Mamana Daya Ya Fi Daya Girma, Ya Halatta Na Fada Wa Wanda Zan Aura

    TAMBAYA (87)

    Akwai wadda take tambaya tana cewa ya halatta ta gayawa wanda zata aura gaskia saboda mamanta daya da rabi ne wato daya yafi daya girma

    AMSA

    Alhamdulillah

    Wannan kam tayi kyan kai

    Bata bari kanta ya kulle ba, saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo

    Boyewar zai zamo matsala saboda watarana ai dole zai gano gaskiya. Ya halatta ta sanar dashi gaskiya

    Amman sanar dashi din (cikin siyasa) shine masalaharta kuma zai fahimce ta musamman ma ace mai addini ne

    Kowa da irin halittar sa, kuma kowanne mutum 9 yake bai cika 10. Duk kyawun mace a zahiri to a badini zaka tarar da muni, wanda kodai bakada ikon ganewa silar rashin iko da jikinta ko kuma bata sanar dakai ba saboda baka kai matsayin ka sani ba

    A shawarce kamata yayi idan zata sanar dashi ta fara ce masa;

    Nikam ina son nayi maka wata tambaya. Idan yace akan menene ? Sai ta ce masa me ka sani game da matan Aljannah, Hurul Ayn ?

    Me yiwuwa ya fara zayyano mata irin kyawun halitta da Allah Azzawajallah ya basu, irin kyawun fuskarsu da kyawawan idanuwansu, da kyakkyawar surar jikinsu da sauransu. To akan gabar nan, sai tace masa: "Tsarki ya tabbata ga Allah Subhanahu wata'ala wanda ina maka fatan ya aura maka Hurul Ayn a Aljannah, kamar yanda ya fada

    ( كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ )

    الدخان (54) Ad-Dukhaan

    Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.

    Mai yiwuwa yace Amin ya rabbal alamin. Sai tayi masa irin tambayar da Umm Salamah (Radiyallahu anha) ta yiwa Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) sai tace masa: "Shin Ya Rasulullah, tsakanin matan duniya da matan Hurul Ayn su wanene suka fi wasu ?"

    Da irin wannan firar ne zata kai ga fahimtar dashi cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Matan Aljannah sunfi na duniya kamardai yanda wajen riga yafi cikinta"

    [Kamar yanda hadisin yazo a cikin Tabarani; da Tafsir na Ibn Kathir]

    La'akari da su matan duniya sun bautawa Allah, sunyi sallah, azumi da sauransu sabanin Hurul Ayn wadanda kawai an halicce su ne domin mazajen duniya

    Sannan kuma su Hurul Ayn basa fitar da duk wata kazanta da matan duniya suke fitarwa kamar Jinin Haila wanda shi ya kasance cuta ce ga kowacce diyar Nana Hauwa'u (A.S) kamar yanda Allah Subhanahu wata'ala ya fada a cikin Suratul Baqara aya ta 222, saboda haka sakamakon jarabawar nan da Allah yayiwa matan duniya hakan zaisa darajarsu zata zarce ta Hurul Ayn

    Allan da zai iya jarabtar miji da tsufa har ya kasa tafiya sai da dogara sanda hakama zai iya jarabtar mace da tsufan da silar shayar da yayan ta sai abin shayarwar ta ya tsofe kamar dai wadda bata taba rayuwar budurci ba

    Sai ta ci gaba da ce masa;

    "Akwai wadanda ake haihuwarsu da ido daya, wasu kuma makafi, wasu da abin shayarwa daya, wasu kuma cutar cancer (dajin mama) ke zama silar da za'a yanke musu duka maman nasu. Ni dakai ba boye boye, 9 muke ba mu cika 10 ba, kamar yanda idon ka daya yafi daya girma, haka haqora na turame sunfi fiqa girma"

    "Kamar yanda maman Hurul Ayn girman su daya cif-da-cif haka mu kuma Banu Adam maman mu daya yafi daya girma. Kamar yanda likitocin ido (Optometrist) suka ce idon kowa daya yafi daya girma, haka kuma likitocin fata (human anatomist) suka ce mama (breast) din kowacce mace ba girman su daya ba. Wannan kadai ya isa ya tabbatar da cewar babu macen da take Perfect a bangaren surar halittarta har sai ta shiga Aljannah"

    "Sama da rabin matan duniya, maman su ba girman su daya ba, kuma masana sun gano cewar maman bangaren hagu yafi girma, harma masana suka ce banbancin girman yana kai kamar dunkulen hannun mutum, dalili kuwa shine: kowacce mace akwai yanayin halittar da Allah yayi mata na tsarin balagarta, wasu matan gado sukai, wasu kuma canzawar sinadarin hormones ne ke sa maman nasu wani yafi wani, wasu kuma nauyin jikinsu ne, wasu kuma shekarunsu ne, wasu kuma saboda jinin al'adarsu ne, da dai wasu dalilan dayawa. A Aljannah kuwa babu wannan cutar"

    "Sweetheart, ina son ka kuma ina qaunar ka saboda Allah, kuma fata na da buri na, da ni dakai mu shiga Aljannatil Firdous, mu sha Zanjabeel daga tafkin Salsabeel"

    Ina tunanin dole zai ce Amin thumma amin

    Wannan shine yanda nake hakaito firar da zaki tattauna dashi za ta kasance, ammanfa da sharadin zaki yi hakanne da kyakkyawar niyya ba wai don wata manufar ba, idan kikai haka za'a samu mafita guda biyu. Kuma dukkansu alkhairi ne a gareki;

    1) Idan yana da zurfin ilimi da tunani sosai zai iya gano cewar kin fadi hakanne saboda boye masa matsalarki na cewar mamanki daya da rabi ne, wanda a karkashin hakan, indai da gaske yana son ki to imanin da yayi cewar akwai Aljannah zai sa ya canza shawarar kawai bari yayi haqurin zama dake a haka ko kuma domin kuwa ya tabbatar da cewar acan Aljannah din za'a mai da ke kyakkyawar budurwa yar bana bakwai, wadda ta ninninka Hurul Ayn kyau, kuma wadda mamanta zai zamo girmansa daya da maqocinsa

    2) Idan har ya nuna kai wannan bari na haqura da auren ta (wanda hakan zai wahala - indai har kin iya masa bayanin kamar yanda nayi miki a rubuce) to hakan na nufin ba son ki da qaunarki yake don Allah ba, jikinki kawai yake so, wanda hakan na nufin idan kin tsufa (jikinki shima zai tsufa, haka ma maman naki dole su tsufa) to zai daina baki kulawa yanda ya kamata, kinga yaci moriyar ganga kenan, zai yada qauranta

    Idan har kinyi addu'ar Istikhara tun a karon farko to ba abin damuwa bane idan kun rabu tunda daman Allah kika bawa zabinki tun asali. Idan kuma bakiyi addu'ar ba (saboda rashin sani) sai ki yi ta don gudun kada Allah ya barki da zabinki

    Wannan shine shawarata a matsayi na na dalibin ilimi

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAnsa

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.