Ticker

6/recent/ticker-posts

Kallon Blue Film Don Motsawa Sha'awa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko ya halatta ma'aurata su kalli blue film don sha'awarsu ta motsa sosai sannan kuma su koyi nau'ikan yadda ake yin kwanciyar jima'i dabam-dabam?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ko shakka babu cewa shari'ar muslunci ta zo ne tayi yaƙi da dukkan wani abu wanda yake ɓarna ce da fasadi a bayan ƙasa, kuma ta yanke dukkan wata hanya da za ta kai mutum zuwa ga wancan fasadi, dan haka shari'a ta haramta yin dukkan wani nau'i na kallo irin na sha'awa da namiji zai yiwa wata mace wacce ba matarsa ba, haka nan itama mace bai halatta ba ta yi wa wani namiji kallo na sha'awa wanda ba mijinta ba, to balle kuma ace tsiraicin ne kansa ake kallo saboda Aʟʟαн() Yana cewa

قُل لِّلْمُؤْمِنِينَ يَغُضُّوا مِنْ أَبْصَارِهِمْ وَيَحْفَظُوا فُرُوجَهُمْ ذَلِكَ أَزْكَى لَهُمْ،.............إلَيخ

MA'ANA

Aʟʟαн() Ya ke cewa) ka gayawa muminai su rintse idanunsu (ga barin yiwa wasu kallo na sha'awa) domin yin hakan shi ne yafi tsarkaka a garesu……… har dai zuwa ƙarshen ayar: (Suratul Nūr aya 30)

A saboda haka Malamai sukace ba ya halatta mutum ya kalli blue film ko shi kaɗai ko kuma tare da matarsa, haka nan ba ya halatta mutum yake karanta wani dukkan wani labari irin wanda zai motsawa mutum sha'awarsa, domin kuwa waccan ayar hukuncin da ke cikinta ya game dukkan wani abu da ya ke da alaƙa da hakan, ko a zahiri ko a film ko a rubuce cikin littafi ko kuma a jikin wani hoto, Ko a blue film irin na Cartoon, ko kuma ayi zanen surar abinda zai iya motsa sha'awar mutum a jikin takarda. To dukkansu hukuncinsu ɗaya ne, domin Aʟʟαн() Ya na cewa

"إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا"

MA'ANA

Haƙiƙa dukkan abinda kunne zai ji, ko idanu ya gani, ko abinda zuciya ta ƙunsa, to dukkaninsu ababan tambaya ne (a gaban Aʟʟαн(): (Suratul Israa  aya 36)

Saboda haka kallon blue film ta kowacce irin hanya bai halatta ba, balle a fake da cewa wai ai ana so a koyi Style ne. Ai abin kunya ne ma ace wai mutum musulmi ya koyi yanda ake yin jima'i daga wajen dabbobi, (ma su yin Blue-Film) sannan kuma jima'i ai ba koyonsa ake ba, kowa da iliminsa aka halicceshi, kuma muslunci ya koyar da mu hanyar da ma'aurata za su bi don su motsa sha'awar junansu ta hanyar yin wasanni a tsakaninsu kafin su kai ga saduwa. Dan haka kenan babu wani buƙatar wai sai an kalli blue film sannan sha'awa za ta motsa.

Wasu mutanen kuma sai su fake da cewa wai larurace tasa suke kallo saboda wai suna da raunin sha'awa, amma idan suka kalli blue film wai nan take sha'awarsu za ta motsa, to suma su sani cewa bai halatta su kalla ba domin wannan ba zai iya zama musu dalili na su kalli blue film ba, kenan idan haka ne ai akwai mutanen da za su sha giya amma komai yawanta ba za ta sa su maye ba, amma duk da kasancewar giyar ba ta sa su maye hakan ba zai iya halatta musu cewa su riƙa shan giya ba.

Sannan wani abu da mutane ba sa kula dashi anan shi ne galibin ma'auratan da za su kalli Blue film kafin suyi jima'i za ka samu cewa a lokacin da suke yin jima'in to waɗancan abubuwan da suka kalla shi suke surantawa a cikin zuciyarsu a haka har mutum ya gama biyan buƙatarsa.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαм

​​

           Mυѕтαρнα Uѕмαn

              08032531505

​​Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments