Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari A Kan Illolin Kai Kananan Yara Makarantun Allo

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Nazari A Kan Illolin Kai Kananan Yara Makarantun Allo

DAGA

IBRAHIM RABIU

LAMBAR WAYA: 08065973237

EMAIL: ibrahimrabui228@gmail,com

TSAKURE

Ita dai wannan mukala ta mayar da hankali ne game da binciken illolin da ke akwai wajen tura yara a makarantun allo, domin nazartar wasu al,umma don tattaunawa da su domin jin ra’ayoyin su. Da kuma hanyar bincike ta yanar gizo-gizo domin samun sakamakon bincike mai kyau.

GABATARWA

Tsangaya a arewacin Nigeria ba wani abu sabo bane domin an dade ana yi saboda koyawa yara saukin kai dakuma samun abin da zasu ci sau tari kuma su ciyar da malamansu. Kamar Arewacin Najeriya da kuma kasar jamhuriyar Nijar akan ga yara kanana wani zubin matasa suna yawon bara musamman bayan karewar damina. Wato an gama aikin gona rani ya shigo.

DABARUN BINCIKE

Ta hanyar dora wannan bincike zuwa ga ingantaccen tsari ne, ya sa mukayi amfani da wadannan hanyoyin tattara bayanai kamar haka

1.      Nazarin ayyukan da suka gabata

2.      Takaitaccen nazarin kundayen bincike-bincke da Makalu

3.      Nemo bayannai ta hanyar fira da malamai da sauran al’umma

4.      Da kuma bincike ta hanyar yanar gizo.

GUNDARIN AIKI

Wasu yaran da aka gansu suna yawon bara an tuntubesu dalilin da ya sa suke yawon barace-barace wani yaron yace yana karatu ne amma ya fito yawon bara ne ya samu abinci. Bayan ya koshi sai ya kaiwa malaminsa sauran. Wani ma cewa yayi dole ne su fito bara su samu abunda da allah ya basu.

1.      Shi ko wani matashi cewa yayi tun yana yaro yake zuwa neman ilimi amma sai yayi bara kodayaushe domin ya samu abinci tare da kaiwa malaminsa

2.      To sai dai wasu iyayen yaran sun yi furuci game da yawon bara da yaran suke yi. A cewarsu iyaye ne keda sakaci wajen kula da malaman ya yansu domin idan da ana daukar nauyin malaman babu inda zasu tura yaran. Rashin ba malaman tallafi ya sa suna tura yaran zuwa bara. Malaman basu da abinda zasu ci balantana almajiransu idan basu yi bar a ba.

3.      Wani yace illa na tattare da barin yara kanana da basu san ciwon kansu ba zuwa yawon barace-barace yace wasu yaran basu da rigunan sawa a jikinsu ko sabulun wanka daga nan suke shiga wani hali na daban su shiga ayyukan assha. Suma malaman addinin islama suna da nasu laifi lallai barin yara kanana su yi bara a wannnan zamani bai dace ba sam.

Shima tsohon sarkin kano Muhammadu Sanusi II ya yi ta fadi tashin ganin an yi wa tsarin karatun allo kwaskwarima ta yadda za a hana sakin kanana yara barkatai a kan tituna kuma har sukan fada hannun wasu miyagun mutane da kan aikata laifuka marasa kyau da su.

 Babu wani banbanci tsakani almajiranci a jiya da kuma yau, yadda ake kai yaro “gabas” daga shi sai akwatinsa a baya yau ma haka ko yanzu yake, illa iyaka maimakon gabas, yanxu ko‘ina fantsama akai ana kai yara.

 Kuma wani abu da aka lura da shi a wannan zamani shi ne iyaye na kai yaransu almajiranci ne domin guje wa daukar nauyin da ke kansu da kuma talauci” a zamanin baya ba a barin almajirai suje bara kan tituna ko kan mahadar titi kusan kowanne yaro na da uwar gida da yake yi wa aiki wadda a wurinta yake samun abinci kila ma har sau uku a rana.

 Yara da yawa basa samun kulawar da ta dace daga malamansu da kuma iyayensu, a lokuta da dama wasu ba ta gari na amfani da irin wadannan damarmakin wajencin zarafi da tozarta kananan yaran. A wannan bangaren malamai suna daukar yaran da suka fi karfin kulawar su, sai ka ga malamin bai ma san adadin almajiransu ba balle kuma sanin sunayensu day bayan daya. Wannan na daga cikin dalilin da suka sa masu rajin kare hakkin dan adam ke kafa hujja da su wajen ganin an daina kai wadannan yara nesa da gidajen uwayen su.

 Iyaye da yawa a arewacin Najeriya na tura yaransu ciki har da kananan yara yan kasa da shekara shidda, zuwa makarantun allo domin saukar Alkur’ani mai tsalki.

Ana bayyana damuwa kan makomar yaran musamman yanzu da cutukka ke ci gaba da yaduwa a arewacin Najeriya

 Batun almajiranci a arewacin Najeriya shi ne wani batu da ya fi janyo ce-ce ku-ce musamman kan yadda za a gyara tsarin domin dacewa da zamani da ma yadda ake gudanar da ririn tsarin a wasu kasashen musulmi da suka ci gaba a duniya.

 Wasu dai sunyi kira a haramta bara a wajen kananan yara inda wasu kuma ke cewa ba haramta ta ya kamata a yi ba illa kawai a saka wa tsarin sabon fasali

(SAKAMAKON BINCIKE)

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya fito da tsari na sanya almajirai cikin wani dunkulallen tsarin karatun zamani inda aka gina makarantu domin koya masu Alqur’ani hade da na boko a wasu jihohin arewa yanzu dai abin jira a gani shi ne ko annobar korona za ta yi sanadin yi wa karatun almijaranci garanbawul ko kuma kawo karshen al’majiranci bisa dogaro da yadda wasu jahohi suka fatataki almajiran zuwa jahohin da suka fito

 Kasashen larabawa na gudanar da tsarin makarantun allo amma ya sha banban da yadda tsarin ke wakana a kasashe irin su Najeriya.

 Hadurran da yara kanana almajirai ke fadawa sun hada da:

1.      Rashin samun abinci

2.      Saurin kamuwa da cututtuka

3.      Fuskantar danniya da take hakki

4.      Rashin samun ilimin zamani

5.      Saurin bin masu miyagun dabi’u

6.       Rashin basu gudunmawar abinci su tafi da shi makaranta

7.      Rashin samun ziyara daga uwaye ko yan uwa

8.      Talaucin da ya addabi iya yansu.

9.      Suna fuskantar Zalunci daga manyan su.

10.  Kuma basu mallaki hankalin kansu ba.

SHAWARWARI

Mafita ita ce hanyar da ya kamata abi domin magance matsalar barace-barace tsakanin kananan yara ita ce a daina tura yara nesa da gidajensu domin neman karatun Al’qurani. Ya kamata iya ye su rinka tura yaransu makaranta da ke kusa da gida ta yadda kananan yara zasu samu damar zuwa makarantar boko da na allo, sannan kuma su kasance kusa da iyayensu wadanda za su ba su tarbiyyar da ta dace.

A karkashin wannan shirin gwamnati za ta tura malaman boko su rinka koyar da almajirai darussa irin su turanci da lissafi a ranakun alhamis da juma’a na kowanne mako, wato ranakun da ba a karatun Qur’ani.

Haka nan kuma gwamnati ta ce za a rinka tallafawa alarammomi da kayan abinci da kuma albashi a duk wata.

KAMMALAWA

Wannnan mukala kamar yadda bayanai suka gabata wani yunkuri ne na gano yanda illolin suke a fili ga duk yaran da aka tura a makarantun allo.


Post a Comment

0 Comments