Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Marigayi Mai Girma Dagacin Banga, Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar

Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Dagacin Banga,  Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1934 zuwa wafatinsa a shekarar 1963), Ta Makaɗa Sa'idu Faru mai taken "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshik'an Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi. 

Jagora :

Zama Giwa ta fito kiyo tai miƙa ta zo ta sha ruwa,


Y/Amshi :

Kuji Ɗan Zomo na hwaɗin hwaɗama su Tsari, Tsara mu tai gida

Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,


Jagora/Y/Amshi :

Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki, 


Jagora :

Gurnanin Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora ɗemuwa, 


Y/Amshi :

Ga wani ya yi Kokuwa da wan ƙarfi nai, 

Ya hwaɗi ya kare,

Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lank'wanshe tsara, 


Jagora /Y/Amshi :

Tun dai ba a tantance ba shi na nishi ya lank'wanshe tsara, 


Jagora :

Ko jiya na iske Gamdayak'i da Tuji sun iske Jinjimi,

To sun ko murd'a gardama, 

Sun iske su Bubuk'uwa ruwa, 


Y/Amshi :

Dan naan niko ina gaton gab'a, 

Sai nik kwaɗa gaisuwa, 

Su ko sun dak'ile ni dud, 

Niko nik' ƙara gaisuwa, 

Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya amsa gaisuwa, 


Jagora :

Dan nan sai Jinjimi da yad darzaza ya suntule shi dud, 


Y/Amshi :

Shi ko Tuji da ad da girman baki yak kwashe Jinjimi, 

Dan nan Bubuk'uwa da tar rura tag gangame su dut, 


Jagora /Y/Amshi :

Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani, 

Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani, 


Y/Amshi :

Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, 

Gamshik'an Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi, 

Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, 

Gamshik'an Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi, 

www.amsoshi.com
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments