Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane ne Zartu?

"Arna sun sani akwai Zartu Yanshawara,

Amadu Kakanka na mazaizan gaba an nan"

Inji Makaɗa Alhaji (Dr.) Ibrahim Buhari Abdulƙadir Mai Dangwale Narambaɗa Tubali a faifansa na Marigayi Mai Girma Uban Ƙasar Isa/Hakimin Gundumar Isa, Jihar Sakkwato, Malam Ahmadu Basharu /Sarkin Gobir Na Isa Amadu I /Ahmadu Bawa (ya yi Sarauta daga shekarar 1935 zuwa shekarar 1975) mai amshi 'Gwarzon Shamaki na Malan Toron Giwa, Baban Dodo ba a tamma da batun banza' /Bakandamiya.

Wa ne ne Zartu? Me ne ne Yanshawara? Ya kuma dangantakar Zartu take da wanda aka yi wa Waƙar? Zartu /Zarto dai laƙabi ne da ke da nasaba da wani abu da ake yi da Ƙarfe dake da kaifin  yanke /yanka Katako ko Kwangi ko Ƙyame da makamantan su dake da wani garje-garje a bakin sa. Saboda irin jaruntarsa a fagen yaƙi, Malam Abubakar ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio wanda daga baya ya yi Sarautar Raɓah ya kuma zamo Sarkin Musulmi daga shekarar 1873 zuwa shekarar 1877 har ma ana kiran sa da Sarkin Musulmi Abubakar II ko Sarkin Musulmi Abubakar Mai Raɓah ya samu laƙabin Zartu/Zarto. Wannan Bawan Allah shi ne Kakan Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE Sardaunan Sakkwato, Firimiyan Jihar Arewa domin shi ne Mahaifin Sarkin Raɓah Ibrahimu wanda shi ne ya haifi Sardaunan.

Ina ne Yanshawara, kuma me ne ne alaƙar Sarkin Raɓah /Sarkin Musulmi Abubakar II /Mai Raɓah da Yanshawara da ma alaƙar sa da wanda aka yi wa wannan Waƙar? Yanshawara gari ne na Ribaɗi da Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ya ƙirƙira a kan iyakar Arewa maso gabas ta Cibiyar Daular Usmaniya ta Sakkwato da Tsohuwar Daular Gobir. A lokacin mulkin Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami Ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio (1842-1859) ya sake farfad'o da wannan gari ya ɗauki wannan Ƙane nasa, Abubakar Zartu ya kai shi garin a matsayin Sarki gabanin ya taho  Raɓah a matsayin Sarki inda daga nan ne a shekarar 1873 ya zamo Sarkin Musulmi, wato Sarkin Musulmi Abubakar II/Abubakar Mai Raɓah. A halin yanzu babu wancan gari na Yanshawara duk da yake akwai Unguwa/Shiya/ƙauye da ake kira Yanshawara kusa da garin Raɓah na yanzu, ƙila an ƙirƙire shi da zummar taskace Tarihin wancan garin Yanshawara na asali, Allahu Wa'alam!

Alaƙar mai wannan Waƙar, Sarkin Gobir Na Isa Amadu I da Zartu /Zarto Yanshawara, Sarkin Musulmi Abubakar II /Mai Raɓah ita ce : Sarkin Gobir Na Isa Amadu I /Ahmadu Bawa Ɗan Sarkin Gobir Na Isa Basharu ne, Sarkin Gobir Na Isa Basharu ɗan Sarkin Gobir Na Isa Ummaru ne, Sarkin Gobir Na Isa Ummaru ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami (wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1842-1859), Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne, shi kuma Zartu /Zarto Yanshawara wato Sarkin Raɓah /Sarkin Musulmi Abubakar II /Mai Raɓah ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio ne, kenan Ƙane yake ga Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami, Mahaifin su ɗaya, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio, da wannan dangantaka ta ƙud da ƙud a tsakanin waɗan nan mutane guda biyu, Sarkin Musulmi Aliyu Ƙarami (1842-1859)da Sarkin Musulmi Abubakar II/Mai Raɓah (1873-1877) dukan su biyun sun zamo Kakanni ga Sarkin Gobir Na Isa Amadu I /Ahmadu Bawa ɗan Basharu ɗan Ummaru ɗan Aliyu ɗan Bello ɗan Shehu Ɗanfodio. Saboda haka Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya taskace wannan Tarihi na dangantaka da tabbatar da samuwar garin Yanshawara a cikin Tarihin Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

www.amsoshi.com
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments