Dafa-Dukan Dankalin Turawa da Taliya
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Alayyafu
ii. Albasa
iii. Dankali
iv. Kayan yaji
v. Mai
vi. Nama
vii. Ruwa
viii. Taliya
ix. Tarugu
x. Tattasai
xi. Tumatur
Da farko,za a fere dankali a jajjaga kayan miya a soya. Daga nan, sai a tafasa nama da gishiri da albasa. Za a yi sanwa, idan ta yi sai a saka nama da dankali da taliya da alayyafu, da zarar sun dafu sai saukewa.
Dafa-Dukan Dankalin Hausa da Kabeji
Kayan haɗin da za a tanada su ne:
i. Albasa
ii. Dankalin Hausa
iii. Gishiri
iv. Kabeji
v. Koren tattasai
vi. Magi
vii. Man gyaɗa
viii. Nama
ix. Ruwa
x. Tarugu
xi. Tattasai
Za a samu kabeji a yanka shi, sai a wanke da kyau a juye a cikin kwando don ya tsane, a
ajiye a gefe. Daga nan a ɗauko albasa a wanke ta a ɓare
ta a yanka ajiye a gefe. Sannan a ɗauko tattasai da koren tattasai a
yanka ƙanana a ajiye.
Daga nan za a ɗauko tukunyar suya a ɗora a kan wuta a zuba mangyaɗa
a ɗauko nama tafasasshe a zuba a ciki.
Idan ya soyu,
sai a tsame a ɗauko yankakkun tattasai da attarugu da
albasa a juye a
soya sama-sama. Bayan nan za a ɗauko kabejin da aka yanka a zuba a kai a saka
gishiri da magi a ɗauko ruwa kaɗan a zuba a ciki a bar shi ya ci gaba da dahuwa. Za a ɗauko
naman da aka dafa a yanka ƙanana
a zuba a ciki,
sai a zuba dankali a ciki. Haka za a bar shi har sai ya dafu sosai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.