Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Alhaji Amadu Na Funtua (Sain Katsina) da Alhaji Dr. Mamman Shata Katsina.

A ranar Litanin 25/12/2023 ce Alhaji Amadu Na Funtua (Sain Katsina) ya cika shekara Hamsin chif da nadinshi wanda Marigayi Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo Mai Turawa yayi mashi.

Makada, Maroka, Mawaka babu shakka sun sheda wannan nadin amma Tabbas babu Kamar Na Ali Hukumar Waka.

Tsakanin Baba Sa'i da Dillalin Duniya Kanen Sasana Allah kadai ya san tsammaninsu domin tarensu ta amana ce tun tali-tali.

A wata hira da nayi da Baba Sa'i a cikin shekarar 2019 ya sheda mani cewa lamarinsu Allah ne kawai ba wani mahaluki. Domin a zaman da yayi a Sierra Leon, Shata ya so ya je har Chan Amma Allah ne bai yi ba. Shatan ya ambaci wani baiti makamancin haka a Wakarshi ta Yawon Duniya Mafarki ne Alhaji Shata.

Baba Sa'in ya sheda mani yana daga cikin mutane Ukku da ke sa Shata yayi abu ko da ba ya son yayi shi. Sauran biyun sun hada da Ummaru Yaro Funtua da Yusuf Musa Yar'adua (Dan London Na Mairo)

Tsanin da tsabagin jituwa, yadda da Amana da ke tsakaninsu Shata ya na da daki a Nasara Club wanda ko da ya rasu sai da aka zo aka kwashe kayanshi a wannan daki. Sannan Nasara Club na daya daga cikin manyan wuraren da Shata ke wasa a Katsina Idan ya zo.

Duna na Bilkin Sambo ya yi ma Baba Sa'i wakokin da suka hada da:

Sasau Na Korau Dan Abdu,

Amadu Sain Katsinarmu,

Na Funtua Amadu Na Abba.

Ya kuma ambace shi a wakoki da dama, ga kadan daga cikinsu:

Allah raya Jihar Katsina

Zakari Magajin Zakari (Yau Magajin Yau)

Salele Alhaji Dakwari

Hajji Armayau na Yar Salau (Saliyo)

Jamiyyar SDP.

Mai karatu a daidai nan akwai wakoki da dama, ka zamo cikin masu karo wasu domin lissafinmu ya daidaita.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen sa Shata yayi ma mutane da dama wakoki wasu a gidanshi, wasu a hilin Kofar Gidan Marigayi Alhaji Sani Mai Sanda, wasu a Nasara Club wasu a gidan wasan Marigayi Shema DanDoka.

Duk da kyakkyawar alaka da ke tsakaninsu bai hana Dodo ya nuna ma Baba Sa'i shi Na Yelwa Mai Ban Shaawa ne kuma mai ban haushi ne. Wata rana an sanarwar wasan Shata aka  taru a Nasara Club Dodon sai ya gudu ya tafi garin Muduru ya boye ma Baba Sa'i da sauran masu son ganin wasan shi amma duk da haka sai da ya je ya taho da shi.

Tarihin Shata ba ya cika ba Baba Sa'i haka zalika na Baba Sa'i ba ya cika ba Shata.

Da wannan Dan takaitaccen bayani muke kara yi ma Baba Sa'i fatan Alkhairi a daidai lokacin da ya cika shekaru 50 da wannan sarautar.

Allah ya kara lafiya da nisan Kwana Baba.

www.amsoshi.com

Kabir Umar Saulawa (PRO)

07034610481

24/12/2023

Post a Comment

0 Comments