Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Yasa Musulunci Ya Hana Musulma Auren Kirista, Amma Ya Halattawa Musulmi Auren Kirista?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam wasu Arna ne suka mana tambaya a makaranta cewa: Yaya aka yi addinin Musulunci ya halattawa namiji Musulmi auren kirista mace, amma ya hana a baiwa kirista namiji auren Musulma? Malam mun rasa amsar da za mu ba su, shine muke so ka taimaka mana, don kar su samu hanyar da za su aibanta addininmu.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To, 'yar'uwa Sheikh Aɗiyya Muh'd Salim ya yi ƙoƙari wajen warware wannan mushkilar a ƙarashen tafsirin Adhwa'ulbayan da ya yi, inda ya ambaci dalilai guda biyu, wadanda suka hukunta hakan

1. Kasancewar Musulunci shine yake yin sama, amma ba'a yin sama da shi, idan kirista ya auri Musulma, zai zama yana sama da ita, tunda namiji shine yake bawa mace umarni idan ya aure ta, saɓanin idan namiji Musulmi ne ya auri mace kirista, tunda shi zai zama a samanta.

2. Musulmi ya yi imani da Annabi Isah (A.S.) da kuma Injila, wannan zai sa idan ya auri kirista zai girmama ta, shi kuwa kirista bai yi imani da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi Wasallam) ba, don haka zai iya wulakanta Musulma idan ya aure ta, tunda bai san darajar addininta ba, wadda hakan zai sa su kasa fahimtar juna, zaman auren ya ta'azzara.

 Duba Adhwa'ulbayan 8/164

Allah ne mafi sani.

Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments