Hukuncin Jinin Da Yake Zuwa Wa Mace Mai Ciki

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamualaikum alaikum barka da safiya ya ibada Allah yakarbi ibadumu Ameen mallam don Allah tambaya nake; ina da ciki ina azumi sai inrika ganin jini ɗan kaɗan kamar digo ɗaya kuma azumi Ramadan ne toya matsayin azumi na yake nagode Allah yakara ma mallam lafiya.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikis Salaam:- Jinin da yake zuwa ma mai ciki kala uku ne

    Akwai wasu Matan idan sun ɗauki ciki ba su yin Jinin Haila Sai na biqi kaɗai, akwai wasu Kuma idan sun ɗauki Cikin Suna yin Haila.

    Misalin wata idan Cikin yayi wata 3 zatayi Jinin Haila, idan ya ɗauke ba zai sake dawowa ba sai Cikin yayi wata 6, idan ya Zo ya ɗauke toh ba zai sake zuwa ba sai cikin yayi wata 9 shine sai Jinin nakuda ya Zo sai Jinin Biqi Haka wasu Matan suke yin join Hailar su wata Kuma Bata yi.

    Sabida Haka Idan Ya zo kuma tsakanin shi da ranar haihuwa kwanaki biyu ne ko ukku toh jinin Naki ne wato na haihuwa dan haka ba zata yi Azumi ko Sallah ba, za ta gane hakane musamman idan na'kuda ta same ta a kwanakin nan.

    Idan Jini ne a farkon wata ko yadda ta saba ganin jinin ta na al'ada to wannan jini ne na haila, domin Magana mai rinjaye cewa mata masu ciki sukan iya yin jinin al'ada, to idan shi ɗin ne za ta bar Sallah da azumi.

    Idan ba duka biyun nan bane amma ya zo da ruwan 'kasa ko fatsi fatsi to wannan istihala ne ba shi da hukunci kawai wanke shi zatayi tayi bautarta,  idan kuma jajawur ne mai ainihin launin jini to wannan shine bleeding wato zubar jini saboda wani dalili, shima wannan wanke shi za ayi ayi ibadah.

    To da alamar nakin nan bleeding ne ba al'ada ko biki ba. Zakiyi Sallah kiyi Azuminki matu'kar ba haka kika saba gani ba.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.