Ticker

6/recent/ticker-posts

Saurayina Ya Yaudare Ni Muka Aikata Zina, Sai Na Yayyaga Takardun Karatunsa Na Makaranta Da Shaidar Filaye

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam saurayina ne yake matsa min akan in aikata zina dashi (har mun aikata sau da yawa) to sai mukayi faɗa naji labarin zai auri wata bayan kuma munyi alkawarin aure kafin na yarda mufara aikata zina da shi, to malam sai naje gidansa ba tare da saninsa ba, na ɗauke takardun karatunsa na makaranta dana shaidar filayensa na yayyagasu to malam inada laifi? Duba da irin cin zarafina da shima yayi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Kwarai kuwa, kin yi laifi babba a kan wannan lamari. Zina babban zunubi ne, kuma Shiga gidan saurayin naki ba tare da saninsa ko izininsa ba laifi ne na barna. Sa'an nan, yayyage takardunsa na makaranta da shaidar filaye barna ce da zalunci.

Abu na farko shine laifin zina, kin biye wa son rai, kin ruɗu da Qaryar da wannan saurayin yayi miki alhali a hakikar gaskiya mafiya yawan samarin dake fakewa da haka su aikata zina, daga karshe tserewa sukeyi. Sun san cewa ke sun gama lalata rayuwarki don haka ba zasu yarda su aureki ba.

Zina haramun ne kuma daya daga cikin manyan laifuffuka a Musulunci. Alkawarin aure ba ya halatta ku aikata zina kafin a ɗaura auren. Kuma koda saurayi ya biya sadakinki, duk da haka baki zama matarsa ba, har sai an ɗaura muku aure tukunna. Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Yace "BAYAN YIN SHIRKA DA ALLAH, BABU WANI LAIFIN DA YAFI GIRMA KAMAR MANIYYIN DA MUTUM YA JEFA ACIKIN MAHAIFAR DA BATA HALATTA GARESHI BA".

Duk macen da ta bada kanta wa wani dan iska mayaudari wanda baya sonta baya son rayuwarta da tarihinta da sunan wai yana sonki ko kuma kunyi alkawarin aure wallahi duk yaudara ce. Duk wanda zaki masa haka kina tunanin zai aminta cewa idan wani yazo gunki ba zaki bashi irin damar da kika bashi ba? Kiyi tunani da kyau yake ‘yar uwa! ba wani sonki da yake kawai wani abu ya keso ya cimma akanki na mummunan aiki ya ɓata ki dajin kunyar duniya da ta lahira. Ki sani da zarar ya cimma mugun burinsa akanki shine zaifi kowa kyamarki da gudunki.

kiji tsoron Allah ki fara tuba daga wannan laifin da kikayi, domin hakika baki san yaushe ne mutuwa zata riskeki ba. Kuma ki ɗauki niyyar har abada bazaki sake komawa cikin laifi irin wannan ba.

Shi kuwa laifin yaudararki da yayi, yana nan akansa. Domin hakika yaci amanarki, yaci amanar iyayenki tunda ya aikata fasadi dake.

Yayyaga takardunsa kuwa da kikayi, hakika kin cutar da rayuwarsa ta hanyar da zai daɗe bai dawo daidai ba. Ya zama wajibi a kanki ki nemi gafarar wannan saurayi dangane da takardunsa, ko kuma ki biya shi diyya (kuɗin) abin da kika lalata masa saboda wannan ramukon da kikayi ya zarce iyaka, ya zama zalunci kuma, Allah Maɗaukakin Sarki Yace:

وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُمْ بِهِ ۖ وَلَئِنْ صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِلصَّابِرِينَ

Kuma idan kun yi sakamako (ramuwa), to ku yi sakamako da misalin abin da aka cutar da ku da shi. Kuma lalle idan kuka yi haƙuri, haƙĩƙa shi ne mafi alhri ga mãsu haƙuri. (An-Nahl, Ayat: 126).

Allah (SWT) ya halasta wa wanda aka zalunta ko aka cutar ya yi ramako, amma sharadin shi ne ramakon kada ya wuce misalin abin da aka yi masa (wato kada a wuce gona da iri wajen ramawa). Duk da cewa an halasta ramawa, ayoyin sun kammala da cewa yin hakuri da yafiya shine mafi alheri ga wanda aka zalunta.

Kiji tsoron Allah ki nisanci irin waɗannan laifukan, ki yawaita istighfari da ayyukan alkhairi, da sannu zasu wanke miki laifin da kika aikata a baya. Shi kuma saurayin naki idan ba zai zama matsala ba, kije ki nemi yafewarsa bisa zaluncin da kikayi masa. Idan kuma babu damar haka, ki cigaba da yi masa addu'ar neman shiriya da yafewar zunubansa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments