Ticker

6/recent/ticker-posts

Yin Jima'i Sau Huɗu A Wata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Wai Gaskiya Ne Yin Jima'i Sau Huɗu Da Mace A Wata Shine Sunnah ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Babu Wani adadi na iya Yawan jima'i da miji zaiyi da Matarsa, domin Abune daya sassaba Tsakanin Mutane da kuma ikon yinsa, Jima'i Haqqine akan mace, wajibi akan namiji, Ibnu rajab Al Hambali Allah ya jiqansa da rahama yace: ( Wajibine Miji ya Sadu da Matarsa indai ba wani uzurine dashi ba, haka Imam Maliku ma ya fada ) Al-Mugny ( 7/ 30 ).

Bukhari ya ruwaito Hadisi daka Abdullahi bin Amru binul Ããs Allah yaqara yarda dasu Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace: yakai Abdullahi bazaka bani labariba kana Tsaiwar dare kullum, kana Azumi kullum, Sai Abdullahi bin Abmru yace "eh" Ya Manzan Allah, sai Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace kada ka qara aikata haka, kayi Azumi yau gobe kasha ruwa, Kayi Sallar dare yau Gobe kayi bacci, domin jikinka yana da Haqqi akanka, idonka yanada haqqi akanka, Iyalinka tana da Haqqi akanka, ).

Ibnu Hajar Allah ya jikansa da rahama asharhin wannan hadisin yace: ( Bai dace ba miji yadunga dagewa wajan ibada dare da rana, Har hakan yasa ya kasa biyan buqatar Matarsa ta sha'awa da Buqatun rayuwa nayau da kullum ).

Ibnu Qudama yace: idan mutum yana da mata, ya zamar Masa dole wajibi ya dunga kwana da ita, duk bayan dare huɗu, Matuqar ba Wani uzurine dashi ba.

Al-mugny (7/ 28 ) da Kashful Qina'i ( 3/144 ).

Shaikul Islam ibnu Taimiyyah rahimahullahu yace: Wajibine Miji ya dunga saduwa da Matarsa Gwar-gwardon buqatarta Matuqar hakan bazai kassara Masa jiki ba, kuma bazai shagaltar dashi daka neman sauran Abubuwan buqatar rayuwa ba. idan sukayi jayayya da matarsa akan hakan, Alqali ya wajabtawa mijin, kamar ciyarwa.

Zababbun fatawoyin Shaikul islam Ibnu Taimiyyah Akan Mas'alolin Fiqhu shafi na ( 246 ).

Abunda Shari'a take nema shine miji yazama yana daukewa Matarsa buqatar sha'awarta ta jima'i don kaucewa fadawa Alfasha, ita macen ta dunga biyawa mijinta buqatarsa ta sha'awa, Bawai qayyade jima'i da wani adadi ba, na wata huɗu ko sati ko kwana huɗu ba, ko wata, Kawai iyakar itace gwargwadon buqatuwarsa, da kuma ikon mijin Akan cikawa da qosar da buqatar iyalinsa, Idan miji yana gari kuma yana rayuwa tare da Matarsa..

 Idan Miji zai iya saduwa da iyalinsa sau uku ko Sama da haka kullum da iyalinsa, kuma yanada ikon hakan, hakan bazai taɓa masa lafiyar jikiba, ko hanashi neman Abuncin dazasu rayuba, Hakan shine dai-dai kuma Shine Sunnah.

Babu wani iyakar adadin saduwar da miji zai da matarsa, kawai Abun yana da Alaqane da yanayinsu dakuma buqatuwarsu zuwa ga hakan, ko qarfin sha'awarsu.

Wanna idan Miji yana Ahalin zaman gida, Amma idan yayi Tafiya bayanan, saboda wani Uzuri na shari'a ko dalili na shari'a, Wannan ba'aso tafiyar Tasa ta yi tsawo. Kamar Tafiya zuwa jihadi don daukaka kalmar Allah, ko leqen Asirin dazai kare Musulmai da Musulunci, Anan yazama Wajibi adunga Tausasa musu ana basu hutu don dawowa zuwaga iyalinsu duk bayan wata huɗu, don ya dawo Tsakanin iyalinsu yabiya musu buqatunsu, Wannan shine Salon Mulkin Umar Bin khaddab Allah yaqara masa Yarda, Inya tura runduna sukayi wata uku ko 4 sai adawo dasu cikin iyalansu atura wasu.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments