Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauyin Launin Jinin Al’ada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaamu Alaikum, Ni ban gane period ɗi na ba ne. Ka san an ce idan ya ɗauke mutum zai yi azumi, ko kuma idan ya canja daga ja zuwa brown. To, ni shekaranjiya ya ɗauke duka, sai na yi wanka, jiya kuma na yi azumi, amma da safe sai na ga brown kaɗan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah .

Jinin haila yakan ɗauki ɗayan waɗannan launukan ne guda huɗu

1. Launin duhu (ba ja-jau ba)

2. Launin Ja (Ja zur)

3. Launin Ruwan ciwo (As-Sufrah)

4. Launin Ruwan ƙasa (Al-Kudrah).

 (Dubi Fiqhus Sunnah: 1/102 na As-Sayyid Saabiq).

Don haka, duk lokacin da kika ga kowane ɗaya daga cikin waɗannan a farkon jininki, to haila ce.

Amma idan guda biyun ƙarshe suka zo miki a ƙarshen hailar, to a nan ba za ki ɗauke shi Haila ba kuma ba za ki damu da shi ba. Haka Sahabiyya Ummu Atiyyah (Radiyal Laahu Anhaa) ta bayyana. Ta ce

كُنَّا لَا نَعُدُّ الْكُدْرَةَ وَالصُّفْرَةَ بَعْدَ الطُّهْرِ شَيْئًا

Mun kasance ba mu ɗaukar Al-Kudrah da As-Sufrah a bayan tsarki a matsayin wani abu.

 (Sahih Al-Bukhaariy: 326 da Abu-Daawud: 307).

Abin nufi da: ‘ƙarshen hailar’ shi ne: ‘a bayan tsarki’, kamar yadda ya zo a cikin hadisin, amma ba wai kafin ɗaukewar jinin ba.

Domin Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito (#19) cewa: Mata sun kasance suna aikawa da ’yar auduga mai ɗauke da launin fatsi-fatsi (yellow) zuwa ga A’ishah suna neman bayanin tsarkin haila, sai ita kuma ta ce

لاَ تَعْجَلْنَ حَتَّى تَرَيْنَ الْقَصَّةَ الْبَيْضَاءَ

Kar ku yi gaggawa, ku bari har sai kun ga Al-Qassatul Baidaa’u .

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments