Ticker

6/recent/ticker-posts

Miji Mai Yin Ball

TAMBAYA (62)

Assalamuh alaikum. Mlm enada tambaya neh. Meneneh hukunchin mijih maiyin ball

AMSA

Alhamdulillah

Ita kanta ball idan mutum yana yi bazaka ce sabo yake aikatawa ba, saidai haramcin yana zuwa ne ya yinda aka duba abubuwan da suke kewaye ball din kamar yanda kowacce sana'a sabo zai iya kewayeta

Misali: lokacin sallah, azumi, gajeran wando saboda cinya tana fitowa kuma cinya al'aurace

To amman babbar al'aurace qaramar al'aurace ?

Idan kabi fatawar Ibn Hazm to cinya ma ba al'aura bace hujjar hakan shine; Sayyadina Usman RA ya ga cinyar Annabi SAW. Da ace babbar al'aurace da Annabi SAW bazai bari Sayyadina Usman Bin Affan RA ya ga cinyarsa ba

Babbar al'aura itace: duwawu da kuma gaban mutum

Abin kiyayewa shine; wando yazo gwiwa, saman kuma ya wuce cibiya

Idan kika duba littafin mai ahlari yace: al'aurar namiji tana farawa ne daga cibiya zuwa gwiwa

Sannan kuma sai azo batun kudin da yake samu (salary idan har ya maida ita sana'arsa kenan) kuma yake ciyardake ya shayar dake ya kuma tufatar dake, menene hukuncin wannan kudin, halak kuke ci ko kuma haramun ne ?

Anan za'a duba asalin tushen kudinne, bi ma'ana; idan ya zamana yasan cewar kamfanin giya da makamantansa ne suka dauki nauyin kungiyar kwallon kafar tashi to haramun yake ci idan kuma kamfanin kasuwanci ne ko kuma coach dinnasu yana harkar kasuwanci ne yana zuba hannun jari to anan baza'a haramta abinda yake samu ba indai har ya kiyaye dokokincan guda 3

Idan kuma yana yin ball dinne a matsayin motsa jiki wannan kada ki takura masa indai har yana kiyaye wadancan matakan guda 3 domin kuwa wannan motsa jikin yanada matuqar amfani ga lafiyar kowanne mutum namiji da mace

Sannan kuma abu na karshe shine yakamata ya dinga ball din a matsayin exercise bawai a matsayin abin burgewa da koyi da yahudawa ba domin kuwa daman asalinta sun kawota ne kasar Spain (Andalusia) suka rushe masallatai da makarantun addininmu na musulunci suka gina stadium din ball don ganin sun rabamu da addinin gaskiya

Alhalin Imamul Qurtubi (Malamin Tafsir dinnan) dan kasar Spain ne, hakama Abbas Ibn Firnas da ake kirada Father of Aviation (Wanda ya bude kofar yiwuwar qirqiro jirgin sama ta hanyar daure jikinsa da wasu abubuwa kamar fuka-fukai ya hau saman bene ya fado yana shawagi kamar tsuntsu a sama) duk yan kasar Andalusia ne, da sauran malaman musulunci wadanda lokaci bazai bawa alqalami na damar zayyanosu ba

A binciken da masana sukayi duk cikin mutane 5 na kasar Spain da akwai dan kwallo guda 1, kuma gashi an cusa mana aqidar kallon ball. Kamata ya yi yanda samari suke zuwa kallon ball su maida hankali wajen sanin addininsu da hukunce hukuncensa a makarantu

Sun ja ra'ayin wasunmu kuma suna samun kudi damu a duk lokacin da muka saka data muka kallesu ko kuma muka biya kudi muka shiga gidan kallo. Dr. Bashir Sani Sokoto yace; shin ko mutane sun san cewar a binciken da masana sukai na shekarar 2019 Real Madrid tanada a qalla 4.2 billion US dollars a asusunta, Barcelona na da 4.02 billion dollars, Manchester United sunada 3.81 billion dollars. Magana ake ta tiriliyoyin nairori fa

Idan zaka hade jimullar kudaden clubs dake kasashen waje gaba daya, idan da za'a siyar dasu, tareda stadium dinsu da yan ball din, sun doshi 24.094 billion US dollars. Wannan a bangaren wasannin iya football fa kenan shiyasa suka fi jan ra'ayin samari a wannan bangaren. Kuma a haka akwai project da Amurka sukayi na titin hawa (road) wanda ya ninninka wancan kudin har sau 3. Iya budget din Amurka na sati daya yafi budget din Nigeria na shekara guda. To wadanne kudade kake tunanin Amurka ta ware don ganin ta rusa musulmai da addininnamu na musulunci gaba daya ?. Iya budget din da Amurka tayi na 2015 yakai 3.7 trillion US dollars, a shekarar 2016 3.9 trillion US dollars, 2017 yakai 4 trillion US dollars. Idan da ace za'a siyarda dukkan clubs da ake dasu a duniya bazasu kai 1 trillion US dollars ba, kai ba ma zasu kai 200 billion dollars ba. Sannan a shekarar 2020 budget din Amurka yakai 4.8 trillion US dollars

A iftila'in 9/11 (wato 9 ga watan September, 2001) kadai Amurka ta rasa kudaden da zasu kai adadin da za'a iya siyan clubs irinsu Real Madrid guda 50. Sun sako bombs a cibiyar kasuwanci ta duniya (World Trade Center dake birnin New York) kawai don su dakushe musulunci kuma da suka tashi sai sukace ai Osama Bin Laden ne ya sako bama-baman, amman a binciken qwaqwaf da akai an tabbbatar da cewar Yahudawa ne suka tsara abin da taimakon gwamnatin Amurka dan dai kawai a shafe musulunci kuma a sakawa mutane tsanar musulman duniya baki daya

A daidai kan wannan gabar yakamata na jefa qalubale ga matasa musamman wadanda suke bata lokaci wajen asarar data suna kallon wasan kwallo live

A shawarce wadannan sune sunayen litattattafai guda 24 da yakamata mu je mu karanta mu fahimcesu domin amfanuwarmu, domin kuwa na amfana dasu matuqa kuma ina kwadayin yan uwa, iyaye da abokan arziqin dake wannan group na tambaya da amsa su amfana dasu

Ga littattafan kamar haka;

1) Sifatu Salatin Naby PDF (Siffar yanda Annabi SAW ya yi sallah, wallafar Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany (Rahimahullah)

Ya suffanta tare da kawo bayanai daki-daki akan yanda Annabi SAW ya koyar da yanda ake sallah dogaro da hujjar hadisin "Sallu kama ra'ayta muni usalli" bi ma'ana: "Kuyi salah kamar yanda kuka ga ina yi". Don haka ya zama dole kowa ya koyi sallah irin yanda Annabi SAW ya koyar. Kamar yanda muka sani cewar kowa yana cikin dayan biyu ne: immadai kana sallah ne a al'adance (kamar yanda ka taso ka ga ana yi) ko kuma kana sallah ne a addinance (yanda Ma'aiki SAW ya koyar)

2) Zaadil Ma'ad (Guzirin Alqiyama, wallafar Imam Ibn Qayyim al-Jauziyya (Rahimahullah)

A cikin littafin mai suna "Guzurin Alqiyama" ya yi bayani daki-daki dangane da kyawawan dabi'u tare da ayyukan Annabi SAW. Zanso mu mallaki littafin domin amfanuwa da ilimin da ya qunsa

3) Albidaya wan Nihaya (Farko da Karshe, wallafar Abubakar Alhafiz Ibn Khathir (Rahimahullah)

Littafi ne wanda ya yi bayani tun daga farkon halittar Alqalami, Al-Arshi, Kursiyyu, Sammai da Kassai da tarihin Annabawa har zuwa shiga Wuta (Allah ya tsaremu) ko Aljannah (Allah ya shigar damu), ya kawo bayananne da hujjoji a cikin Qur'ani da Hadisai. Duk wanda ya karanta wannan littafi to haqiqa zai kara sanin yanda rayuwa take kuma tunanin mutum zai canza saidai idan mutum bai karanta littafin ba

4) Talbis iblis (Yaudarar iblis, wallafar Imam Abdurrahman Aljauzi (Rahimahullah)

Yayi namijin qoqari wajen ganin ya ilimintar da mai karatu da koyar dashi sanin hanyoyin da iblis yake bi yana kafa tarkonsa don batar da malamai da jahilai. A wannan zamanin mai cike da qalubale da son abin duniya, ina shawartar kowa ya karanta wannan littafin don ganin ka nesanta kanka daga tarkon iblis

5) The Evils of Music: Devil's Voice and Instrument (Sharrin kade-kade: sautin shaidan da kayan kidansa, wallafar Ibn Qayyim Aljauziyya (Rahimahullah)

A cikin littafin: "Sharrin kade-kade: sautin shaidan da kayan kidansa", ya yi bayani akan illar sauraren kida da kuma narkon azabar da Allah ya tanada ga wadanda suka mutu suna jin kida basu tuba ba da kuma gargadi akan za'a hana mutum jin kida mai dadi a Aljannah. A wannan zamani na kide-kide ya zama kusan dole mutum ya nemi wannan littafin ya karanta don katange kai daga fadawa fushin Allah Azzawajallah

6) Music Made Me Do It (Jin Kide-kide ne sila, wallafar Dr. Gohar Mushtaq)

Dr. ya yi bayanai daki-daki akan yanda jin kida ya zama silar kurmancewa da mutuwar masu saurare, ya yi bayani akan illar jin kida ga lafiya da kuma ruhin mutum. ya yi jan hankali akan jin kida yana haddasa munafurci kuma yana kawo mummunan qarshe, ya kafa hujja da hadisai sahihai. Lallai yakamata mu nemi wannan littafi sannan mu nusar da mawaqa masu saka kida a wakensu sharrin dake tattare da saka wannan kidan

7) Natural blood of women (Jinin Mata, wallafar Shaikh Saleh al-Uthaymeen (Rahimahullah)

Ya tattauna matsaloli akan jinin mata, kama daga jinin haila, haihuwa da na ciwo. Yakamata kowacce mace tasan ilimi akan rabe-raben wadannan jinane masu rikitarwa a dabi'ance tareda sauqin ganewa a addinance

8) Guidelines to intimacy in islam (Shiriya akan alaqar auratayya a musulunce, wallafar Mufti Ahmad Ibn Adam Alkautary)

Yayi bayani sosai kuma daki-daki akan yanda Annabi SAW ya koyar da al'ummarsa yanda ake rayuwar auratayya. Qalubale ga gwauro da gwauruwa wadanda basuda ilimin sanin hakan kuma gashi suna da niyyar aure

9) Newborn baby guide (Shiriya ga Jarirai, wallafar Ibn al-Qayyim Aljauziyya (Rahimahullah)

Ya rubuta littafinne a matsayin kyauta ga qanwarsa a lokacin da ba shi da ko da riga daya da zai bata a matsayin tukwici a lokacin da ta haihu, sai gashi Allah SWT ya albarka littafin ga shi muna amfana dashi. ya yi bayanai akan yiwa jariri kiran sallah, sakawa jariri suna, yin aski, kaciya, yanka da sauran bayanai dai da hujja a Qur'ani da sahihan hadisai, kai abin sai wanda ya karanta dai

10) Ahkamul Jana'iz (Hukunce-hukuncen Jana'iza, wallafar Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany (Rahimahullah)

A wannan zamani wanda ake bidi'o'i kala-kala ya yin aiwatarda ibada Jana'iza, zakaga mutane suna abubuwan irin na zamanin jahiliyya a sakamakon hakanne Malam Albany ya rubuta littafin da hujja a cikin Qur'ani da sahihan hadisai akan yanda Annabi SAW ya koyar. Allah ya bamu ikon ilimantuwa

11) Evil eye is real (Kambun ido gaskiya ne, wallafar Ahmed Abdurrahman)

Malamin ya tattaro bayanai a Qur'ani da hadisai akan sharrin kambun ido da kambun baka. La'akari da mun tsinci kanmu a zamani na social media zakaga musamman yanda mata suke dora hotunansu, yakamata mu karanta wannan littafi don neman kariyar Allah SWT daga sharrin masu kambun ido

12) Reclaim your heart (Mallakar zuciya, wallafar Ustadha Yesmin Mogahed)

Malama Yesmin tayi matuqar qoqari wajen janyo hankalin mutanen da munanan dabi'unsa suka nesanta da kwaikwayon kyawawan dabi'un wasu. Na amfana da littafin matuqa

13) Unchallengeable Miracles of the Quran (Mu'ujizozin Qur'ani, wallafar Caner Taslaman)

Ban taba karanta littafi mai abin mamaki da dadi irin wannan ba, domin kuwa mawallafin ya tattaro bayanai musamman na kimiyya ya fayyace su, haqiqa ba'a taba littafi kamar Qur'ani ba haka kuma baza'a taba yi - domin kuwa shi ne sha karatu

14) Reviving the Abandoned Sunnah (Dabbaqa sunnonin da aka qyale, wallafar Abdulmalik Alqasim

Ya kawo sunnoni guda 45 da Annabi SAW ya koyar ga al'ummar sa. Na amfana da wannan littafin kuma yakamata duk wanda yake son samun ladan koyi da sunna to ya karanta wannan littafi

15) Jokes of the prophet in the Hadith (Barkwancin Annabi SAW a cikin hadisi, thesis/program din wani dalibi ne daga jami'ar musulunci dake Walisongo, Semarang)

Dalibin ilimin ya kawo hadisai akan yanda Annabi SAW yake barkwanci a cikin wasu al'amuransa. Kamar labarin tsohuwar nan da Annabi SAW yace mata tsofaffi basa shiga Aljannah, ta fara kuka, sai yace mata ai yana nufin sai an maida ita budurwa, sai tayi dariya. Zanso mu karanta wannan littafin domin kuwa na amfana dashi matuqa musamman ta fuskar barkwancina ga yan uwa da abokan arziqi da nake zama tare dasu

16) Looking into the eye of the Dajjal (Ganin idon Dajjal a ilimance, wallafar Abu Muhammad Ibn Dawood)

Na amfana da karanta wannan littafin domin kuwa mawallafin ya yi bayani sosai akan sharrin da yake tattare da bayyanar Dajjal, cewar tun da aka halicci Annabi Adam AS ba'a taba wani bala'i sama da bayyanar Dajjal ba, mu sani cewar duk wanda neman kudi ne abin son sa fiyeda addini to tabbas zai wahala ya qetare fitinar Dajjal. Mafita shine karanta addu'ar da Annabi SAW ya koyar bayan kowacce Tahiyya kafin sallama. Allah yasa mudace

17) Prophet's Wudoo (Alwalar Annabi SAW), fassarar Dawud Durbank)

Ya kawo bayanai daki-daki akan yanda Annabi SAW yake yin alwala da hujjoji a cikin sahihan hadisai. Munsan dai babu sallah ga wanda ba shi da cikakkiyar alwala

18) World of The Jinn and Devils (Duniyar Aljanu da Shaidanu, wallafar Dr. Umar S. al-Ashqar)

Ya kawo bayanai akan yanda Aljanu da shaidanu suke rayuwa da kuma yanda suke hidima ga shugabansu wato iblis, da hujjoji a cikin Qur'ani da sahihan hadisai. Na amfana da littafin sosai

19) Ranking of the 100 Most Influential Persons in History, by Michael H. Hart - Prophet Muhammad No. 1 (Mutane 100 da suka fi kowa daraja a tarihin duniya, Annabi Muhammad SAW shine na 1, wallafar Michael H. Hart

Duk da cewar mawallafin ba musulmi bane ba amman yace Muhammad SAW shine mutum na farko a cikin shahararrun mutane 100 da suka fi daraja da samun daukaka a tarihin duniya. Littafin ya janyo cece-kuce, yace ni kaina Christian ne amman na tabbata Muhammad (SAW) ya fi Jesus komai. Allahu Akbar ! Daman tuni Allah SWT yace "Wallahu ya'asimuka minannasi". Zanso mu karanta wannan littafin domin hakan zai kara mana son masoyinmu Annabi Muhammad SAW

20) The Day of Judgement Preparing for the Hereafter (Ranar lahira, shirye-shiryen alqiyama, wallafar Shaik Muhammad al-Wasaabee)

Yayi bayanai daki-daki akan bala'o'in da suke tattare da ranar alqiyama, da kuma shirye-shiryen da ya kamata mumini ya yi don ganin ya samu dacewa da gidan Aljannah

21) Purifications of the heart (Tsarkake zuciya, wallafar Shaikh Hamza Yusuf Hanson)

Ban taba karanta littafin da ya yi bayani sosai akan yanda zaka tsarkake zuciyarka ba sama da wannan littafin. Abin dai sai wanda ya karanta kuma ya fahimta

22) Signs of the Last Day (Alamomin tashin alqiyama, wallafar Harun Yahya)

Yayi bayanai akan alamomi manya da kanana da suke da alaqa ta kai tsaye da tashin alqiyama. Saidai na cewa masu karatu - Allah ya bada ikon amfana da ilimin da ke ciki

23) The Soul Journey (Tafiyar Ruhi, wallafar Ibn al-Qayyim Aljauziyya (Rahimahullah)

Yayi bayani akan yanda mala'iku suke rejistar ruhin musulmi a saman bakwai a littafin illiyyin (Na yan Aljannah) - Allah yasa muna ciki, ya yinda kafirai kuma ake rejistar sunansu a kasan bakwai a littafin sijjin (Na yan wuta) - Allah ya tsaremu. Na qaru matuqa silar karanta wannan littafin

24) Aljannah wan Nar (Aljannah da Wuta, wallafar Imam al-Qurtubi (Rahimahullah)

To anan ne fa da ni dakai mai karatu zamu tsinci kanmu, ko dai a wuta (Allah ya tsaremu ba don halinmuba) ko kuma a Aljannah (Allah ya dawwamar damu a ciki ba don halinmu ba

Wadannan sune littattafan da naga ya dace na danyi tsokaci akan yakamata da ke da mai gidanki da sauran ma'aurata ya kamata su karanta a maimakon su bata lokaci wajen kallo ko kuma buga ball

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments