"Baƙin Mai Sallah Ɗan
Barmo
Baƙin Alhaji Daɗi Na Amadu baƙin Wakkala
Kokirzon Kada
Yan Tauri kuyi tambaya
Hwarauta an yarda muna ita, bana yada gudunmai za'ayi
Haka kaji ina Waƙad Daɗi
Jabandawa sun zaka
In kau sun zaka ɓanna za'ayi
Na Magaji Baraden yin hwaɗa
Na Amadu Kokirzon Kada
Daɗi baƙin Mai Sallah Ɗan Barmo
Too
Wanga Kiɗi ab basu so
Dole ina Waƙad Daɗi
Ni dai tun da yana kyauta
mani
Ehhhn!
Wasu Yan Tauri Yan Karma ne
Wasu kau gama lalatak kane
Su ba'a da kyauta ba hwaɗa
Bakin mi suke?
Sabad da ina Waƙad Daɗi
Wasu Yan Tauri na gune mani
Hah Anchana na hwaɗa mani
Na hwaɗa mani
Hah yak kama Kalangai
yar riƙe, yacce min ba zuwa
Nicce Dodo barmashi
Kalangai so shi kai?
Shi banni da baki in hwaɗi, tun da mutun nike ba kusu ba ne
In don ƙarhi nayi shi
Don dai bani da ƙwazon tambaya
Da Anchana bai tarbe ni ba
Tsawhhin kanun nika tambaya?
Aa' Katakare in ka aje
In ka raga tuk'e emmani
Gandau in baka yi
In ka raga kambu emmani
Kaga hwa Anchana na hwaɗa mani
Baraun Gyare ka jiya
In ka raga tuk'e ci nikai
Ina Na Mande Garu-garu
Ku ni tambaya kowar raga gari in ji ya
Ko ishe Gurjago nikai?
In ya raga tuk'e in ji ya
Ko hwadama ni kai
In ishe Isan Ɗan Madi?
Su nijji suna ƙago
Isah kai kau emman ƙi-bugu
In ka raga kambu emmani
Kaga hwa Anchana na hwaɗa mani
In don ƙarhi na yi shi
Don dai bani da ƙwazon tambaya
Ko ishe Basare nikai?
Na Shanawa in ka aje
In ka raga tuk'e emmani
Ina Na Naye shegen wando na Tukud'awa?
Manyan dai nika tambaya
Kowar raga gari so nikai
Ina Guguru Ɗan Mande
Aa' ku ni tambaya
Kowar raga gari so nikai
Ina S/Karma Baƙo Mai kacimo na Ango baka riƙon baya na Isa?
Aa' ku ni tambaya
Kowar raga gari in ji ya
Ina Barmo Na Tubali
Na Gidan Bawa Akurkin Ɗund'u?
Manyan ku ni tambaya
Kowar raga gari so nikai
Kun ga Anchana na hwaɗa mani
Ina S/Karma Sharu Ɗankunce Galadi?
Aa' Manyan ku ni tambaya
Kowar raga gari so nikai
Kun ga Anchana na hwaɗa mani
In kau kun ka hana mani
In zaka in ɗau dangana
Ku ma ya ƙare maku
Yau dai ba Tauri sai bagura
Duh haukanka da wayo ne kukai
Gurud'au ne akai
In don kuri na iya
Haaa!
Taro bagura ba yaji bace
Bari in bid'i walki in hwasa
In samu ɗamarru in guma
In samu Takobi in laga
In don kau suma in bari
In ya saran ya cire nikau in sarai in cire
In da ba a huda shi ba nig gani
Kyawon hwaɗa a zwage Takobi ayi sharo
Asa gorori kaji rimis
Wani kau iya sa gitta yakai
Wani had da Wuk'ag gutcu shi kai
Ka iske yana washe da wannan baka da mai jimre mata
Amma bindiga ba yaji ba ce
Ba yaji ba ce
Gurud'au ne akai
Ɗan Bindiga halbo in buga
Daɗi baƙin Mai Sallah Ɗan Barmo".
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.