Za Mu Iya Taya Krista Murnar Bikin Haihuwar Annabi Isa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Malam muna da makota Krista, ko za mu iya taya su murnar zagayowar Kirsimeti?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam, Bai halatta ba, saboda suna yin hakan ne don girmama ɗan Allah, mu kuwa Musulmai Annabi Isa bawan Allah ne da kuma Rai cikin rayukan da Allah ya halitta a wajanmu, kamar yadda Allah ya Yi bayani a cikin suratun Nisa'i da Ma'idah.

    Allah Madaukaki Bai haifa ba, ba a Kuma haife Shi ba, Shi kadai yake ba Shi da abokin tarayya.

    Taya su murna yana nuna yarda da abin da suke riyawa, Kudurce cewa Annabi Isa ɗan Allah ne kafirci ne Kuma ya saɓawa abin da suratul Iklasi ta kunsa.

    Su kan su kristoci sun Yi saɓani mai yawa game da ranar da aka haifi Annabi Isa, wannan yake nuna rashin tabbacin haihuwarsa ranar 25/12.

    Allah ne Mafi sani

    DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.