Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Sarrafa Nama (Soyayyen Nama, Tsire, Dambun Nama, Nama Da Karas, Nama Da Kabeji)

Gabatarwa

Babi na goma sha hu ɗ u (14) an gina shi ne sukutum kan bayanin nama da yadda ake sarrafa shi a ƙ asar Hausa . Kamar dai sauran nau’ukan abinci, yadda ake sarrafa nama a gargajiyance ba shi da wani bambanci mai tazara tsakaninsa da yadda ake sarrafa shi a zamanance. Bambancin ya fi shafar kayan ha ɗ i da kuma kayayyakin amfanin gida da ake amfani da su a lokacin aikin sarrafawar. Misali , yadda ake farfesun nama a gargajiyance, haka ake yi a zamanance. Kodayake, kayan ha ɗ in sun ɗ an bambanta. Zamani ya zo da nau’ukan kayan ɗ an ɗ ano da na ƙ amshi wa ɗ anda babu su a tsarin gargajiya. Za a iya lura cewa, a wannan  babi an tsallake wasu daga cikin nau’o’in dabarun sarrafa nama da ake da su na gargajiya. An yi hakan ne saboda ba su da bambancin a-zo-a-gani tsakaninsu da na zamani.

Soyayyen Nama

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kayan yaji

d. Magi

e. Mai

f. Nama

g. Ruwa

h. Tafarnuwa

i. Tarugu

j. Tattasai

A yayin samar da soyayyen nama, za a tafasa naman bayan an wanke . Yayin wannan  tafasawar, za a sanya kayan yaji tare da albasa . A ƙ a’ida, ba za a sanya ruwa da yawa ba, za dai a sa shi ne daidai gwargado yadda naman zai iya shanyewa. Bayan an tafasa shi, sai a soya shi sama-sama.

A gefe guda kuwa, za a jajjaga tarugu da tattasai da albasa  sannan a sanya sauran kayan ƙamshi da na ɗanɗado da ba a a sanya ba. Daga nan za a ɗan soya su sama-sama. Sai kuma a haɗe su da wannan  nama da aka soya. Bayan an haɗa, za a iya ƙara soya su tare ko kuma a ma bar su haka nan.

Tsiren Nama  Cikin Tukunya

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Gishiri

iv. Kori

v. Magi

vi. Mai

vii. Nama

viii. Ƙuli-ƙuli

ix. Ruwa

x. Tumatur

Za a wanke  naman, sannan a tafasa shi kamar dai yadda aka yi bayani a sama (haɗe da kayan ɗanɗano da na ƙamshi). Daga nan sai a jajjaga tarugu da tattasai a soya sama-sama. Sai kuma a daka ƙarago/ƙuli tare da kori a zuba saman naman. Wannan dakakken ƙarago za a zuba kan naman sannan a soye su tare.

Tsiren Nama

i. Albasa

ii. Citta

iii. Koren tattasai

iv. Kori

v. Magi

vi. Nama

vii. Ƙwai

viii. Ruwa

ix. Tafarnuwa

x. Tarugu

xi. Tumatur

A nan kuma, za a yi maganar tsire nau’i biyu. Nau’i na farko, bayan an wanke  naman za a tafasa shi da magi da albasa . Bayan ya tafasa, sai a ɗauko tattasai da tarugu da albasa waɗanda aka yanka ƙanana-ƙanana a haɗe wuri guda. Za a kawo tsinkaye a riƙa sossoka wannan  nama da kuma kayan lambu da aka yayyanka. Za su kasance a jere reras. Daga nan sai a barbaɗa  musu kayan yajin da aka tanada.

Nau’in tsire na biyu kuwa, ya bambanta da wannan  nau’i na farko. Yawanci mahauta ne suka fi yin sa. Kuma  irinsa ne ake sayarwa ko’ina kan hanya. Wannan nau’i na tsire ba ya buƙatar a tafasa shi. Za a yanka naman ne ƙanana sannan lafe-lafe. Sai a sanya su da yajin ƙarago, daga nan sai a jera su jikin tsinke. Za a caccaka waɗannan tsinkaye a gewaye da wutan da aka tanada. Yawanci akan yi hakan ne bisa abin da ake kira tukubar tsire. Za a riƙa juya su lokaci zuwa lokaci har sai kowane ɓ angare a jikinsu ya gasu.

Tsinken Nama

a. Albasa

b. Dankalin turawa

c. Gishiri

d. Magi

e. Mai

f. Nama

g. Ruwa

h. Thyme

i. Tumatur

Za a wanke  nama a yi masa yankan ƙwallo (wato ƙwalolo-ƙwalolo) sannan a sulala. A gefe guda kuwa za a yanka dankalin Turawa shi ma yankan ƙwallo, sai a sulala. Sannan sai a yanka albasa  da tumatur. Za a haɗe naman da aka sulala da dankali wuri guda, sannan a sanya kayan ƙamshi da kayan yaji, sai kuma a riƙa sokawa a tsinke. Misalin yadda ake sokawa kuwa, idan an saka nama yanka guda, sai a sanya dankali, sai tumatur da kuma albasa. Bayan an kammala, sai a sanya cikin mai domin suya.

Dambun Nama

i. Albasa

ii. Attarugu

iii. Gishiri

iv. Kayan ƙamshi

v. Magi

vi. Nama

vii. Ruwa

Za a tafasa nama da kayan ƙamshi da kuma kayan ɗanɗano tare da ruwa kaɗan. Idan naman yana da yawa, ba a fiye ƙara ruwa ko kaɗan ba, domin ɗan sauran ruwan da aka wanke  naman da shi ya isa ya tafasa shi. Akan sanya albasa  a ciki domin ƙara masa ƙamshi da kuma kawar da ƙarnin da ke tattare da shi.

Da zarar naman ya tafasa yadda ake buƙata, sai a jajjaga tarugu da albasa  a soya sama-sama. Naman kuwa da aka tafasa, za a sanya shi cikin turmi  a ɗan daddaka har sai ya ɗan fara watsewa. Akan iya saka shi a bilander a maimakon turmi. Daga nan za a haɗe naman da jajjagen kayan miyar da aka yi, sannan a sanya cikin tukunya , a ɗan ƙara mai kaɗan a ci gaba da juyawa. Haka za a ci gaba da yi har sai ya nuna sarai.

Nama  da Karas

i. Alayyafu

ii. Albasa

iii. Gishiri

iv. Karas

v. Kayan Yaji

vi. Magi

vii. Mai

viii. Nama

ix. Ruwa.

x. Tafarnuwa

Za a wanke  nama a tafasa tare da albasa  da kayan ɗanɗano. Gefe guda kuwa za a goge karas. Daga nan sai a ɗauko wannan  tafasasshen nama a sanya a tukunya  tare da mai kaɗan domin suya irin ta dambu. Ana cikin wanan suya ne za a sanya tanadajjen karas ɗ in da aka yanka tare da wannan alayyafun da aka yanka ƙ anana, za kuma a sanya kayan yaji a ciki.

Kabeji Da Nama

i. Albasa

ii. Dankali

iii. Gishiri

iv. Kabeji

v. Karas

vi. Kori

vii. Magi

viii. Mai

ix. Nama

x. Ƙwai

xi. Ruwa

Za a yanka kabeji manya-manyan yanka, sai a sanya shi a cikin tukunyar da ke bisan wuta  domin ya yi tafasa guda. A gefe guda kuma, za a yanka karas da dankali ƙananan yanka, sai a soya su sama-sama cikin mai. Daga nan sai a tafasa nama tare da kayan ɗanɗano. Za a yayyanka wannan  tafasasshen nama ƙanana-ƙanana sannan a soya shi a ajiye gefe guda. Daga nan za a kaɗa ƙwai cikin wata roba ko kwano sannan a haɗe naman da kabeji da kuma karas. Za a zuba zuba su cikin mai a soya gaba ɗaya.

Kammalawa

Ha ƙ i ƙ a , Ubangiji Y a wadata ɗ an Adam da nau’o’in nama iri-iri. Wannan babin ya kawo wasu nau’o’i ne k a ɗ an daga cikin wa ɗ anda ake da su. Sai dai za a iya ha sa shen cewa, hanyoyin sarrafa nama a ƙ asar Hausa  ba su wuce wa ɗ anda aka bayyana a sama ba. Sai dai akan samu wasu ‘yan bambance-bambancen da ba za a rasa ba. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments