Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Son Ya Zamo Miji Nagari A Gareni

TAMBAYA (59)

Malam dan Allah idan ina son wani xan iya yin addu'a cewa Allah yasa wane ya zamo alkhairi agare ni?ya zamo miji nagari a gare ni?

Ba tare dana bi son zuciya ta ba

AMSA

Addua ibada ce kuma ba laifi bane ka yi ta idan har kaji wani ya kwanta maka a rai amman kamar yanda muka sani cewar addinin musulunci ya koyar damu komai sai mu koma hadisin Annabi SAW mu ji wacce shawara ya bada ga wanda yake son wani ko wata

Ya tabbata a cikin sahihin hadisi (Da littafin Hisnul Muslim) cewar Annabi SAW yana koyawa sahabbansa Addu'ar Sallar Istihara (Neman Zabin Allah Idan Mutum Zai AikaTa Wani Abu)

Jabir Ibn Abdullah, Allah ya yarda da shi da mahaifinsa, ya ce; Manzon Allah (SAW), tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara (neman zabin Allah) a Cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga Cikin Alkur'ani, yakan ce, "Idan dayanku ya yi niyyar yin wani al'amari to ya yi sallah raka'a biyu ba ta farilla ba, sannan ya ce;

اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ  حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.

Allahumma innee astakheeruka bi'ilmik, wa-astaqdiruka biqudratik, wa-as-aluka min fadlikal-'azeem, fa-innaka taqdiru wala aqdir, wata'lamu wala a'lam ,wa-anta 'allamul ghuyoob, allahumma in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ki fadi sunan wanda kike so din) khayrun lee fee deenee wama'ashee wa'akibati amree fakqurhu lee, wayassirhu lee, thumma barik lee feeh, wa-in kunta ta'lamu anna hazal-amr (sai ki fadi sunansa) sharrun lee fee deenee wama'ashee wa'aqibati amree fasrifhu 'annee wasrifnee 'anh, waqdur liyal-khayra haythu kan, thumma ardinee bihi.

Ya Allah ! Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonka daga falalarka Mai girma; domin Kai ne mai iko ni kuwa ba ni iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan fake. Ya Allah! Idan ka san cewa wannan al'amari sai ya ambaci bukata tasa alheri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma karshen al'amarina a wata rayuwar; da magaggaucin ala'marina da majinkircinsa Ka kaddara mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkance ni a cikin sa. Kuma idan Ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata da karshen al'amarina a wata ruwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa – Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka  kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma Ka sanya ni in yarda da shi".

Duk wanda ya nemi zabin mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a Cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;

(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)

"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".

Kinga kenan a shawarce sai ki bincika halayyarsa idan yana da addini da kyakkyawar iya mu'amala da mutane shi kenan ba abin kunya bane ki fada masa kina son sa, saboda Nana Khadija RA ita ta buqaci auren Annabi SAW sabida kyawawan halayensa

Ina fatan idan shine alkhairi a gare ki - Allah ya baki shi, akasin haka kuma Allah ya musanya miki da wanda yafi alkhairi

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments