Ticker

6/recent/ticker-posts

Farfesun Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Kayan Lambu, Gasasshiyar Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Nama, Farfesun Kifi Da Kayan Lambu, Soyayyiyar Fara

Wannan rubutu ya kawo bayani game da yadda ake Farfesun Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Kayan Lambu, Gasasshiyar Kaza, Soyayyiyar Kaza Da Nama, Farfesun Kifi Da Kayan Lambu, Soyayyiyar Fara. Ku turo mana sharhi ko tambayoyi a sashen comment da ke ƙasa.

Farfesun Kayan Ciki

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kayan ciki

d. Kayan yaji

e. Magi

f. Mai

g. Ruwa

h. Tafarnuwa

i. Tarugu

j. Tattasai

k. Zogale

Za a wanke  nama, sannan a tafasa tare da albasa  da kayan da kayan ɗanɗano da kayan yaji. Bayan ya tafasa, idan akwai sauran ruwa cikin tukunyar akan zubar da shi. A gefe guda kuwa za a yi jajjagen tarugu da tattasai da albasa, sannan a soya su sama-sama tare da kayan yaji. Idan waɗannan sun samu, sai a yi sanwa da ɗan ruwa kaɗan ba mai yawa ba. Bayan ruwan ya tafasa, sai a sanya wannan  jajjage da nama ciki. Sannan sai a wanke zogale  ɗan daidai ba mai yawa ba a sanya ciki. Haka za a bar su su ƙarasa nuna tare.

Soyayyiyar Kaza Tare Da Kayan Lambu

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Kabeji

iv. Karas

v. Kayan yaji

vi. Kaza

vii. Kori

viii. Kukumba

ix. Magi

x. Mai

xi. Ruwa

xii. Tarugu

xiii. Tattasai

Yadda ake soyayyen nama, haka ake sarrafa wannan  nau’in nama na soyayyiyar kaza da kayan lambu. Bambancin kawai shi ne, a nan akan sanya kayan lambu iri-iri kamar yadda aka bayyana a sama.

Gasasshiyar Kaza

i. Attarugu

ii. Gishiri

iii. Kaza

iv. Kori

v. Magi

vi. Mai

vii. Ruwa

viii. Tafarnuwa

Bayan an yanka kaza an fige an wanke , za a tsaga ta ta ƙasa ko sama daidai yadda za a iya cire kayan cikin (ba tare da an feɗe ba). Daga nan sai a sake wanke ta sarai. A gefe guda kuwa, za a jajjaga kayan lambu sannan a soya su sama-sama. Za a sanya wannan  jajjagen da aka soya cikin kazar. Wajenta kuwa za a shafe shi da magi wanda aka ɗan kwaɓa. Yawanci akan yi amfani da zare domin a ɗaure wurin da aka tsaga domin fitar da kayan ciki (wanda kuma ta nan ne aka sanya jajjagen da aka soya). Daga nan za a tura cikin obun. Idan ba obun kuwa, sai a ayi amfani da madambaci.

Gasasheyar Kaza Banƙarara

i. Barkono (tonka)

ii. Gishiri

iii. Kayan yaji

iv. Kaza

v. Magi

vi. Mai

vii. Ruwa

viii. Tafarnuwa

Yadda ake sarrafa wannan  nau’i na nama na matuƙar kama da yadda ake tsire na kan tukuba. A nan bayan an gyara kaza, akan feɗe ta a banƙare sannan a tsire da tsinke. Haka a banƙare za a ajiye ta gefen wuta . Zafin wutan ne zai gasa ta har ta dawo kamar an soya.

Soyayyar Kaza Da Nama

i. Albasa

ii. Dankalin Turwa

iii. Gishiri

iv. Kabeji

v. Karas

vi. Kaza

vii. Magi

viii. Mai

ix. Nama

x. Ruwa

Wannan nau’in sarrafa nama daidai yake da sauran nau’o’in suyar nama. Bambancin kawai shi ne, a nan ana haɗa naman sa ne ko na rago (ko makamancin waɗ annan) da na kaza.

Farfesun Kifi da Kayan Lambu

a. Albasa

b. Citta

c. Kayan miya

d. Kifi

e. Koren tattasai

f. Mai

g. Ruwa

h. Tafarnuwa

Za a yi amfani da lemon tsami  ko ɗoɗoya domin a wanke  kifi, sai a sanya shi domin ya tsane. A gefe guda kuwa, za a jajjaga tattasai da tarugu da albasa  a soya sama-sama (za a iya amfani da su ba tare da an soya ba). Bayan waɗ annan sun samu, sai a tanadi kayan yaji. Sannan sai a goge karas a kuma yayyanka koren tattasai.

Bayan waɗannan duka sun samu, za a ɗora sanwa da ruwa kaɗan, daidai adadin kifin da ake da shi. Bayan ruwan ya tafasa, sai a sanya wannan  kifi. Da zarar ya fara jin wuta , sai a saka jajjagen da aka tanada da kuma karas da koren tattasai.

Soyayyan Kifi Da Soyayyiyar Miya

i. Albasa

ii. Gishiri

iii. Kifi

iv. Magi

v.   Ruwa

vi. Tarugu

vii. Tattasi

viii. Zogale

Za a wanke  kifi sannan a soya shi tare da magi da albasa . A gefe guda za a jajjaga tattasai da tarugu sannan a soya su. Za a sanya kayan yaji yayin soyawar, sannan kuma za a watsa zogale  a cikin wannan  soyayyen jajjagen.

Soyayyiyar Fara

i. Albasa

ii. Barkono (tonka)

iii. Fara

iv. Gishiri

v. Haɗaɗɗen Yaji

vi. Magi

vii. Mai

Za a gyara fara sarai a cire gashin da ke jiki, sai kuma a tafasa ta. Bayan ta tafasa sai a zubar da wannan  tafasasshen ruwan. Za a ajiye wannan fara ta sha iska har sai ta fara bushewa. Daga nan za a cire cinya da fiffike a jiye su daban. A gefe guda kuma za a tanadi kayan yaji. Za a iya sanya waɗannan kayan yajin kafin a soya ta. Za kuma a iya ajiye kayan yajin har sai an kammala soyawa kafin a saka.

 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments