Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Suke Sa Allah Ya So Mutum

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Mene ne Mutum Zai Aikata Allah Ya Soshi Sannan Mutane Su Soshi, Sannan Me Zai Aikata Su Kishi.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahamtullahi Wabarkatuh

Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana cewa; Ka guji duniya sai Allah ya soka, sannan ka guji abin hannun mutane (ka guji kwadayi) sai mutane su soka.

To abubuwan da yawa sunasa Allah ya so bawa daga cikinsu akwai

1. LALLAI ALLAH YA NA SON MASU ADALCI.

2. ALLAH YANA SON MASU TUBA SANNAN YANA SON MASU TSARKAKA.

3. ALLAH YANA SON MASU KYAUTATAWA.

Sannan akwai abubuwa da dama da zasusa Allah yaki mutum Kamar...

1. Ha'inci.

2. Ɓarna (fasadi).

3. Zalunci

Allah yana cewa: ALLAH BAYASON MASU YAWAN HA'AINCI. ALLAH BAYASON MABARNATA.

Da sauransu.

Sannan kyautatawa mutane yanasa mutane su so mutum. Haka munanamusu yanasasuji basu son mutum.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments