Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Dan Tauri Ibrahim Shayi/Ƙudunguru Shayi Dan Gidan Labbo Ta Makada Abubakar Amadu (Kassu Zurmi)

Ku bak kora ta,
Mai kwana ya tashi,
Mai tahiya ya dakata shi kau,
Ku tashi kun ji Kiɗin Shayi ɗan gidan Labbo Na Abu ɗan baƙin daji,
Ku hwalka na kai ga masu ɗan gashi,
Lalle Shayaya adda ɗan gashi,
Ya yi biɗaa amre bara sai da yas samu,
Iro ya kai ta gidan maigidansu yah hwaɗi,
Yam mutu yab bassu ba abin amren kana ba hatcin ɗiba,
Don an game da Labbo yana tattalin ɗiyan dangi,
Dodo ga amre Shayaya Labbo ya wahala,
Ga amren Shayi Labbo yay yawo,
Labbo ya yi jidali garin biɗab bashi,
Ya sha  Raɓa kamak Karen daji,
Ya sha Rana kamat tukuin ɗaki,
Labbo ya takwaikwaye walki ya na ginah hanya,
Maidabo Ɗan Auta za ya basu yah hwasa,
Ahaaa!
Sun yi gidan Bawa Ɗangaladima,
Sai da Bawa yab basu sai Ta Ɗari ta ƙwace,
Tacce sabilin Shayaya ba a bashe su,
Ɗan nema bai raga ma kowa ba,
Wata yar gona garai cikin tabki,
Bara yat tashi ya na kashin Awakinmu,
Tacce masalin mai ƙato gudum awash Shayi an nan ka biɗab bashi?
Labbo yacce ƙaton gidan na banza ne,
Komi yab biɗa na mata ne,
Dum mata sun bi Iro sun kod'e,
Yar ƙaunatai tana yi mai wazu,
La'ananne baya jin batun ƙaunat,
Tana hwaɗin Shayi gaka dai da ƙarhin ka Na Abu hak ka lalace Tsohuwa ka cishe ka,
Ta Ɗangiwa Hauwa na yi mai ɗiba,
Bata da ƙarhi bata ɗiyak kuyya,
Yar Tahwasa taka ɗiba a bata sadare ta kau ci hat ta cishe shi,
Taro kun san kau hah uwaa ubanai ce,
Yihuuuuu!
Katakoron Lando Iro Na Ummaru Kura mai guzurin kunya,
Shayaya Magarya ta yi ma doro,
Ta Ladan ta bakka bata ta tcere,
An barmaka Tsohuwa ta cishe ka Tsohuwag ga ta tuzga,
To daɗa Shayaya wa ka cishe ka?
Kakab bana tai kyawo ko ta bara mun gode,
Sai dai Shayaya bai yi komi ba,
Naga yan Tantabaru cikin Rihewassu,
Tantabara goma,
Amma yanzu basu sun ƙare,
Saura nai guda baƙi namuji,
Ko shi kau don yana yi mai Waƙa inda swahiya taw waye ya ɗora mabanci,
Tantabari na rigan ka tasowa,
Kai gaka da ranak kwana sai luhwa ta shuid'a,
Sai Tsuntsu ya hito yana shan hantci yana kashin ƙeya,
Shi na dibin inda zaka hudowa,
Shi kau yana cikin ɗaki,
Tantabari na gyaran jiki nai,
Ayyyihuuuuu!
Sai in Shayaya yaɗ ɗago ɗaki ɗan mazan Tantabarin ga na yi mai gud'a,
Shi na ƙudunguru Shayi ɗan gidan Labbo,
Ƙudunguru Shayi ɗan gidan Labbo,
Ƙudunguru Shayi ɗan gidan Labbo,
Ƙudunguru Shayi ɗan gidan Labbo,
Shi kau kokirzon sai ya watsa yar tsaba,
Kai kau Tsuntsu tcince tciyakku ta biku,
Ɗan Annan dubu kamash Shayi,
Babu kayan Turwa guda Rihewassu,
Wasad da mun kazo tare da yan Magarya tai kyawo,
Ran nan Shayaya yash shigo sa'a,
Aha!
Ga ya da dogon baki da yar wutab' ɓota,
Na Abu yankan bakin ka ya yi ma kyawo,
Ya samu gamon aron zanen swak'i,
Had da tsamiya yaɗ ɗamro da yar baƙash shadda,
Iiiiwwuuu!
Yan mata sun gane shi tun gebe an ka ɗora wasoso,
Ni wan in Shayi nika jish she shi,
A'a kina ƙarya na riga ki zaɓo shi,
Yiiiiiyiiiii!
Kamas su buga gasu nan cikin gebe,
Nicce masu ka ku buga ya ishe ku jid'awwa,
Ɗaukash Shayaya mun kasha daula,
Mun sha yan Na Lutsa mun sha mai,
Mun sha Zabbi ga ɗan gidan Labbo,
Nicce ma yan yara na ku sha ahaha ce tun da baya mai she su,
Katakoron Lando Iro Na Ummaru Kura mai guzurin kunya,
Sai da zamu watcikkewa kana Uwayen matan ga sun ka jawo ni,
Gani ga yan matan ga ga Uwayensu mu kaɗai cikin Zaure,
Kassu amanar Allah ka bamu labari,
Nicce wane labari?
Labarin Shayi ɗan gidan Labbo,
Yan mata sun walwale baikonsu,
Sun ce Shayaya za shi rankon su,
Shi muka son ka bamu labari in akwai gidan kirki,
Nicce yau kau dattib'e kun ɗamarshe ni,
Yahi ku koma ku sake ɗan shaida Na Abu ɗan uwana ne,
Mutun kau bai shaidad' ɗan uwansu ko hwada,
Kassu amanar Allah ka bamu labari,
Ni kau amanar Allah ka ɗai ka sha min kai,
In nabi amanar Allah ga nayi ɓatanci,
Kuma in tuna bani cin amanar Allah sabad da tantiri,
Amma hwa ku bashi in kuna bashi Na Abu Shayi dai ɗa ne,
Sun kace ba haka mun ka so ba ɗan yaro,
Ai mun san ɗa ne tun da an ka haihe shi,
Bamu labari in akwai gidan kirki,
Nicce i gaskiyak ka dattijo,
Mutun kau ba za ya kai ɗiyatai ba gidan da ba abin kirki,
Amma hwa ku bashi in kuna bashi,
Sai ɗiyad dattib'ai kad'ai ka amre Shayaya ɗan gidan Labbo,
Tun da ko waa amre shi ita ka cishe shi,
Ta biya kuɗɗin garin Karen Kyarson,
Sannan tayi mai abin ruhwa koren.
www.amsoshi.com
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments