Mene Ne Fa'idar Yin Murmushi

    TAMBAYA (71)

    Aslm Usmannoor ya kake, mene ne matsayin murmushi ko fa'idarshi, alkhairi ne, ko ihsani, ko sadaka?? Sako daga Zhrdn Zeemo.

    AMSA

    Allah SWT yace;

    ( وَأَنَّهُ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ )

    النجم (43) An-Najm

    Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kuka

    Kamar yanda muka sani cewar da dariya ko murmushi da kuka ko yaqe dukkansu halittu ne da Allah SWT ya sakawa dan Adam da manufar isar da saqo. Dariya idan ta wuce iyaka tana zama matsala haka ma kukan

    An karbo hadisi daga Abu Hurairah (RA) yace, Annabi SAW yace: Yin murmushi ga dan uwanka musulmi sadaka ne, umarni da kyakkyawa da hani da aikata mummuna sadaka ne, yin mu'amalar auratayya shima sadaka ne"

    (Hadisin yana cikin Kutubus Sittah wato Bukhari, Muslim, Abu Dawud, Tirmidhi, Nasa'i da Ibn Majah)

    Dangane da dariya kuma ya tabbata a cikin Hadisil Qudsi (Divine Narrative) cewar Allah SWT yana dariya. Kamar yanda Annabi SAW ya fada a cikin hadisi cewar yasan dan Aljannah na karshe (Wanda shi ne karshen fita daga Wuta) wanda bayan Allah SWT ya sa a fito dashi daga wuta zai ji dadi shi a tunaninsa ma nan wajen shi ne Aljannah

    Sai a suranta masa wata bishiya mai kyau, yace ya Ubangiji ka bani ikon zuwa karkashin bishiyarcan na ci na sha daga itaciyarta na ji inuwarta, sai Allah SWT yace masa, ai iya alfarmar da ka roqa shi ne fitowa daga wuta

    Sai yace ya Ubangiji don rahamarKa ba don ni ba. Allah SWT zai bashi ikon zuwa wannan bishiyar. Daganan zai qara hango wata bishiyar wadda ta ninninka ta farko a komai na daga ni'ima, ya qara roqon Allah SWT, hirar farko ta kara maimaituwa har dai zuwa bishiya ta uku wadda ta ninninka ta farko da ta biyu. Anan ne zai fara jiyo sautin mutanen gidan Aljannah (Allah ya sa muna cikinsu), idan yaji haka sai yace; ya Allah a dan kara matsar dani zuwa koda gate din Aljannah ne

    Allah SWT yace; bamuyi haka dakai ba ya bani Adam, yace don RahamarKa ba don ni ba. Bayan an bashi ikon karasawa gate din ne zai ce, ya Ubangiji kada dai a gaji da ni, a dan saka ni daga cikin Aljannar

    Har zuwa inda hadisin yace; zai ga wani wanda bai taba ganinsa ba, nan take zai zube yayi sujjada shi a tunaninsa Allah SWT ya bayyana, sai ace masa tashi wannan ai mala'ika ne mai gadin gidanka. Allah SWT zai ce masa roqi dukkan abinda kake so, zai kure burinsa amman a karshe za'a ce masa an baka dukkan abinda ka roqa, an kara maka da abinda ke cikin duniya sau 10, zai ce ya isheni haka ya Rab, Allah SWT zai yi masa dariya

    Sai yace ya Ubangiji, kaine fa Ubangijin sammai bakwai da kassai bakwai kuma kake dariya, ko dan na kasance nine na karshe (talakan) Aljannah ?

    Sai Allah SWT yace; "ba don haka nake maka dariya ba, nayi ne saboda ina da iko akan aiwatar da dukkan abinda na ga dama"

    (Duba cikin littafin Albidaya wan Nihaya na Ibn Khathir)

    A Tirmidhi an tabbatar da cewar Annabi SAW yana dariya saidai dariyarsa ba irin ta sauran mutane bace ba, kuma yawanci yafi yin murmushi kuma yana cewa ina yin barkwanci amman duk abinda zan fada gaskiya ne

    _*(Tirmidhi hadisi mai lambata 1990, da Musnad Ahmad bin Hambal

    hadisi mai lambata 8481)*_

    Haka kuma Tirmidhi ya fitar a riwayar Abdullahi Ibn Abbas cewar haramunne yin dariya. Imam an-Nawawi yace yawan yin dariya yana qeqashe zuciyar mutum ga barin yawaita ambaton Allah SWT kuma yana rage darajar mutum, idan kuma an yi ne don asaka wani dariya to zai zama mustahab (recommended)

    (Muhammad AbdulRahman, al-Mubarak furi, Tuhfatul ahwazi bi sarhi Jami'al Tirmidhi a cikin "babu majaa fi al-muzahi)

    Misali shi ne hadisin wannan tsohuwar da tace: ya rasulullah shin tsohuwa kamar ni zata shiga Aljannah ?

    Sai Annabi SAW yace: Ya Ummu fulan, ai tsofaffi basa shiga Aljannah

    Tsohuwa sai ta fara kuka saboda tasan gaskiya ya fada

    Sai ya karanta mata ayar Qur'ani inda Allah SWT yake magana akan matan Aljannah, yace;

    ( إِنَّا أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءً )

    الواقعة (35) Al-Waaqia

    Lalle Mu, Mun ƙaga halittarsu ƙagawa

    ( فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًا )

    الواقعة (36) Al-Waaqia

    Sa'an nan Muka sanya su budurwai

    Aikam da jin haka, nan da nan, yar tsohuwa ta ji dadi saboda taji ance za'a maida tsohuwa zata koma budurwa a Aljannah

    Da kuma hadisin Ummu Ayman (RA) da tazo wajen Annabi SAW tace: Ya rasulullah, miji na yana gayyatar ka gidanmu. Sai yace: wanene mijinki, ko shi ne wannan wanda da akwai fari a cikin idonsa ?

    Sai tace: ya rasulullah wallahi miji na babu fari a idonsa

    Sai Annabi SAW yace mata: kowanne dan Adam ai yanada fari a cikin idonsa

    Anan Annabi SAW yana nufin wannan farin da yake a kusa da baki da yake a idanun kowanne mutum

    Haka kuma akwai hadisin Anas Bin Malik (RA) da yace: Annabi SAW yana yawan kira na da "Ya dhal udunayn" ma'ana: "Yakai ma'abocin kunnuwa biyu"

    Da dai sauran masu yawa da suka tabbatar da barkwancin Annabi SAW

    (Duba littafin "Joke of Prophet Muhammad in the Hadith" wato "Barkwancin Annabi SAW a cikin hadisi")

    A kimiyyance kuma malaman Human Anatomy sun gano cewar Dimple naqasu ne ga fuskar mutum a kimiyyance amman a zahiri tsarin halittane mai saka kyau ga fuskar da take dauke dashi. Ana kiran cutar da suna Genetic Disorder kokuma Anatomical Defect wanda akewa taken Blessing in Disguise. Ana samun Dimple ne sanadin tsokar Zygomaticus major idan ta ribanyu (Double kokuma Bifid akan fuskar mutum). A duk lokacinda mai dimple tayi murmushi sai wannan tsokar ta Zygomaticus ta bude ta hanyar tattare fatar kumatu ta fitarda wani qaramin rami a karshe hakan ya wanzarda murmushi mai taushi

    To mene ne yake kawo murmushin kokuma dariya ? Mutane da yawa basa iya bada amsar wannan sauqaqaqqiyar tambayar, wani zai iya cewa abinda ya sa ake murmushi ko dariya shi ne farin ciki, alhalin ba haka baneba, kuka wani zaice baqin ciki ke kawoshi kuma shima ba haka baneba, abinda ke kawosu shi ne isarda saqo zuwaga wanda akai niyyar isarwa da taimakon Allah dakuma tallafawar ita waccan jijiyar mai suna Zygomaticus (wadda sun rabu kashi 2, akwai zygomaticus major akwai kuma zygomaticus minor)

    Duk suna yiwuwane da izinin Allah ta sunayensa guda 2 cikin 99, Alqabid wal Basid. Shi ne Al-qabid (The Contractor) mai quntace abu sannan kuma shi ne Al-basid (The Expander) mai bude abu. Quntacewar da kuma budewar da jijiyar take a samu murmushin yana yiwuwane silar sunayenSa SWT. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai bada ikon saka kuka ko dariya, da ba dan Zygomaticus ba, da bazamu iya kuka ko dariya ba

    Kamar yanda ya fada a cikin Suratul Najm ayata 43 "Wa'innahu huwa adhaka wa'abka" ma'ana "Kuma lalle, Shi, Shi ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kuka". Wannan ayar bai kamata kawai mu dauketa a matsayin ayar dake nuni akan Dariyar mutum kokuma Kukansaba saidai anan Allah SWT yanason bayinSa suyi Tadabburi ga littafin Qur'ani ne domin gano wasu boyayyun hikimomi da yake son su gano ta hanyar fadada bincike a kimiyyance da fasahance ta yanda hakan zai tabbatarwa da masu binciken akwai Mahalicci (The Grand Designer), sannan kuma wannan ayar hujja ce akan masu ilimin Human Anatomy wadanda basu yarda da WanzuwarSa ba. Sannan kuma wannan ayar kadai ta isa ta tabbatar maka da cewar Shi Mai Iko Ne akan komai

    Ba iya kuka ko dariya bane suke damfare da sirrin dake cikin Alqabid wal Basid ba, hatta sassan jikin mutum (irinsu zuciya, hunhu, harshe, ido, hanci, hannu, kafa, baki da sauransu) idan mun samu lokaci zamu fadada bayanin akansu, insha Allahu

    Ina fatan wannan amsar za ta sa mutane su kara Imani da kuma godewa Allah SWT akan ni'imomin da yayi mana wadanda bazasu qirgu ba. Alhamdulillah bini'matihi ta'atimus salihat

    Wallahu ta'ala a'alam

    Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

    Amsawa;

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.