Dashen Da A Mahaifa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mace ce ta yi auren fari bayan ta wuce shekaru hamsin. Saboda matsalar rashin haihuwa sai aka haɗa ƙwayayen haihuwar mijinta da na wata matar daban a waje, daga baya kuma aka dasa haɗaɗɗen ƙwan a cikin mahaifar ita amaryar. To wai wannan jaririn ga wace macen za a jingina shi? Kuma ko yin hakan ya halatta a musulunci?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .

    Da farko dai aikata hakan kai-tsaye bai halatta ba a musulunci, saboda a addinance kuma a aƙidance abin da aka fi so ga maauratan da suka kasa samun haihuwa ta hanyar da aka saba shi ne, su yi haƙuri kawai tun da dai abin yana da alaƙa da ƙaddarar Allaah Ubangijin Halittu ne. Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce

     

    لِّلَّهِ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۚ يَهَبُ لِمَن يَشَاءُ إِنَاثًا وَيَهَبُ لِمَن يَشَاءُ الذُّكُورَ ٩٤۝ أَوْ يُزَوِّجُهُمْ ذُكْرَانًا وَإِنَاثًا ۖ وَيَجْعَلُ مَن يَشَاءُ عَقِيمًا ۚ إِنَّهُ عَلِيمٌ قَدِيرٌ ٠٥۝

    Mulkin sammai da ƙasa na Allaah ne kaɗai, yana halitta duk abin da ya ga dama, yana yin baiwar ’ya’ya mata ga wanda ya ga dama, kuma yana yin baiwar ’ya’ya maza ga wanda ya ga dama, ko kuma ya gauraya su maza da mata (ga wanda ya ga dama), kuma yana ƙyale wanda ya ga dama a matsayin bakarare (mara haihuwa), haƙiƙa shi mai ɗimbin sani ne, mai cikakken iko. (Surah As-Shuuraa: 49-50).

    A nan Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala ya raba mutane gida huɗu ne dangane da baiwa ko kyautar haihuwa da yake bayarwa

    1. Wanda Allaah yake ba shi haihuwar ’ya’ya mata zalla, ba namiji ko ɗaya a cikinsu.

    2. Wanda yake ba shi haihuwar ’ya’ya maza zalla, ba mace ko ɗaya a cikinsu.

    3. Wanda yake gauraya masa, ya ba shi haihuwar ’ya’ya maza da mata a haɗe.

    4. Wanda yake hana masa haihuwar ko ɗaya daga cikin jinsunan guda biyu.

    Kuma duk wannan a wurin Allaah yana babin jarabawa ne ga bayinsa, ba wai alama ce ta soyayya ko ƙiyayyarsa ga bayin ba. So yake dai kawai ya ga yadda mai shi da mara shi za su rayu a cikin duniya: Shin za su gode masa ne, su yi yadda yake so da kyautar da ya ba su, ko kuwa butulce masa za su yi? Sannan shin za sui ƙan-ƙan da kai, su yi tawakkali tare da yawaita ibada da addua gare shi ne, ko kuwa ba za su yi ba?

    Don haka kamar yadda ya gabata, a lokacin da ma’aurata suka rasa haihuwa kwata-kwata, ko suka rasa wani jinsin da suke sha’awarsa, abin da ya fi kyau gare su shi ne: Su yi haƙuri, su mayar da alamarin ga Allaah Ubangijin Halittu kawai, su yi ta roƙonsa don ya ba su na-gari daga falalarsa. Haka manya Annabawa irinsu Annabi Zakariyya (Alaihis Salaaam) suka yi kamar yadda ya ambata a cikin Surah Al-Imraan:

    هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُ قَالَ رَبِّ هَبْ لِي مِن لَّدُنكَ ذُرِّيَّةً طَيِّبَةً إِنَّكَ سَمِيعُ الدُّعَاءِ  

    A can ne Annabi Zakariyya ya roƙi Ubangijinsa, ya ce: Ya Ubangijina! Ka yi mini baiwar zuriya kyakkyawa, lallai ne kai mai amsa addua ne. (Surah Al-Imraan: 38)

    Amma duk da irin waɗannan bayanan, malamai sun yarda cewa a lokacin da ma’aurata suka shiga tsananin buƙatar haihuwa, ya halatta a yi wa matar irin wannan dashen na ɗa a cikin mahaifarta. Sai dai a bisa wasu sharuɗɗa da malaman suka shimfiɗa kamar waɗannan

    1. Ya zama ƙwayayen haihuwan da za a ɗebo a haɗa, su zama na miji da matan da aka riga aka yi musu sahihin auren Sunnah ne kaɗai. Bai halatta a yi amfani da ƙwayayen haihuwa daga wani namijin da ba mijin matar ba, ko na wata matar da ba matar auren shi mijin ba.

    2. Ya zama mijin ne zai yi aikin fitar da ƙwayayen daga cikin matar, kuma shi ne zai yi aikin saka haɗaɗɗen ƙwan a cikin mahaifar matarsa, watau dai mijin ya zama shi ne likitan. Don kauce wa buɗe tsiraici da kallon tsiraicin ba tare da larurar da Shari’a ta halatta ba. Musamman dayake neman haihuwa bai kai larurar da saboda shi za a je ga wannan buɗe al’aurar da kallonta ba!

    3. Ya zama mahaifar da za a dasa haɗaɗɗen ƙwan a cikinsa na matar auren likitan ce. Bai halatta a dasa shi a cikin mahaifar wata matar da ba ita ce matar auren mijin a sharia ba, kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen kafirai. A nan kuwa ba haka abin ya ke ba.

    Da farko dai matar da aka yi amfani da ƙwayayen haihuwarta ba matar auren mijin da aka yi amfani da ƙwayayen haihuwarsa ba ne wurin samar da jaririn.

    Sannan ko da likitan da ya yi aikin ɗebo ƙwayayen haihuwar shi ne mijin matan guda biyu: Wacce aka ɗebo ƙwayayenta daga gare ta da wacce aka dasa haɗaɗɗen kwan a mahaifarta, duk da haka dai akwai kuma matsalar wadda za a jingina mata jaririn.

    Ko da an ce jariri na mai mahaifar da ya zauna a cikinta na tsawon watannin haihuwa kuma wacce ya fito daga cikinta ne, sai dai kuma a nan jaririn ba ɗa ne na asali ba. Bare ne shi daga ƙwan haihuwar wata matar da ba ita ce mai wannan mahaifar ba.

    Saboda wannan rikicin kuma da kasantuwar wajibcin tsare dangantakar mutane, da kuma tsare mazaunin gado ya zama dole a nan a ce: Abin da ya fi kawai shi ne iyaye su guji samun haihuwa ta wannan hanyar.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.