cewar program din na tsawon watanni 3 ne)

    3) Newborn baby guide (Shiriya ga Jarirai, wallafar Ibn al-Qayyim Aljauziyya (Rahimahullah)

    Ya rubuta littafinne a matsayin kyauta ga qanwarsa a lokacin da ba shi da ko da riga daya da zai bata a matsayin tukwici a lokacin da ta haihu, sai gashi Allah SWT ya albarka littafin ga shi muna amfana dashi. Yayi bayanai akan yiwa jariri kiran sallah, sakawa jariri suna, yin aski, kaciya, yanka da sauran bayanai dai da hujja a Qur'ani da sahihan hadisai, kai abin sai wanda ya karanta dai

    Sai kuma ki bawa angonnaki shawarar ya dafa goshinki da hannun dama sannan ya karanta addu'ar nan da Annabi SAW yace: Idan dayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, sai ya ce;

    اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.

    Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.

    "Ya Allah ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa"

    Sai kuma addu'ar da kike bida game da yaya idan Allah SWT ya azurtaki da samu anan gaba

    Amman abinda ya tabbata shine; an rawaito cewar Annabi SAW yana yiwa jikokinsa wato Hassan da Hussaini bin Ali (Allah ya kara musu yarda baki daya) wadda ta tabbata a cikin sahihan hadisai, kamar yanda Shaikh Sa'id Alqataani (Rahimahullah) ya kawo a cikin littafinsa na Hisnul Muslim (Asaka mawallafin littafin a addu'a domin kuwa a watanni baya ya koma ga MahaliccinSa)

    Inda yace: Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar (Harma yace babanku {Annabi Ibrahim AS} yana yiwa yayansa {Annabi Ismail da Ishaq} ga addu'ar kamar haka

    أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.

    "O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah"

    Bi ma'ana: "Ina neman muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa"

    (Duba Sahihul Bukhari hadisi mai lambata 3371)

    Sannan kuma kamar dai yanda na fada kwanaki tun ran gini tun ran zance, akan yi tuya a manta da albasa ma'ana mutane sukan manta da addu'ar da Annabi SAW ya koyar kafin tarawa da iyali, wadda rashin yinta kan iya kawo yiwuwar a haifi yaro kangararre ya zo ya dameku ya dami al'umma da shaidanci domin kuwa sakacin rashin neman tsarin Allah ne daman yasa shaidan kan shafi abinda Allah ya azurta ma'aurata tunma kafin a haifi yaron, (ananma kamata yayi ki shawarci angon ya haddace ta) addu'ar itace kamar haka

    بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.

    "Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana"

    Ma'anarta: "Da sunan Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi"

    Addu'ar tana cikin Sahihul Bukhari tareda Fathul Bari 4/181, harma Shaykh Pantami yace ba abin mamaki bane idan kaga shaidanin yaro a wannan zamanin, kana bin salsala zakagano iyayensa basuyi waccan addu'ar bane

    Don haka wadannan sune wasu daga cikin sahihan addu'u'o'in da suka inganta daga Ma'aiki SAW. Kuma naga ya dace na baki shawarar domin kuwa Annabi SAW yace: addu'a itace takobin mumini (Kamar yanda hakan ya zo a Sahihul Bukhari)

    Ina roqon Allah ya bamu ikon fahimtar addini dakuma aiwatar dashi, ya Allah ka tabbatardamu bisa tafarkin magabata na qwarai (Salafus salih)

    Allah ya baki zaman lafiya a gidan mijinki, Allah ya kauda fitina, Allah yasa zamanki dashi ya zamo alkhairi tun anan duniyar har zuwa can lahira. Allah yasa ya shayar dake Zanjabeel daga tafkin Salsalbeel a Aljannatil Firdous

    Wadanda suke singles (gwauraye), Allah ya basu abokan zama nagari

    Wallahu ta'ala aalam

    Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka, wa'atubi ilayk

    Amsawa;

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.