"Kore na Magaji
Mazaizan yan maza
Kai yaro gudu Gora ya taho
Ko baka gudu sai ya yima?
Muna tahiya yaƙi jama'a amma hwa a tsaya ga hwaɗan gargajiya
In an koma ga hwaɗan gargajiya
Ina zuwa yaƙi amma sai an koma ga hwaɗan galgajiya
Yaƙi da Takobi ko Kibau
Koko a sa masoshi ana ruwan Gorori, to kun ji hwaɗan gargajiya
Don wani baya tarara man wuta
Ni wani baya turara man wuta.. Nak'i
A dai koma ga hwaɗan gargajiya Yan Tauri
Daji na Magaji mazaizan yan maza
Ku aje makammanku Turawa
Ku amshe makammai Turawa
Ku dai amshe makammai Turawa
A tsaya ga hwaɗan gargajiya
Da dum mai yaji ga hwadan sai kun gani
Ɗankura mazaizan yan maza
Amma baka ji ba baka gani ba
Ba kaga abukkan hwaɗa ba, sai a tarara ma wuta
Wanga hwaɗa yau ɗau wuri
Daji na Magaji daagi nauyin ƙasa
Yaro gudu Gora ya taho".
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
Post your comment or ask a question.