Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Yayi Magana A Lokacin Da Liman Yake Huduba A Ranar Juma'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu Alaikum Malam. Ya Hukuncin Wanda Yayi Magana Ko Danna Waya A Lokacin Da Liman Ke Huduba Ranar Juma’a.??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Wanda yayi magana ranar juma'a ko wasa, ko danna waya, ahalin liman yana huduba, babu shakka yayi laifi wato yayi lagawu wato yashasshen zance na wargi.

Domin shi sauraren huduba ranar juma'a ibada ne yana cikin hukunce hukuncen da juma'a ta keɓanta dasu da sauran ranaku, kuma hadisi ingantacce ya razanar dangane da masu zance ko wasa da wani abu wanda zai dauke hankalinsu daka sauraren huduba lokacin da liman ke huduba, kuma basu da ladan juma'a kawai dai sunyi azahar ne.

Maganar nan kuwa koda ta nusar wace koda wani dan'uwanka ne yake wani abu da bai daceba kace yabari ko yayi shiru to kayi lagawu, kuma baka da ladan sallar juma'a.

Allah kayi salati da sallama abisa Annabi muhammad da alayensa da sahabbansa.

Wallahu a’alam

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments