𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wanda ya kashe kafiri ko zai yi kaffara?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Malamai sun ce: kafirai nau’i-nau’i ne: Waɗanda ake yaƙi da
su da waɗanda ba
haka ba. Waɗanda ba
a yaƙi
da su kuma nau’uka uku
ne: Zimmiyai da Mu’aahadai
da kuma Musta’amanai.
1. ZIMMIYYAI su ne waɗanda
aka ƙulla
alƙawarin
zaman tare na aminci tsakaninmu da su.
2. MU’AAHADAI su ne waɗanda
aka ƙulla
yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙi a tsakaninmu da su.
3. MUSTA’AMANAI kuwa su ne waɗanda
suka shigo garinmu cikin aminci domin kasuwanci ko wani aiki ko ziyarar ɗan’uwa da sauransu.
Musulunci bai yarda a kashe wani daga cikin waɗannan nau’ukan guda uku
ba saboda maganarsa (Subhaanahu Wa Ta’aala) cewa
وَمَا
كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَنْ يَقْتُلَ مُؤْمِناً إِلا خَطَأً، وَمَنْ قَتَلَ مُؤْمِناً خَطَأً
فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ، وَدِيَةٌ مُسَلَّمَةٌ إِلَى أَهْلِهِ إِلا أَنْ يَصَّدَّقُوا،
فَإِنْ كَانَ مِنْ قَوْمٍ عَدُوٍّ لَكُمْ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ،
وَإِنْ كَانَ مِنْ قَوْمٍ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ مِيثَاقٌ فَدِيَةٌ مُسَلَّمَةٌ إِلَى
أَهْلِهِ وَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ، فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ
مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً مِنَ اللَّهِ، وَكَانَ اللَّهُ عَلِيماً حَكِيماً
Bai kamaci mumini ya kashe wani mumini ba sai dai a bisa
kuskure. To, duk wanda ya kashe mumini a bisa kuskure sai ya ’yanta baiwa
mumina, da kuma diyya da za a bayar ga dangin mamacin, sai dai ko in sun yafe.
Idan kuwa daga cikin mutane ne maƙiya gare ku alhali kuma shi musulmi ne,
to sai ya ’yanta baiwa
mumina. Idan kuwa yana daga cikin mutane ne da kuke da alƙawarin
aminci a tsakaninku da su, to akwai diyya abin bayarwa ga iyalinsa, da kuma ’yanta baiwa mumina. Wanda
kuma bai samu iko ba sai ya yi azumin watanni biyu a jere. Wannan hanyar samun
tuba ce daga Allaah. Kuma Allaah ya kasance Masani ne Mai Hikima. (Surah
An-Nisaa’: 92).
Ƙarshen wannan ayar ta nuna, wanda ya kashe kafirin da
musulunci ya tsare jininsa, akwai abubuwa biyu a kansa
1. DIYYA: Wacce zai bayar ga dangin mamacin, muddin dai babu
yaƙi
a tsakaninmu da danginsa.
2. KAFFARA: ’Yanta baiwa mumina, ko kuma azumin watanni biyu
a jere idan bai samu baiwar ba.
Wannan ce maganar malamai masu yawa.
Waɗansu
sun zaɓi cewa babu
kaffara a kan wanda ya kashe kafiri da kuskure, saboda abin da ya zo a farkon
ayar cewa
وَمَنْ
قَتَلَ مُؤْمِنًا خَطَأً فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ
Kuma wanda ya kashe mumini a bisa kuskure sai ya ’yanta
baiwa mumina. (Surah An-Nisaa’i: 92).
Suka ce: Abin fahimta daga wannan shi ne: Babu kaffara idan
wanda aka kashe ba mumini ba ne.
Amma kuma hukuncin kaffara a cikin maganarsa
وَإِنْ
كَانَ مِنْ قَوْمٍ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُمْ مِيثَاقٌ فَدِيَةٌ مُسَلَّمَةٌ إِلَى أَهْلِهِ
وَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُؤْمِنَةٍ
Idan kuwa yana daga cikin mutane ne da kuke da alƙawari
a tsakaninku da su, to akwai diyya abin bayarwa ga iyalinsa, da kuma ’yanta baiwa mumina. (Surah
An-Nisaa’: 92).
Wannan magana ce Manɗuuqiya,
wacce kuma ake gabatarwa a kan Mafhuumiyar maganar ayar da suka janyo.
Kuma dayake wannan kafirin da aka kashe yana da alƙawari
mai ƙarfi
a tsakaninmu da shi kamar yadda ayar ta nuna, to ya shiga cikin Mantuuq na
ayar.
Haka kuma dayake shi ɗan
Adam ne da aka kashe shi a bisa zalunci, to ya zama kamar musulmi kenan, wanda
lallai a yi kaffara a kan kashe shi.
Daga cikin malaman da suka zaɓi
wannan maganar akwai At-Tabariy (9/43) da Al-Qurtubiy (5/325) da Ibn Katheer
(2/376) da Ibn Qudaamah a cikin Al-Mughnee (12/224).
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.