Bikin Ranar Masoya (Valentine’s Day)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Ina da tambaya a kan bikin ranar masoya ta duniya a ake yi a 14 ga watan Fabrairu, menene matsayin musulunci akansa? Kuma ko ya halatta musulmi ya yi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Abu ne muhimmi ƙwarai da gaske musulmi ya fara sanin asalin yadda abu ya ke kafin ya karɓe shi ko ya amince ya yarda da shi, har ya shige shi. Kar ya yaudaru da irin abin da masu tallata shi suke faɗi a kansa. Domin ko masu magana da harshen Nasara suna cewa: ‘You don’t judge a book by its cover.’ A yanzu mutane sun ƙware sosai a kan algushu da yaudara da cuta a wurin harkokinsu na kasuwanci da sauransu.

    Fassara ‘Valentine’s Day’ da cewa: ‘Ranar Masoya’ a fahimtata ɗaya daga cikin yaudarar da nake magana a kai kenan. Domin a ciki hakan ba a koma ga asalin kalmar ba. Idan da an ambace shi da sunan Ranar Valentine da galibin Hausawa mazansu da matansu kuma manyansu da yaransu ba za su yaudaru ba, in shaa’al Laah. Tun da za su fara tambayar wanene kuma Valentine?! Me ya haɗa mu da shi?!

    To, ina kuma da an bayyana musu asalin sunansa cewa: Saint Valentine, wato Waliyyi Valentine?!! Ai ko waɗanda suka yi fice da girmama waliyyai a cikinmu ba za su amince ba. Domin za su ce, ba mu taɓa jin wannan sunan a cikin waliyyai masu karama ba a tsawon tarihi! Dole za su yi ɗari-ɗari da amincewa da bin hanyarsa!

    Saint Valentine waliyyi ne daga cikin waliyyan da mabiya cocin kiristanci suke girmamawa. Ya rayu a ƙarni na uku na tarihin kiristanci, a zamanin wani sarkin Romawa mai suna Emperor Claudues II wanda kuma ake kiransa: Claudues the Cruel saboda tsananin muguntansa da rashin tausayinsa. Ya kasance sarki ne mai yawan shiga yaƙe-yaƙe na cin ƙasashe a zamaninsa, don haka ya yawaita ɗaukan matasa da yawa a cikin aikin soja. A tunaninsa ya lura cewa matasa masu aure ba sa zama ƙwararrun sojojin da ake buƙata, saboda yadda zukatansu suke ɗamfare da matan aurensu da iyalinsu. Don haka sai ya kafa doka ta musamman mai haramta wa kowane matashi a ƙarƙashin daularsa yin aure!

    Amma shi Saint Valentine sai wai ya ƙi yin biyayya ga wannan dokar ta sarki. Ya cigaba da haɗa aure a ɓoye a tsakanin matasa maza da mata masu son juna. A ƙarshe dai sarki ya gano abin da yake aikatawa, don haka ya sa aka kamo shi, aka tuhumce shi da yi wa dokar sarki zagon-ƙasa. Kuma a kan hakan aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar duka da kulake har sai ya mutu, sannan a yanke kansa!

    A lokacin da yake tsare a gidan yari kafin a zartar masa da hukunci shi ne wai alaƙa ta ƙullu a tsakaninsa da yar mai tsaron gidan kurkukun. Shi ne wai lokacin da aka fitar da shi zuwa inda za a yanke masa hukunci sai ya bar mata rubutacciyar wasiƙa, a ciki ya rubuta cewa: Daga: Na ki Valentine. Wai wannan abin da ya auku da kashe shi da aka yi a ranar 14 ga watan Fabrairu 270 AD shi ne tushen bikin tunawa da abin da ya shahara daga baya da sunan: Valentines Day, wanda masu fassara suke kira: Ranar Masoya ta Duniya.

    Don haka masu yin wannan bikin na ranar masoya kowace shekara a wannan ranar ta 14 ga watan Fabrairu wannan faston kawai suke tunawa!

    Kodayake wannan labari bai nuna wata ɓarna ko rashin ɗa’a ba a tsakanin shi waliyyi Valentine da ’yar mai tsaron kurkuku, amma daga baya wannan rana ta zama rana ta aikata ma sha’a a tsakanin matasan al’ummomin da suke bin koyarwar kiristanci a duniya. An ce wannan ya ƙarfafa abin da su kansu sarakunan Romawa suka riƙa shiryawa na taron bikin haɗuwa da saduwar sojojin da aka hana su aure da ’yan matan gari. Wannan domin a ba su daman holewa da jin daɗi kawai, sannan ’ya’yan da aka samu ta wannan hanyar kuma sun zama na hukuma wacce za ta cigaba da renonsu a matsayin waɗansu matasan sojojin daular Rumawa!

    Wannan bikin ya cigaba da yaɗuwa a cikin al’ummomin duniya a wurare da yawa, har ya shigo ƙasar nan ta hanun mabiya addinin kirista. Na fara sanin wannan abin ne a lokacin ina aiki a wani kamfani (1994-2004). A ofis ɗin mu a lokacin akwai kiristoci biyar: Inyamurai biyu da Bayarben Kaba ɗaya da Jaba ɗaya da kuma inyamura mace ɗaya! Wani daga cikin inyamuran maza ne watarana ya yi shakkan abin da ya ji cewa ana samun ’yan mata a cikin mu musulmin Arewa waɗanda sai a bayan aure ne suke sanin namiji! Ya yi mamaki ƙwarai a kan hakan, har ma yake cewa, shin ku a cikinku ba a yin bikin Valentines Day ne?!

    Wannan ya nuna yadda bikin tunawa da Masoyi Valentine ya gurɓace hatta a cikin mabiya kiristancin.

    Wannnan gurɓataccen bikin ne ya shigo mana daga baya saboda yaɗuwar hanyoyin sadarwa na zamani wato, social media aka fassara shi da sunan Ranar Masoya. Kuma galibi a hakan mutane - musamman matasa maza da mata - suke ɗaukarsa. Wato ranar haɗuwa a tsakanin samari da ’yan mata da nuna soyayya ga juna mai kai wa ga aikata alfasha da sauran ayyukan maa shaa’a!

    A ƙarƙashin wannan bayanin muna iya taƙaice bayanai kamar haka

    A ƙaidar Addinin Musulunci bai halatta musulmi ya shigar da kansa cikin irin wannan irin bikin ba, domin ba a san hakan daga magabatan wannan alummar ta musulunci tsararriya ba.

    Koyi da malaman kiristoci haram ne a cikin abin da ya tabbata a cikin addininsu a keɓe. To ina kuma ga abin da ya shafi saɓo ko bidi’a a cikin addinin nasu?!

    Sannan yadda ake gudanar da bikin a yanzu a cikin matasan ƙasashen da suke yarda da wannan abin ya ci karo da koyarwar addinin musulunci wanda ya hana cakuɗa a tsakanin maza da mata. Ubangiji Ta’aala ya ce

    وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا

    Kuma kar ku kusanci zina. Lallai ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa’: 32).

    Allaah ya ƙara tsare mu, kuma ya tsare mana zuriya daga dukkan makirci da shirin maƙiya.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAmsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.