Ticker

6/recent/ticker-posts

Uwa Mai Kashe Auren ’Yarta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Da yardar mahaifiyata aka ɗaura min aure da mijina uban ’ya’yana biyu. Amma yanzu tana ta hura wutar sai lallai in rabu da shi, domin in auri wani mai kuɗi da ita take so. Idan ta san na bi wani umurni na mijina sai ta yi fushi ta ce: ‘Ba ni ba ita!’ Ko ta ce: ‘In nemi wata uwar ba ita ba!’ Idan kuma na saɓa wa mijin sai shi kuma ya yi ta fushi, yana cewa: ‘Bai isa da ni ba kenan?!’ Don Allaah yaya zan yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Idan dai haka abin ya ke kamar yadda kika zayyana, to da farko lallai ki zauna ki natsu, ki mayar da al’amura ga Allaah.

Mutane da dama suna fama da irin waɗannan matsalolin da waɗanda ma suka fi wannan tsanani a cikin rayuwarsu. Ba ke kaɗai ba ce.

Cikakken dogaro ga Allaah da mayar da al’amura gare shi, da kyautata biyayya gare shi a cikin dokokinsa su ne mafita, in shaa’al Laah.

Idan dai mijin na ki musulmin kirki ne, mai biyayya ga dokokin shari’a gwargwadon hali, to bai halatta ki rabu da shi saboda damuwar mahaifanki ba.

Abu ne sananne a Musulunci cewa: Biyayya ga miji a kan mace shi ne a gaba da biyayyar iyaye (mahaifi ko mahaifiya), matuƙar dai ba ya yi umurni da saɓon Allaah ba ne.

Bai halatta ki yi wa mahaifiyarki biyayya a kan saɓa wa mijinki, ko kuma ki takura masa har sai ya sake ki ba, domin yin hakan

1. Zalunci ne ga mijinki, domin bai yi wani laifin da ya cancanci hakan ba a shari’a.

2. Zalunci ne gare ki, domin an raba ki da gidan auren da shi ne alherinki a duniya da lahira.

3. Zalunci ne ga ’ya’yanku, domin an hana su samun tarbiyyar iyayensu biyu kamar sauran ’ya’ya.

4. Zalunci ne a kan mahaifiyarki, domin ta saɓa wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan hakan.

5. Zalunci ne a kan sabon mai neman, in ya sani. Domin in ba azzalumi ba babu wanda zai goyi bayan a lalata auren wata mace a raba ta da gidan mijinta na-kirki, domin shi ya aure ta!  Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

لَيْسَ مِنَّا مَنْ خَبَّبَ امْرَأَةً عَلَى زَوْجِهَا أَوْ عَبْدًا عَلَى سَيِّدِهِ »

Wanda ya lalata ɗabi’ar mace a kan mijinta ko bawa a kan maigidansa baya tare da mu. (Sahih Abi-Daawud: 2175).

Don haka dai, lallai wannan mahaifiya da sauran masu zalunci irin wannan su gaggauta tuba daga irin wannan mummunar ɗabi’a, tun kafin lokaci ya ƙure musu. Allaah Ta’aala ya ce

وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنْقَلَبٍ يَنْقَلِبُون

Nan gaba kaɗan, waɗanda suka yi zalunci za su san wace makoma ce za su koma mata. (Surah As-Shu’araa’: 227).

Sannan kuma ta yaya ma ita wannan mahaifiyar ta iya tabbatar da cewa zaman gidan wannan mai kuɗin zai yi ma ’yarta da ita kanta kyau, kuma ya yi daɗi?

Idan lokacin shigan ’yar cikin gidan mai kuɗin ya dace da abin da Allaah ya ƙaddara masa na karayar tattalin arziƙinsa fa, yaya kenan?

Wai har yanzu mutane ba su rabu da wannan mashirmancin tunanin ba cewa, kuɗi ne kaɗai hanyar samun jin daɗin zaman aure?

Matan mawadata nawa ne a yau suke fama da hawan jini da ciwon zuciya? Kuma na matalauta nawa ne suke cikin kwanciyar hankali da natsuwar zuciya?

Kuma ko ita wannan mahaifiyar ta leƙa cikin littafin rubutun ƙaddara ne, har ta gano cewa mijin ’yarta na yanzu ko wani daga cikin ’ya’yan da ’yar tata ta haifa tare da shi ba zai taɓa yin kuɗi ba a rayuwa?!

Sannan wai mutane masu dakusasshen tunani irin wannan ba su taɓa jin karatun irin waɗannan ayoyin na Alqur’ani ba ne

فَأَمَّا الْإِنْسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ ٥١۝ وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ ٦١۝

Amma dai shi mutum idan Ubangijinsa ya jarraba shi, wato ya karrama shi ya ni’imta shi sai ya riƙa cewa: ‘Ubangijina ya karrama ni.’ Amma kuma idan ya jarraba shi, wato ya ƙuntata masa a cikin arziƙinsa, sai ya riƙa cewa: ‘Ubangijina ya wulaƙanta ni!’ (Surah Al-Fajr: 15-16).

Daga nan muke gane cewa: Samun wadata jarrabawa ne, kamar yadda rashi da ƙuncin wadatar ma duk jarrabawa ne daga Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala. Kuma duk wanda bai san hakan ba, to lallai yana da sauran aiki a cikin ilimi da fahimtar imani da taqawarsa a cikin sahihin addinin musulunci.

Allaah ya ganar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments