𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam na kanji wasu mutane na
fadar cewa ba ya halatta idan matar mutum tana da juna biyu yayi jima'i da ita
har sai ta haihu meye gaskiyar maganar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
To ɗan'uwa
ya halatta a sadu da mace lokacin da take da ciki, saboda faɗin Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi : "Duk wanda ya yi imani da Allah da
ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu-dawud :
1847
Ibnul kayim yana cewa :
"Wannan hadisi yana nuna cewa ciki yana kara karfi duk lokacin da ake
saduwa, saboda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kamanta
shi da shuka, ita kuma shuka tana kara girma, idan aka ba ta ruwa"
Tahzibussunan 1\193 .
Masana likitanci suna cewa: Ba'a
so miji ya dinga hawa kan matarsa lokacin da take da ciki, zai fi kyau ta dinga
yin goho yayin da za su sadu, ko kuma ya sadu da ita ta gefe, saboda kwanciya
akanta yana iya wahalar da yaron .
Sannan yawanci mata basu cika son
yawan saduwa ba idan cikinsu ya girma, wasu likitocin suna bada shawara cewa a
karanta saduwa a waɗannan
lokutan.
Allah ne ma fi sani .
Jamilu Yusuf Zarewa
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.