Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Yawan Dariya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Mallam HAMISU Muna godiya sosai da irin kokarin da kake yi, Allah ya saka maka da mafificin alkairi da kuma addu'ar cikawa da imani su tabbata agareka tare da iyalanka, iyaye, malumanka da kuma daliban wannan group mai albarka.

Tambayata ita ce mene ne hukunci wandanda suke Kirkirar labarin karya don su bama mutane dariya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace : ( AZABA TA TABBATA GA WANDA ZAI BADA WANI LABARI SAI YAYI KARYA DOMIN YADARIYANTAR DA JAMA'A DASHI, AZABA TA TABBATA AGARESHI, SANNAN AZABA TA TABBATA AGARESHI).

Tirmizi yaruwaitoshi acikin كتاب الزهد (kitabus zuhudi) babi na 10.

Masu rubutawa da masu karantawa da masu yi da baki duk sun shiga cikin wannan hadisin.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace: Da kunsan abinda nasani, da kunyi dariya kaɗan, kuma kuyi kuka mai yawa.

Yana yin yanda mu keyin dariya ya sha ban-ban daga wani zuwa wani. Inda yawan dariyar wani ba ta da makama kuma ta wuce kima, sai kaga wani nata sharara dariya harda hawaye sai kace an yafe masa dukkanin laifukkansa na duniya.

Wani har fina-finnan barkwanci yake kallo dan kawai nishadin da zaisa ya sharara dariya har sai ya ji cikinsa ya yimar ciwo. Ba tare da lura da ainihin illar da yawan dariyar nan take haifarwa ba.

Ba laifi bane dan an yi dariya sai dai yawan yinta akai-akai baya da fa'ida musamman kyakkyatawa.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) bai taɓa yin dariya ba saidai yakan yi murmushi.

Abu huraira ya rawaito hadisi inda yace Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) "yana cewa karkayi dariya da yawa, tabbas yawan dariya na busarda zuciya"

Al-tirmidhi,2305;Ibn Maajah,4193.

Idan muka dubi wannan hadisin to zamu ga cewa duk abinda ke busarda zuciya to a hakika yakan gusarda imani, domin zuciya ita ce tsoka mafi kyau da ake son ta gyaru wanda da zaran ta gyaru to a hakika dukkanin sauran ganganr jiki ya gyaru.(Hadisi)

Amma ayi fara'a, ayi annashuwa da raha, da murmushi da kalamai masu daɗi a tsakanin juna duka ba illa bane.

Wasu sun ɗauki yin dariya ta hanyar nishadi da kallon fina finnai na gusarda damuwa da yawan tinani wanda wannan ba haka bane, ba abinda ke saurin gusarda hushi da ɓacin rai a duniya tamkar sadaka da karatun Qur'ani. ko miye damuwarka to ka tsare hakan ka gani wallahi zaka samu waraka.

Don haka akwai bukatar mu kula da yanda muke yin dariya ganin wannan zamanin samuwar hanyoyin sadarwa na kara ta'azzara labaran barkwancin da ake ta yaɗawa daga shafukan sada zumunta na ' facebook da whatsapp' inda zaka ga labaran kirkire masu matukar barkwanci, gaya kuma Allah ya tsinewa duk mutumen dake zama ya kirkiro da labari dan ayi dariya.

Abinda yazo gameda Wanda zai furta wata kalma domin ya sa mutane dariya dubi: Hadisi na 2315.

A dubi: Abu dawud:4990.

A dubi: Sahihul jam'i:7136.

Daga: Bahazu bin Hakim daga Babansa daga kakansa (رضي الله عنهما)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments