Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani Akan Sallar Matafiyi (Qasaru)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum.. Malam don Allah muna Neman cikakken bayani akan sallar kasaru, da yadda ake haɗa salloli biyu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam hakika An shar’anta wa matafiyi yin qasarun sallloli masu raka’a huɗu (Azzahar, La’asar, Isha) zuwa raka’a biyu, haka kuma zai iya haɗa sallar azzahar da la’asar, magariba da isha, saboda faɗin Allah Maɗaukakin Sarki :

وَإِذَا ضَرَبْتُمْ فِي الْأَرْضِ فَلَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَقْصُرُوا مِنَ الصَّلَاةِ إِنْ خِفْتُمْ أَن يَفْتِنَكُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا إِنَّ الْكَافِرِينَ كَانُوا لَكُمْ عَدُوًّا مُّبِينًا 

Idan kuka yi tafiya a bayan qasa to babu laifi a kanku ku rage (qasaru) sallah, in kuna jin tsoron kada waɗanda suka kafirta su fitine ku, haqiqa kafirai maqiyanku ne masu bayyana qiyayya”. (Suratun Nisa’i : 101).

Da abin da ya tabbata daga Anas dan Malik – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun fita tare da Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) daga Madinah zuwa Makkah, ya kasance yana mana sallah raka’a bibiyu, har muka dawo” [Nasa’i ne ya rawaito shi].

Abin Da Ake Nufi Da Tafiya Ita ce duk tafiyar da za a kirawo ta tafiya a al’adance, to wannan tafiya za a yi mata qasaru.

1 – Matafiyi zai fara qasaru da ya bar gidajen garinsu. Ba ya halatta ya yi qasaru a cikin gidan da yake zaune, saboda bai tabbata Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya yi qasaru ba har sai bayan ya fita (daga gari).

2 – Idan matafiyi ya isa wani gari, kuma ya yi niyyar zama kwana huɗu ko sama da haka, to wajibi ne a kansa ya cika sallah.

In kuwa ya yi niyyar qasa da kwana huɗu to ya hallata ya yi qasaru, idan kuwa bai niyyar wasu kwanaki qididdigaggu ba, kawai dai yana da wata buqata ce, duk lokacin da ya qare ta zai koma, to wannan ya halatta ya yi ta qasaru har sai ya dawo, koda kuwa lokacin ya wuce kwana huɗu.

3 – Wajibi matafiyi ya cika sallah idan ya yi sallah bayan liman mazaunin gida, koda kuwa raka’a ɗaya ya samu a tare da shi.

4 – Idan mazaunin gida ya yi sallah bayan matafiyin da yake qasaru, to wajibi ne a kansa ya cika sallah bayan liman ya yi sallama

YADDA AKE HAƊA SALLOLI BIYU

1 – Ya halatta matafiyi da mara lafiya su haɗa salloli biyu, azzahar da la’asar a lokacin ɗaya daga cikinsu, magariba da isha a lokacin ɗaya daga cikinsu. Idan ya haɗa sallar ne a lokacin ta farko, to wannan shi ne “Jam’u Taqdim”, in kuwa ya haɗa a lokacin sallah ta biyu, to wannan shi ne “Jam’u Ta’akhir”.

2 – Ya halatta ga wanda ya yi sallah a masallaci ya haɗa sallah saboda ruwan saman da zai sha wahala da qunci (wajen dawowa masallaci a cikinsa).

Amma wanda yake yin sallah a cikin gidansa, kamar mata, ba a yi musu rangwamen haɗa sallah ba .

3 – Ba dole ba ne qasaru da haɗa sallah biyu su haɗu a lokaci guda ba, za a iya haɗa wa ba tare da qasaru ba, za a kuma iya yin qasaru ba tare da haɗawa ba.

SALLAR MATAFIYI A CIKIN MOTA

1 – Idan sallar nafila ce ta inganta da uzuri ko ba uzuri, saboda abin da ya tabbata cewa “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya kasance yana yin sallar nafila a kan abin hawansa, duk inda abin hawan ya yi da shi” [Bukhari ne ya rawaito shi].

2 – Idan kuwa sallar farilla ce tana inganta idan ya kasance baya iya sauka kan qasa, ko kuma ba zai iya hawa ba idan ya sauka, ko kuma yana jin tsoron abokin gaba, da makamancin haka.

Sallar anan tana da kamanni da yawa, daga cikinsu akwai

1 – Ya zama zai iya fuskantar alqibla, kuma zai iya ruku’u da sujjada, kamar a ce yana cikin jirgin ruwa, to anan wajibi ne ya yi sallah yadda take, saboda zai iya yi.

2– Ya zama zai iya fuskantar alqibla, amma ba zai iya ruku’u da sujjada ba, to wajibi ne ya fuskanci alqiblar yayin kabbarar harama, sanna ya ci gaba da sallar duk inda motar ta yi da shi, yana mai nuni wajen ruku’unsa da sujjadarsa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments