Jarrabawar Rayuwa

    TAMBAYA (62)

    Assalamualaikum mllm dftn antshi lfya tambaya na shine Allah ya jarrabci mijina da yana samu amma yanzu ya tsaya cak har abunda zamuci yanason ya gagara wani addua zan dinga karanta masa kada zuciyana ya karkata wajen bin hanya da bai daceba

    Kowani sallah ina masa addua har jki na ya yi sanyi nafila ma ina gagaran tashi mallam ataimakeni da addua

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum

    To yar uwa da farko dai ina tayaki alhinin halin da kuka tsinci kanku sannan kuma ina roqon Allah SWT ya ci gaba da baki qarfin gwiwar kasancewa tare dashi har lokacin da Allah zai kawo karshen jarabawar da kuke ciki

    Idan da ace za'a nuna miki yanda wasu iyalan suke rayuwa da anan zaki tabbatar da cewar ashe ku ba a cikin talauci kuke ba. Akwai yan uwanmu da suke rayuwa a garin Gaza dake kasar Palestine wadanda naga video din wata mata da dan ta suna tsintar ciyawa saboda tsananin yunwa da tsinannun yahudawa suka jefa su ta hanyar yi musu kisan kiyashi

    Zan so ki dinga bibiyar abin da ke faruwa ga wadannan yan uwa namu dake zirin Gaza (Palestine) anan zaki tabbatar da muna cikin ni'ima da kwanciyar hankali

    Talakawa zasu riga masu kudi shiga Aljannah da wuni guda (wato shekaru 500 na duniya - wannan hadisi ne sahihi), a lokacin da za'a ga talakawa na shiga Aljannah ba tare da an binciki dukiyarsu ba tunda basu tara ba - a sannan masu dukiya zasu ce ina ma bamu tara kudade dayawa da zasu zama silar tsaikonmu a wannan ranar ba. Allahu Akbar !

    Yake yar uwa, wannan sallar da kike kina addu'a to kada ki gaji, ki ci gaba da hakan, ki dage ki bawa shaidan kunya wajen qoqarin tashi da daddare kamar misalin karfe 3 haka (Saboda ya tabbata a cikin Hadisil Qudsi cewar idan kin raba dare gida 3 - kason karshe ne Allah SWT yake sakkowa (nuzul) zuwa sama'ud dunya, sakkowa wadda ta dace daShi, yana tambayar wanene zai roqi gafara ta, na yafe masa, wanene zai roqi arziqi na azurtashi), ki jefa qoqon bararki kiyi kuka, ki qasqantar da kanki, ki fadawa Allah SWT halin da kike ciki, in sha Allahu zakuga sauyin alkhairi

    Kuma a shawarce bawai ke kadai ya kamata ki dinga hakan ba, shi mai gidannaki ne ma yafi dacewa ya dinga hakan

    Sannan kuma da ke dashi ku yawaita karanta wadannan addu'o'i da Annabi SAW ya koyar kamar haka

    Annabi SAW yace: duk wanda ya karanta wannan addu'ar to Allah SWT zai kawo mafita a cikin lamuransa. Yace;

    لاَ إلَهَ إِلاَّ اللَّهُ الْعَظِيمُ الْحَلِيمْ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ رَبُّ العَرْشِ العَظِيمِ، لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهْ رَبُّ السَّمَوَّاتِ ورّبُّ الأَرْضِ ورَبُّ العَرْشِ الْكَرِيمُ.

    La ilaha illal-lahul-'azeemul-haleem, la ilaha illal-lahu rabbul-'arshil-'azeem, la ilaha illal-lahu  rabbus-samawati warabbul-ardi warabbul-'arshil-kareem.

    Ma'ana: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mai girma (wanda babu abin da yake girmama a gare shi), mai hakuri (mai jinkirin azaba tare da cikakken ikon aiwatar da ita). Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin Al'arshi, mai girma. Babu abin bautgawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai Ubangijin kasa, Ubangijin Al'arshi, mai yawan baiwa.

    Sannan kuma ku dinga karanta;

    اَللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُوفَلا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْن، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ.

    Allahumma rahmataka arjoo fala takilnee ila nafsee tarfata 'ayn, wa-aslih lee sha'nee kullah, la ilaha illa ant.

    Ya Allah! Rahamarka nake kauna, don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha'ainina dukkansa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.

    Haka kuma yazo a cikin sahihin hadisi cewar Annabi SAW yace duk wada ya karanta addu'ar da ma'abocin kifi (Addu'ar da Annabi Yunus Ibn Mat'a AS ya karanta a lokacin da yake a cikin kifi) to Allah SWT zai kawo masa dauki a lamuransa. Yace;

    لاَ إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ.

    La ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minaz-zalimeen.

    Ma'ana: Babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Tsarki ya tabbata gare ka, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.

    Sannan a yawaita karanta;

    اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.

    Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hazna idha shi'ta sahlan.

    Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki.

    Sai kuma ku lizamci

    اَللهُ اللهُ رَبِّ  لاَ أُشْرِكُ بِهِ شَيْئاً.

    Allahu Allahu rabbi la oshriku bihi shay'a.

    Allah ! Allah ne ubangijina, ba na yin tarayya da shi da wani abu a cikin bauta.

    (Duk wadannan addu'o'i suna cikin littafin Hisnul Muslim)

    A karshe ina son jan hankalinki akan kada ki bari shaidan ya rinjaye ki, ki ji kinason rabuwa da mijinki - domin kuwa dukkan kofofin azurtawa suna wajen ar-Razzaqu don haka ku roqe shi zai azurta ku ta hanyar da baku taba zato ba. Sannan kuma a shawarce ki dinga sadaka da kyauta ko min qanqantar ta, kada ki ga kamar ba ki da abinda zaki bayar, a'a - idan almajiri ya yi bara ki raba abincinki 3, ki ci 2 ki bada kaso 1 domin kuwa Allah SWT yana musanya alkhairi ga masu taimako kamar yanda ya fada a cikin Qur'ani mai girma;

    ( قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ ۚ وَمَا أَنفَقْتُم مِّن شَيْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُ ۖ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ )

    سبأ (39) Saba

    Ka ce: "Lalle, Ubangijĩna Yanã shimfida arziki ga wanda Ya so daga bãyinSa, kuma Yanã ƙuntatãwa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shĩ ne zai musanya shi, kuma Shĩ ne Mafi fĩcin mãsu azurtawa."

    ( اللَّهُ لَطِيفٌ بِعِبَادِهِ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْقَوِيُّ الْعَزِيزُ )

    الشورى (19) Ash-Shura

    Allah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi.

    A karshe ina roqon Allah SWT ya yaye muku damuwar ku, tare da sauran musulmai baki daya

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

     https://t.me/TambayaDaAmsa

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.