Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu

 

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR  da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu
"Kututturan da ba sanyi gasu sun yi toho,
Sun ɗau Salati sun ɗau Azumi da Kono da Zakka" 

Inji Makaɗa Abdun Inka Yarkofoji, Bakura a  faifansa na Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III mai amshi 'Ya tsare gaskiya Bajinin gidan Hassan, Jikan Bello Sarkin Musulmi'. Irin wannan aiki ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR ke ci gaba da gudanarwa a halin yanzu. 

A wannan hoton, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III CFR ne a gefen dama, a lokacin da Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu ke yi masa marhabin da sauka Masarautar Bauchi domin baiwa wasu Bayin Allah su fiye da 60 Kalmar Shahada a yankin Ganjuwa mai hedikwata a Kafin Madaki ta Jihar Bauchi a kwanan nan. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya ƙara wa Masu Martaba Sarakunanmu Lafiya da nisan kwana mai albarka, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin. Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara. 08149388452, Jumu'a, 29/12/2023. 4:42 Na Yamma.

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments