Ticker

6/recent/ticker-posts

Uwa ta ce wa ɗanta: ‘za ka gani!’

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ni ce na dawo daga unguwa sai na yi ta yi wa yarona ƙarami wasa amma sai ya yi banza da ni, bai kula ni ba. Sai ni kuma na ce: Ai ko? To, za ka gani! Ina nufin ni ma zan rama idan nan gaba ya zo yi min wasa. Shi ne babansa ya hau ni da faɗa. Menene matsayin wannan maganar da na faɗa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Kalmar ‘Za ka gani!’ a nan kalma ce mai harshen-damo: Tana ɗaukar fassarori fiye da ɗaya.

Tana iya ɗaukar mummunar ma’ana ta mugun addu’a ko yin baki ga yaron, kamar idan mahaifiyar ta fusata a kan abin da yaron ya yi mata. Sanannen abu ne kuwa a addini da rayuwa cewa: Addu’ar iyaye tana tasiri a kan ’ya’yansu.

Wataƙila wannan fassarar ce mijinki ya hararo a lokacin da ya ji kalmar ta fito daga gare ki.

Amma kuma kalmar tana iya zama mai kyakkyawar ma’ana wacce babu tsoron komai a ƙarƙashinta, kamar yadda kika yi nufi kuma kika yi bayani.

A irin wannan halin kodayake mijinki shi ne shugaban gida, kuma daidai ne ya yi ƙoƙarin gyara duk wani abin da ya ga zai cutar da zamantakewar gidan a kusa ko a nesa - musamman ma a kan abin da ya shafi magajin gidan watau ɗansa, amma kuma dole ya san cewa ke ma fa uwa ce kuma mahaifiya ga yaron, wacce kuma ba za ki yi nufin cutar da shi haka nan siddan ba.

Ke ma kuma kodayake ke ce uwar wannan yaron wacce ba za ki so aukuwar duk wani abin da zai cutar da shi ba, amma kuma dole ne ki fahimci matsayin mijinki, wanda alhakin gyara duk wata karkata ko ɓatar da ya gani a cikin iyalinsa - har da ke matarsa - ya rataya a wuyarsa a duniya da barzahu da lahira.

Hadisin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito ya tabbatar da cewa

إِنَ اللهَ تَعَالَى سَائِلٌ كُلَ رَاعٍ عَمَا اسْتَرْعَاهُ : أَحَفَظَ ذَلِكَ أَمْ ضَيَعَهُ ؟ حَتَى يَسْأَلَ الرَجُلَ عَنْ أَهْلِ بَيْتِهِ

Lallai Allaah Ta’aala mai tambayar duk wani makiyayi ne a kan abin da ya ba shi kiwo: Shin ya kiyaye hakan ko ya tozarta shi? Har sai ya tambayi mutum a kan iyalin gidansa. (Sahih Al-Jaami’: 1774)

A taƙaice dai: Ƙoƙarin fahimtar juna da bai wa kowane mai matsayi matsayinsa ba tare da rage komai ba, shi ne maganin irin waɗannan matsalolin a tsakanin ma’aurata, in shà Allâh.

Don haka, iyaye su zama masu haƙuri da juriyan bin abubuwa sannu kan hankali, tare da ƙoƙarin kyautata zato da fahimtar juna a tsakaninsu, musamman ma dayake ga yayansu a gabansu waɗanda suke son yi wa kyakkyawar tabiyya. Su riƙa neman bayani da ƙoƙarin tattaunawa da fahimtar junansu a kan alamura, kuma su riƙa yi wa maganganu da ayyukan junansu kyakkyawar fassara kafin su kai ga yanke hukunci, ko kafin ma su sanar da waɗansu a waje.

Allaah ya datar da mu gaba-ɗaya ga abubuwan da yake so kuma yake yarda da su na zantuka da ayyuka da ƙudurori.

WALLAHU A'ALAM.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments