Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).
Nazari Akan Kirkirarrun Kalmomin Siyasa A Jihar Zamfara Daga 2007 Zuwa
2023
Na
Muhammad Mustapha Ɗanmanga
Phone number:09031113464
Email: mdmanga88@gmail.com
Tsakure
Wannan muƙala mai taken “Nazari
akan ƙirƙirarrun kalmomin siyasa a jahar
Zamfara daga 2007 zuwa 2023” an gudanar da ita
ne domin ganin kalaman da al'umar jahar Zamfara ke yi a lokacin siyasar jahar
Zamfara da yayin gudanar zaɓe, wannan muƙala zata mai da
hankali ne wajen nazarin ƙirƙirarrun kalmomin siyasa da ma'anar
siyasa ita kanta,tare da fito da ainihin samuwar ƙirƙirarrun
kalmomin a fili.
Fitilun
kalmomi
Ƙirƙira,siyasa
1.0 Gabatarwa
Kamar yanda aka sani cewa,duk wanda ya zo
zangon ƙarshe na kammala karatun digiri na farko a jami'a,to
yakan ruhuta muƙala domin cikamakin karatunsa.
A wannan babi na ɗaya a cikin wannan
muƙala da aka gudanar mai taken “nazari
akan ƙirƙirarrun kalmomin siyasa a jahar
Zamfara daga 2007 zuwa 2023”an yi bayanin
dalilin bincike, manufar bincike,da sauransu.
1.1 Dalilin Bincike
Dalilin wannan bincike shi ne domin gano
wasu ƙirƙirarrun kalmomin siyasar jahar
Zamfara, waɗanda akayi amfani
da su a lokacin siyasar jahar, kafin zaɓe da kuma bayan zaɓe.
1.2 Manufar Bincike
Manufar wannan bincike ita ce a ruhuta
wannan muƙala domin ya zama cigaba akan wasu ayyuka da suka
gabaci wannan, an yi rubuce-rubuce da yawa a kan fannoni daban-daban masu
dangantaka da harshe da adabi da kuma al'adu a wannan sashe na nazarin hausa.
Manufar wannan bincike shi ne zai taimaka
wajen fahimtar nazari akan kalmomin ƙirƙira
da nazari akan siyasa,yin nazari irin wannan a cikin al'umma da ke siyasa zai
taimaka wa ɗalibai da masu
sha'awa har ma malamai wajen bunƙasa tunaninsu akan
ganin yanda ake siyasa da kuma ƙirƙirar sabbin kalmomi
a cikin siyasar, tare da fatan ya zama jagora ga masu buƙatar
gudanar da bincike irin wannan.
1.3 Maƙasudin Bincike
i. domin nazartar ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa na jahar Zamfara
ii. Nazartar dalilan da ke haifar da sabbin
kalmomin
iii. Nazartar tasirin ƙirƙirarrun
kalmomin a siyasar jahar Zamfara
iv. Binciko miye ke haifar da ƙirƙirarrun
kalmomin na siyasar jahar.
1.4 Tambayoyin Bincike
i. Me ya sa ake ƙirƙiro
kalmomin siyasa a jahar Zamfara?
ii. Mene ne dalilin da ke haifar da sabbin
kalmomin?
iii. Waɗanne dalilai ke haifar da tasirin ƙirƙirarrun
kalmomin a siyasar jahar Zamfara?
iv. Miye ke haifar da ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara?
1.5 Muhimmancin Bincike
Daga cikin muhimmancin wannan bincike akwai
i. Domin gano tasirin ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara
ii. Domin fahimtar wasu tasirin ƙirƙirarrun
kalmomi ga shuwagabanni
iii. Domin bin diddigin ƙirƙirarrun
kalmomin ga shuwagabanni da kuma tasirinsu ga al'uma
iv. Domin magance cin mutuncin shuwagabanni
ta hanyar furta ƙirƙirarrun kalmomi ga shuwagabanni.
1.6 Kadadar Bincike
Kadadar wannan bincike zata ta ƙaita
ne a kan sabbin kalmomin siyasar jahar Zamfara kawai tun daga shekarar 2007
zuwa 2023.
Binciken namu zai taƙaita
ne kawai ga iya ‘yan siyasa da kuma al'umar jahar Zamfara.
Sakamakon samun sabbin ƙirƙirarrun
kalmom da al'uma ke yi na siyasa, ya haifar da samun ƙirƙira
ta sabbin kalmomi daga al'uma zuwa ga ‘yan siyasa a jahar
Zamfara.
Wannan aiki ya taƙaita
ne a kan nazari akan ƙirƙirarrun kalmomin siyasa a jahar
Zamfara, wannan kadada ta taɓo amfani da harshe a ɓangaren siyasa,haka kuma an duba yana
yin ƙirkirarrun kalmomin siyasa a jahar Zamfara.
1.7 Kalmomin fannu
Nazarin ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara na da salon ko-ba-daɗe-ko-bajima,
al'umma sai sun jefa ‘yan siyasa da wata sabuwar kalma ƙirƙirarra
da ke nuna aibunsa ko alfanunsa, ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara abu ne da keda tsohon tarihi da aka fara tun
bayan shuɗewar mulkin soji
wato tun fara mulkin farar hula a jahar ta Zamfara.
Dabarun
gudanar da bincike
An bi hanyoyi daban-daban domin samun
nasarar gudanar da wannan bincike ta hanyoyi daban-daban kamar haka
An yi dabarar nemo wasu ayyuka da suka yi
shige da wannan domin fahimtar yanda za'a tsara aikin.
Bayan wannan kuma sai kundayen bincike kama
daga digiri na farko da na biyu da littafai da muƙalu da jaridu da
sauransu,duk suna cikin dabarun da aka tsara domin samun nasarar gudanar da
wannan bincike.
Wata muhimmiyar dabara ita ce, ta bin wasu
daga cikin manyan ‘yan social media na gwamnati waɗanda suke da alaƙa
da siyasa,hasali ma gunsu ake samun wasu ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar ta Zamfara, domin kawai samun nasarar gudanar da wannan
bincike.
2.0 Siyasa
Asalin kalmar siyasa kalma ce ta larabci
ma'anarta shi ne, tafiyar da shugabancin jama'a.
Haka kuma larabawa suna amfani da wannan
kalmar a duk lokacin da suke nufin shugabanci mai shiryarwa(wato ba wanda zai
kai waɗanda ake
shugabantar zuwa ga rashin nasara ko halaka ba).
Tarihi ya nuna cewa Farkon wanda ya fara
fito da ilimin siyasa wani mai hikima ne daga cikin girkawa,wato masanin
falsafar nan wanda ake kira Aristotle wanda ya rasu a cikin ƙarni
na huɗu kafin haihuwar
Annabi Isa (A,S).
Taƙaitaccen tarihin jahar Zamfara
Jahar Zamfara ta yi suna tun ana cewa
“Bature zaki” ma'ana tun tana a matsayin daula, daular Zamfara daɗaɗɗiya ce, tarihi ya
nuna cewa daular Zamfara ta kafu ne tun a ƙarni na goma sha
uku (13), Kuma tana ɗaya daga cikin
daulolin ƙasar Hausa tsofaffi (wato waɗanda suka daɗe da kafuwa).
A ɗaya ga watan Oktoba (1996) ne aka ƙirƙiro
jahar Zamfara a lokacin mulkin janar sani Abacha, inda gwamnan soji na farko
shi ne “Lieutenant kanal jibril Bala Yakubu”.
Jahar Zamfara ta samu Gwamnan farar hula na
farko a shekarar (1999), a ƙarƙashin mulkin Alhaji
Ahmed Sani (Yariman bakura) daga nan sai mulkin siyasar jahar ya ci gaba har
zuwa yanzu a yau.
Wani muhimmin abu shi ne jahar Zamfara tana
da kasuwanci iri daban-daban, haka kuma jahar ta bunƙasa
ne a kan noma.
An yi wa Zamfara jaha a shekarar (1996), a
lokacin janar Sani Abacha.
A jahar Zamfara akwai ƙananan
hukumomi guda goma sha huɗu (14 local
government) waɗanda suka haɗa da
. Anka
. Bakura
. Bukkuyum
. Birnin Magaji
. Bunguɗu
. Gusau
. Gummi
. Ƙauran
namoda
. Maru
. Maradun
. Shinkafi
. Tsafe
. Talatan mafara
. Zurmi
2.1 Ma'anar siyasa
Siyasa na nufin tafiyar da shugabancin
al'umma.
Siyasa na nufin wani shugabanci ne na
al'umma wanda ake bada shi ga wasu daga cikin al'ummar domin su jagoranci
sauran jama'a a yankunansu dama ƙasa da jahohi baki ɗaya.
2.2 Ƙirƙira
Masu bincike na farko fannin nazarin
harshen Hausa sun gudanar da bincike daban-daban a kan ƙirƙira
daga wasu harsuna zuwa Hausa.
Idan akace ƙirƙira
ana nufin ƙirƙiro wani abu wanda babu a wurin da
aka ƙirƙireshi.
Ƙirƙira
na nufin ƙirƙiro wani abu ko wata kalma sabuwa da
ake amfani da ita wurin furta wata magana domin ta bada ma'ana a wurin da aka
faɗeta.
2.3 Ƙirƙirarrun
Kalmomin Siyasa a Zamfara
A duka Najeriya ana samun wasu ƙirƙirarrun
kalmomi da ake amfani da su idan siyasa ta matso,wasu Kalmomin kuwa suna zuwa
ne a cikin mulkin da wani shugaba keyi, wani akan ƙirƙiro
wani suna a dinga kiransa da shi ko kuma a kira yana yin mulkin nasa da sunan
wanda za'a ƙirkiro,
Ana samun ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa ne galibi a wurin matasa ko kuma a ɓangarorin jam'iyar
adawa, a jahar Zamfara ma kuwa, bayan matasa da kuma masu amfani da kafar
sadarwa (social media)da kuma ɓangaren masu adawa, to a kan samu harda malamai suna ƙirƙiro
da wasu sabbin kalmomin a siyasar.
3.1 Samuwar ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara
i. Daga shekarar (1999) lokacin da aka fara
mulkin farar hula a jahar Zamfara, wato zamanin mulkin Gwamnan farar hula na
farko Alhaji Ahmed Sani (Yarima) tunanin mutanen jahar ya fara canzawa daga
rakiyar mulkin soji a jahar,inda suka fara laƙanawa shuwagabanni
da ‘yan siyasa waɗansu sunaye da zasu bayyana halayyar
su ta fili, amma a wancan lokacin zamanin mulkin yarima, bincike ya nuna babu
wata kalma ƙirƙirarra da akayi aiki da ita a
lokacin wajen nuna gazawa ko yaba ƙoƙarinsa,
har ya kammala mulkinsa a shekarar 2007.
ii. A shekarar (2007) a zamanin mulkin
Mamuda Aliyu Shinkafi an samu sabbin ƙirƙirarrun
kalmomi a lokacin mulkinsa, an samu kalmomi kamar haka
(A) Mas
(B) Damo
Kalmar (mas) da aka laƙawa
Gwamnan a lokacin, masoyansa ne da jama'ar gari ne suka ƙirƙiro
ta saboda soyayyar da ake yi masa, kalmar ta samo asali ne daga sunayen matan
shi gwamnan a lokacin,
(A) Mariya
(B) A'isha
(C) Sarari
(D) Maciji
Wadannan sune sanadiyar ƙirƙiro
kalmar mas.
Damo, a shekarar ( 2007) an samu wata ƙirƙirarrar
kalma da aka yi masa a lokacin mulkinsa wato kalmar “Damo”
kalmar Damo ta samu ne sanadiyar hakurn shi gwamnan a lokacin, shi ya sa
al'umma sukayi masa laƙabi na sunan Damo.
Kalmar maciji kuwa tasamo asali ne daga ‘yan
ɓangaren masu adawa,
a lokacin neman zaɓen gwamna a
shekarar dubu biyu da shaɗaya( 2011) in da
suke kamfen sai suce yanzu damo sunansa maciji, haka kuma wani mawaƙi
yayi waƙar in da yake cewa “yanzu damo sunansa
maciji yau babu lema ta ƙare”.
iii. A shekarar (2011) a lokacin mulkin
Alhaji Abdul'azizu Abubakar (yari) an samu ƙirƙirarrun
kalmomi a siyasar wannan lokacin, in da aka samu wasu ƙirƙirarrun
kalmomi kamar haka
(A) Ɗanmakau
(B) Gajere
(C) Shehi
Kalmar ɗanmakau wani mawaƙi
ne ya ƙirƙirawa gwamnan ita, in da yake cewa a
cikin wakar tasa “riƙe ƙwarai
gwamna ɗanmakau saura kaɗan ka ida kashemu”
Mawakin yayi wakar ne saboda duba da yanda
gwamnan ya faro solon mulkinsa.
Kalmar gajere itama mawaƙi
ne yafara ƙirƙiro da ita a zamanin mulkin Gwamna
Alhaji Abdul'azizu Abubakar (yari), wannan kuwa yayi wakar ne saboda shi yana ɓangaren adawa ne in
da yake cewa a cikin waƙar tasa “gajeree-gajere,
kutara ku buge bayan gidanmu yake”.
Kalmar shehi kuwa an kira gwamnan da ita ne
saboda ilimi da yake da shi musamman ilimin addini.
iv. A shekarar dubu biyu da goma sha
tara(2019) a lokacin mulkin Bello Muhammad (matawalle) an samu ƙirƙirar
sabbin kalmomin siyasa a jahar Zamfara a lokacin mulkinsa, kalmomin sun haɗa da
(A) Dodo
(B) Kwalhewa
(C) Taliya ba ta zaɓe
Kalmar dodo da ake yiwa gwamna matawalle,
shi da kansa ya faɗi ma'anarta a wata
zanta wa da yayi da ‘yan jarida in da yace musu “kalmar
dodo an samo ta ne sabo da ina ba ‘yan adawa tsoro kuma
ina firgita su”
Kalmar kwalhewa kuwa, tasamo asali ne daga ‘yan
siyasar jahar Zamfara a lokacin neman yaƙin zaɓen matawalle karo
na biyu, matasa ne ke amfani da kalmar domin moriyar kansu, matasa da sun faɗi kalmar kwalhewa
to suna nufin zasu je gidan ɗan siyasa ne su ƙarɓi kudin banza,
ma'ana dai duk wanda basu so shi ne ake zuwa wurinsa a kwalhe.
Haka ita ma kalmar taliya ba ta zaɓe, tasamo asali ne
a lokacin mulkinsa, in da ‘yan siyasar jahar
Zamfara ke raba taliya domin a zaɓesu amma mutane suka fahimci abun da ake
nufi da taliyar, bayan an yi zaɓe masu bada taliyar sun faɗi zaɓe ne sai matasa da
yara ƙanana suka dinga waka suna faɗin cewa “ taliya ba
ta zaɓe”.
V. A
shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023) ne gwamna mai ci ya hau kujerar
Gwamna wato Dr Dauda Lawal Dare PhD, an samu sabbin kalmomi ƙirƙirarru
da aka zo da su a lokacin wannan mulkin nasa kamar haka
(A) Buge-buge
(B) Langaɓu
(C) Laka da Gawai
Kalmar buge-buge ta samo asali ne daga
bakin gwamnan jihar Zamfara mai ci a yanzu wato Dr Dauda Lawal Dare PhD, a
lokacin da ake wata zanta wa da shi da manema labarai an tambaye shi akan yawan
fita da yake yi sai yace “yana fita buge-buge ne a wurin maƙotan
ƙasashenmu
domin ciyar da jahar Zamfara gaba” to a wannan lokaci
ne kalmar tayi tasiri kuma ta yaɗu a tsakanin al'umar jahar Zamfara.
Kalmar langaɓu kuwa tasamo asali ne daga ‘yan
ɓangaren adawar
siyasar jahar Zamfara, in da suke alaƙanta Gwamnan ta
kalmar langaɓu ma'ana (mutun
wanda bayada kuzari)
Kalmar laka da gawai kuwa an samu wani
malamin jahar ta Zamfara ne yayi amfani da wannan kalmomin ya jefi gwamnan da
kuma mataimakin sa da su, kalmar laka ita ce malamin ya danganta Gwamnan da ita
in da ake ganin kalmar na nufin rashin karfi ko kuma rashin kuzari,
Kalmar gawai kuwa ita ce ya jefa ma
mataimakin gwamnan ita, in da ake ganin saboda yana da baki ne ya faɗi kalmar akansa.
3.2 Amfanin ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara
Ƙirƙirarrun
Kalmomin Siyasa a jahar Zamfara na ɗaya daga cikin manyan makaman da al'umma da
‘yan adawa ke riƙewa
a matsayin babban makamin suka ko yabo ga ‘yan siyasa, kalmomin
na yin tasiri matuƙa, za'a iya cewa cikin kaso ɗari kashi tamanin
ko tamanin da biyar na bayyana halin ‘yan siyasa kai tsaye
na alheri ko saɓanin haka
Kalmomin na matukar jawo hankalin al'uma da
ƙara
musu ƙaimi wajen kambama ‘yan siyasa da
kururuta kalmomin ko sunan da aka ƙirƙirar
musu da su wajen yiwa al'umma aiki da kuma shayar da su romon dimokuraɗiyya, har ila yau
kalmomin na tunzura ‘yan siyasa suji kansu kamar sarakuna ko
matasan dawakai masu harbin iska
Misali
Kamar zamanin mulkin Gwamna Bello Muhammad
matawalle, al'umma sun ƙirƙirar masa da wata kalma da ke sa shi
jin daɗi a duk lokacin da
aka ambata masa wannan kalmar wato (Dodo) bincikenmu ya gano cewa ita wannan
kalmar ta Dodo tana nufin dodo tsorata maƙiya,(‘yan
adawa) wannan kalmar tasa mawaƙa da ‘yan bangar siyasa da
maroƙa harma da mutanen gari sukan yi amfani da ita musamman
a duk lokacin da sukayi kitiɓis da gwamnan a lokacin hakan keba gwamnan damar yi
musu alheri da kuma ɗaukar musu wasu alƙawulla
na roman dimokuraɗiyya, sakamakon jin
daɗin faɗar wannan kalma
gareshi.
Haka kuma wasu Kalmomin suna tasiri ga ‘yan
siyasa, sakamakon suna tsoron ‘yaɗa kalmomin da ake
yi, hakan na saka su idan aiki ne basuyi ba ya sa akayi musu jifa da wata
sabuwar ƙirƙirarrar kalma, to sukan yi ƙoƙarin
yin aikin domin magance wannan kalmar.
3.3 Rashin Amfanin ƙirƙirarrun
kalmomin siyasa a jahar Zamfara
A ɓangare ɗaya kuma jam'iyun adawa da magoya bayan su
da kuma ɗai-ɗaikun wasu mutane
sukan yi amfani da damar da suke da ita a kundin tsarin mulkin ƙasa
da ya basu damar faɗar albarkacin
bakinsu wato(freedom of speech) a turance, wajen jingina wa ‘yan
siyasa ko ƙirƙirar musu da munanan kalmomi da ke
tunzura ‘yan siyasar harma da magoya bayan su,wanda
waɗannan kalmomin na
iya haddasa sarewar guiwa ga ‘yan siyasa da kuma
haddasa fitina da faɗace-faɗace a cikin
al'umma.
Misali
A cikin wannan mulki mai cike da taraɗi na jam'iyar adawa
mai mulki wato PDP wadda gwamna mai ci wato Dr Dauda Lawal Dare PhD ke
shugabanta a jahar,an samu wasu baƙin ƙirƙirarrun
Kalmomi da aka jefa masa da shi da mataimakin sa wato malam Mani mumini wanda
aka jiyosu daga bakin wani malami… wanda waɗannan kalmomin sun
tunzura al'ummar jahar Zamfara in da suka karaɗe yanar gizo (sosai media) ga baki ɗaya.
A ɓangare ɗaya kuma jam'iyar adawa sun yi matukar farin
ciki da waɗannan kalmomin
wajen amfani da su wurin suka ga gwamnan da mataimakinsa, wanda wannan ya
haifar da ka-ce-na-ce a tsakanin al'umar jahar Zamfara, wannan ya nuna ƙirƙirar
wata kalma a wani lokacin a jefe shugaba da ita, musamman waɗanda suka saɓawa tarbiyya, ka
iya haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin al'umar jahar Zamfara.
4.0 Sakamakon Bincike
Kowanne bincike da aka gudanar na ilimi,
za'a tarar yana da sakamakon da aka cimma na wannan binciken, wannan bincike
namu ya cimma abubuwa kamar haka
i. Ƙirƙirar
wata kalma a jingina wa wani daga cikin ‘yan siyasa na yin
matuƙar tasiri wajen zaburar da su (‘yan
siyasa) ko sanyaya musu guiwa, sakamakon kyawon kalmar ko munin kalmar.
ii. Ƙirƙirarrun
Kalmomin Siyasa na faruwa ne sakamakon kamun ludayin shi ɗan siyasar a cikin
al'umar da yake mulka, Da kuma irin adawar da al'umma suka nuna masa.
iii.
Ƙirƙirarrun
Kalmomin Siyasa a jahar Zamfara na yin tasiri har a zukatan al'umma da kuma su
kansu ‘yan siyasa har a rumfunan zaɓensu,kamar yadda
bincikenmu ya gano.
4.1 Kammalawa
A cikin bayanan da suka gabata na wannan
aiki,an yi ƙoƙarin fitowa da ma'anar siyasa da kuma ƙirƙira,haka
kuma an yi taƙaitaccen bayani a kan tarihin siyasar jahar Zamfara,
tare da bayyana dalilan da ke haifar da ƙirƙirarrun
Kalmomin Siyasa a jahar Zamfara, tare da bayyana amfaninsu da kuma rashin
amfaninsu.
Manazarta
Hira da ‘yan social media na
siyasa, akwai na ɓangaren gwamnati
mai ci yanzu da kuma ɗayan ɓangaren adawa (waɗanda suka faɗi zaɓe)
Prof S.A Yakasai (2020) Jagoran Ilimin Walwalar
Harshe.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.