𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum. Mace ce ta yi sallar Azahar da La’asar da tufafin da jinin haila ya
shafa, ba ta sani ba sai da ta zo wanki. To ko za ta rama sallolin ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Ramatul Laah
Jinin haila
dai najasa ne a haɗuwar
dukkan malamai. Don haka, in ya shafi tufafi ba za a yi sallah da shi ba sai
bayan an wanke shi. Yadda za a yi wankin kuwa shi ne
• A
fara da kankare shi ko murtsuke shi domin a gusar da sandararren jikinsa da ya bushe
a kan tufar.
• Daga
nan sai a sa ruwa mai tsarkakewa a wanke daidai wurin da ya shafa sosai.
• A ƙarshe
ana iya yin amfani da magarya ko wani sabulu domin ƙara tsabtacewa.
• Sai
kuma a ɗebo ruwa a
yayyafa wa sauran tufar har sai ta jiƙu gaba ɗayanta.
• Daga
nan ana iya yin sallah a cikinta. (Silsilah Saheehah: 299).
Amma matar da
ta yi sallah a cikin tufan da yake dauke da wannan najasar, to ba za ta fita
daga dayan biyu ba: Ko dai ya zama ta yi hakan da gangar ne ko kuma da mantuwa.
• Idan
da gangar ne, ita ma ko dai ya zama tana da ikon gusar da najasar kamar yadda
aka ambata a sama, ko kuma ya zama ba za ta iya ba.
• Idan
za ta iya gusar da najasar amma kuma ta ki yi har ta yi sallar da haka, to
sallarta ba ta yi ba. Dole sai ta sake ramawa a bayan tuba da neman gafarar
Allaah Ta’aala a kan hakan.
• Idan
kuwa ba ta samu ikon gusar da najasar ba, ko ba ta samu wani tufan da za ta iya
sanyawa da wannan mai najasar ba, ko kuma ta ji tsoron lokacin sallar zai fita
kafin ta yi wadancan ayyukan, to sai ta yi sallarta a haka tare da najasar,
kuma sallar ta yi, in shà Allâh. Domin kamar yadda malamai suka ce, shi gusar
da najasa sharadi ne a sallah amma yana tare da iko ne kuma da tunawa. Saboda
abin da Allaah ya ce
{ لَا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلَّا وُسْعَهَا }
Allaah ba ya
dora wa kowane rai face dai iyakan iyawarsa. (Surah Al-Baqarah: 286).
• Idan
kuwa ta yi sallar a cikin tufafin masu najasa a bisa mantuwa ko rashin sani ko
tilasci ne, to a nan ma sallarta ta yi babu wata ramuwa a kanta, in shà Allâh.
Saboda ayar da ta gabata, sannan kuma da hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِى الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ ».
Hakika! Allaah
ya yafe wa al’ummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta ta a kansa.
(Sahih Al-Jaami’: 1731).
Sai dai kuma
duk da haka za ta ɗauki
wadancan matakan na gusar da najasar daga jikin tufar domin sallolin da za su
biyo baya.
Allaah ya kara
mana fahimta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.