Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba ta Mutu Ba Ta Balgace: Nazari A Kan Kayan Maye A Garin Gusau.

Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Ba ta Mutu Ba Ta Balgace: Nazari A Kan Kayan Maye A Garin Gusau.

Na

Abdulrahman Yushau

Phone Number: 08148018025

Gmail: aabdulalkali@gmail.com

Tsakure

Wannan aiki ya mayar da hankali ne, a kan kayan maye masu bugarwa da dangoginsu. Haka kuma zai ba da muhimmanci ƙwarai a kan irin illolinsu ga matasa, tare kalato takaitaccen muƙaddashin a bin da ke haifar da shaye-shayen tare da binciko hanyoyin da suke bi kafin mallakar kayan mayen. An ɗora aikin a kan fahimtar Hausawa da suka ce ‘Allah ya waddaran naka ya lalace” A yayin gudanar da wannan aiki, an yi amfani da gani da ido wato tushe na farko(primary source), sai kuma hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da:Ta hanyar hira (interview), majiya ta biyu (secondary source). Wannan binciken ya gano cewa matasa ba haka kawai suke faɗawa amfani da kayan maye ba, sai dan waɗannan dalilan kamar haka; rashin mafaɗi, son zuciya, ƙuncin rayuwa, da harkokin siyasa, da kuma taadanci. sukan samu matsala ne ta faɗawa tu’ammali da kayan maye musamman idan suka rasa iyayensu. Wannan aiki ya tabbatar da cewa duk waɗannan matsalolin amfani da kayan mayen ana samun su ne sakamakon yawan rashin aikin yi ga matasa da kuma bangar siyasa.

Fitattun Kalmomi; kayan Maye,Garin Gusau.

1.0 Gabatarwa.

Tabbas maye babban lamari ne da yake ci wa duniya tuwo a ƙwarya ta ɓata tarbiya da haddasa harkar ta’addanci da rusa ci gaban yankunan da ya samu rinjaye. Shaye-shayen ba zai yi kansa da kansa ba har sai da abin shan wato kayan mayen.

Abin tambaya a nan shi ne, (¡) ta yaya ake samar da kayan maye a garin Gusau (¡¡) mene ne gurin masu samar da kayan mayen a kan al’umma (¡¡¡) wake hanya ce za a bi domin ganin kayan maye sun daina tasiri ga al’umma. Yana daga cikin manufar wannan binciken zai yi kokari wajen bin diddiƙin samo amsar wadannan tambayoyin.

Makasudi wannan bincike shi ne (¡) zaƙulo tasirin da kayan maye suka yi da kuma karfin yaɗuwar da kayan ke samu a garin Gusau (¡¡) Gano ire-iren sababbin kayan maye da ake samu da kuma ta hanyar da ake tallata wa al’umma su.

Kadadar wannan bincike ta tsaya ne kurum a iya garin Gusau, a inda ta tsaida ganin ta a kayan maye.

1.1 Dubarun Gudanar Da Bincike

Domin gwangwaje wannan aiki da inganta shi an yi amfani da hanyoyi mabambanta kamar haka

        i.            Gani da ido; An yi amfani da wannan hanya ta gani inda aka ziyarci daba-daba (jungle) domin ganin yadda suke yin shaye-shayen da sanin lokacin da suka fi shaye-shayen da kuma yana yin da suke kasancewa a lokacin da abin shaye-shayen ya fara aiki a jikinsu, tare da duba nau’o’in kayan mayen, shin na hayaƙi, ko ƙwaya ce, ko na ruwa ne da sauransu.

     ii.            Ta hanyar hira (interview); Wannan aiki ya samu hira (interview) da ma’abota shaye-shayen domin sanin ta yadda suke mallakar kayan mayen, abin da ya yi sanadiyar jefa su wannan halin na maye.

   iii.            Majiya ta biyu (secondary source); haka kuma wannan aiki ya samu tattauna da makusantan masu wannan dabi’a ta shaye-shaye domin sanin gwagwarmayar da suka yi da su domin su ga sun bar wannan dabi’a da kuma kalar hanyoyin da suke dan ganin mayen ba su zuwa gare su.

   iv.            Bitar ayyuka masu alaƙa da wannan aiki. Wannan aiki ya dubi ayyuka masu alaƙa ta kusa da shi domin sanin makama.

      v.            Daga ciki kuma aikin ya fitar da wasu daga cikin hanyoyin da za a iya bi domin shawo kan matsalar ta hanyar ganin kayan maye sun daina yaɗuwa a garin Gusau, da kuma dakatar da wasu matasan daga faɗawa wannan dabi’a.

1.2 Ra’in Bincike

An wannan bincike a kan ra’in karin magana na Hausa da suka ce “Allah ya waddaran naka ya lalace”

Wannan ra’in ƙarara yana

2.0 Waiwaye A kan Ma’anar Maye

Kayan maye na nufin dukkan wani abu da ya ke tasiri a hankalin mutum, ta yadda zai iya fitar da mutum daga hayyacinsa na asali ya daina fahimtar abin da ke kewaye da shi. Idan mutum ya ɗaure da amfani da wannan abu sai ya zama Dan Marisa, ya zama ba zai taɓa samun jin dadi ko sukuni ba, har sai ya sha wannan abin mayen.

Masana sun fitar da ra’ayoyin su mabambanta dangane maye ko kayan maye. Maye ko shaye-shaye na nufin amfani da wasu sinadarai don manufar haifar da tasiri mai daɗi akan ƙwaƙwalwa. Akwai mutane sama da miliyan 190 masu amfani da muggan kwayoyi a duniya kuma matsalar tana karuwa cikin firgici, musamman a tsakanin matasa yan kasa da shekaru 30. Dr. A. Mandel (2023).

2.1 Waiwaye A kan Garin Gusau

Garin Gusau gari ne da aka kafa shi tun a shekarar 1811 kimanin shekara 212 da suka gabata bayan tasowar garin daga ‘Yandoto a shekarar 1806. Garin Gusau yana daya daga cikin manyan garuruwan tsohuwar Jihar Sakkwato kafin daga bisani ya zama babban birnin Jihar Zamfara a shekarar 1996. Kamar yadda kundin tarihin kasa na 1920 ya nuna, garin yana kan titin Sakkwato zuwa Zariya ne kimanin kilomita 179, kilomita 210 tsakaninsa da Sakkwato. Daga gabas garin Gusau ya yi iyaka da Jihar Katsina da ta Kwatarkwashi daga arewa kuma ya yi iyaka da garin Ƙaura a yayin da ya yi wata iyakar da garin Bungudu daga yamma a bangaren kudu kuma ya yi iyaka da Ɗansadau da kuma Tsafe.

3.0 Nazarin Hanyoyin Shigowa Da Kayan Maye A Garin Gusau

Ba za a yi musu ba, idan aka ce tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi yana taka rawa ta musamman a harkar taaddanci da miyagun laifuka da mahaukata da maula da bangar siyasa da sauransu. Akwai ɓarɓashin gaskiya a maganar Hausawa da suka ce “sai bango ya tsaje”, wato hanyoyin da ake bi dan ganin an shigo da kayan maye sune tsajewar bangonmu dan idan masu sha ba su gani ba, ba za su sha ba. Daga cikin hanyoyin da binciken ya gano, ta hanyar zantawa da masu ruwa da tsaki ga harkar su ne;

1)      Ta ɓaurauniyar hanya: wato ɓaurauniyar wata hanya ce wadda take daga ɓangaren kudu ta inda Gusau ta yi iyaka da Ɗansadau ita wannan hanya idan ka miƙeta daga Gusau tana iya kai ka jihar Naija kuma tana iya sadaka da Birnin Gwari ita dai wannan hanyar, a wannan hanya ana shigowa da kayan maye ta babura da kuma mota ba tare an yi masu sakaye ba, kamar yadda aka saba a manyan hanyoyi.

2)      Ta hanyar manyan motoci: ana shigowa da kayan maye ta cikin manyan motoci, ta cikin tankin suna rizab.

3)      Ta hanyar goro: Ana shigowa da kayan ta cikin ƙunshin goro.

4)      Ta hanyar mashin roba-roba: ana shigowa da kayan maye ta cikin siddin mashin wato shinfiɗar zaman.

Wadannan hanyoyi ne da ake shigowa kayan maye a garin Gusau. Sai kuma hanyoyin da ake rarraba su a cikin gari, su ma ga su kamar haka;

1)      Ta fuskar bara: masu raba kayan suna yin shiga kamar mabarata a kan hanya wajen raba kayan maye a cikin gari.

2)      Ta fuskar mahaukata: wannan wata fuska ce da ake amfani wajen raba kayan maye a cikin gari. Inda idan mai saye ya zo suka gane kwastoma ne sai mahaukacin ya tsokane shi, shi kuma sai mahaukacin ya yar da abin da wancan saye sai ya gudu, shi kuma sai ya ɗauka.

3)      Ta fuskar kabu-kabu: suna rarraba kayan maye da suffar kabu-kabu.

4)      A daba: ana raba kaya a mazaunin da ake shan su wato jangul.

3.1 Sunayen Wasu Tsofaffi da Sababbin Kayan Maye

Akwai kayan maye waɗanda tun da daɗewa ana amfani da su, akwai kuma waɗanda daga baya-baya nan ne suka bayyana. Su dai tsofaffin kayan mayen wasu daga cikin masu amfani da su, suna gajiya da su ne, shi ya sa suke fara neman sababbi wasu kuma sun daina yi masu aiki yadda suke yi ada da dai sauran dalilai ire-iren wadannan. A wannan binciken za a kasa ko za raba kayan mayen zuwa nau’in yadda ake shan su.

        I.            Kayan maye na ruwa

1)      Kodin

2)      Totalin

3)      Kof M

4)      ‘Yan zolin

5)      Bona

6)      Jiya

7)      Kodalin

8)      Izzifilon

9)      Ngc

10)  Asad

11)  Takardar jarida

12)  Kan ashana

13)  Kashin jaki

14)  ‘yan ‘yan darbejiya

15)  Kashin ƙadangare

     II.            Kayan maye na hayaƙi

1)      Marijiwana

2)      Buƙi

3)      Wiwi

4)      Arizona

5)      Lohi

6)      Doha

7)      Sk

8)      Garin bulet

9)      Buƙi

10)  Laud

11)  Karas

12)  Indian-hemp

13)  Ganja

14)  Suton

15)  Daga

16)  Kaifu

17)  Giras

18)  Bahanij

19)  Karas

20)  Hashis

   III.            Kayan maye na ƙwaya

1)      Refanol

2)      Fari

3)      Roki

4)      Tiramol

5)      Suwafa

6)      Diyaza

  IV.            Kayan maye na shaƙawa

1)      Shalisho

2)      Kwata

3)      Fetur

4)      Cinnaka

5)      Hajiya Jamila

6)      Hajiya Aisha

7)      Hajiya Halima

8)      Hajiya Binta

9)      Bullet

10)  Ak47

11)  Mai bindiga

12)  Salma

13)  Mai inyass

14)  Danmilla

15)  Madarar sukudai

    V.            Kayan maye na kuskura

1)      Kuskura

3.2 Hanyoyin Magance Wannan Matsalar Ta Shigowar Kayan Maye da Amfani da Su

A.    Jami’an Tsaro; hukumar hana safara da shan miyagun ƙwayoyi ta kara inganta aikinta da kayan zamani.

B.     Uwaye; da yawan wasu uwayen ba su san sana’ar da ɗiyan su ke yi ba, kuma ba su damu da su sani ba. Saka idon iyaye a cikin al’amuran ɗiyan su zai taimaka kwarai, dan duk masu yin waɗannan abubuwa haihuwar su aka yi.

C.     Malamai; su kara yawaita wa’azi da nuna illolin safara da shan miyagun kwayoyi tare bayyanar sakayyar dake tattare da hakan.

D.    Hukumomi

4.0 Sakamakon Bincike

Sakamakon wannan binciken ya yi dai-dai da makasudin binciken, tun daga taken binciken za a ga cewa aikin ya mayar da hankali ga kayan maye yadda ake shigowa da su da kuma yadda ake raba su a cikin gari da kuma sunayen kayan mayen. A nan za a iya cewa aikin ya yi nasara, domin kuwa aikin ya gano wasu daga cikin hanyoyin sirri da ake shigowa da kayan maye. Wanda a dalilin hakan ake samun faruwar waɗannan abubuwa kamar haka;

Ta’adanci

Sace-sace

Bangar siyasa

Lalaci da ganin laifi

Daƙushewar alumma

Su dai waɗannan matsalolin da aka kawo a sama waɗanda ke faruwa a sakamakon shigo da kayan maye, suna haifar wa da al’umma waɗannan illoli kamar haka;

Rashin ilimi

Rashin tarbiya

Rashin aikin yi

Rashin dogaro da kai

Rashin tunani mai kyau

Wannan abu duka ana samun shi ga mutunen da ke wannan harka ta shan kayan maye, wasun su da dama kafin fara wannan harka mutane ne masu natsuwa, amma bayan shigar su wannan harka ta mai da su tamkar leda idan ana iska.

4.1 Kammalawa

A cikin bayanan da suka gabata na wannan aiki, an yi ƙoƙarin fitowa da maanar kayan maye da tasirinsa. Haka kuma an yi gajeran sharhi dangane da garin Gusau, duk a cikin muƙalar an kawo hanyoyin sirri waɗanda ake bi domin shigowa da kayan maye. Bayan wannan kuma, an yi ƙoƙarin fito da hanyoyin da ake bi don rarraba kayan a cikin gari, sannan kuma an kawo sunaye da dama na kayan maye mabambanta. A cikin wannan aiki da aka gabatar za a ga cewar, kura-kuran da ake samu a cikin hukumomi yana daga abin da ya kamata mahukunta su ɗauki mataki sosai, su ga an gyara su, domin ta hanyar kiyayewar su ne za su samu damar isasshen tsoron da zai daƙale wannan mummunar sanaa cikin sauƙi kamar yadda wannan muƙalar ta yi bayani.

Manazarta

https://drmaigidakachako.blogspot.com/2013/04/kayan-sa-maye-na-gargajiya.html?m=1

https://aminiya.ng/sata-muke-yi-da-karuwanci-mu-samu-kudin-shaye-shaye-a-sabon-gari/

National Institute on Drug Abuse, Division of Research, 5600 Fishers Lane, Rockville, Maryland 20857

Weech, A.A. The narcotic addict and “the street.” Archives of General. Psychiatry, 14:299-306, 1966.

Post a Comment

0 Comments