Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Basmalah A Lokacin Yin Alwala

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, menene hukuncin yin Basmalah a lokacin yin alwala: Farilla ko mustahabbi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Al-Imaam Ahmad da Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn Maajah sun riwaito hadisin da Abu-Hurairah ya samo daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« لاَ صَلاَةَ لِمَنْ لاَ وُضُوءَ لَهُ ، وَلاَ وُضُوءَ لِمَنْ لَمْ يَذْكُرِ اسْمَ اللَّهِ تَعَالَى عَلَيْهِ »

Babu sallah ga wanda ba shi da alwala, kuma babu alwala ga wanda bai ambaci sunan Allaah Ta’aala a kanta ba. (Sahih Sunan Abi-Daawud: 90).

Al-Hasan da Ibn Rahwuyah da Zaahiriyyah (Rahmatul Laahi Alaihim) sun zaɓi cewa wajibi ne yin Basmalah a cikin alwala, ta yadda idan ya bar yin ta da gangar dole ya sake yin alwalar.

Wannan kuma shi ne abin da As-Shawkaaniy da Siddiq Khaan da Al-Albaaniy (Rahmatul Laahi Alaihim) suka zaɓa. (Mausuu’atul Fiqhiyyatul Muyassarah: 1/94-95).

Amma kafa hujja da cewa: Harafin korewa (لَا) a cikin hadisin Abu-Hurairah da ya gabata yana kore kamalar alwalar ce, amma ba inganci ba saboda…

1. Masu riwaito siffar alwalarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba su ambaci Basmalah ba.

2. Kuma da rashin ambaton Basmalar a cikin hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya koya wa wani baƙauye siffar alwala shuɗi uku-uku.

Waɗannan duk ba su zama hujja ba, domin

(i) Asali abin da harafin korewa (لَا) yake nunawa kenan: Kore inganci da sahihancin samuwar haƙiƙanin alwalar.

(ii) Amma rashin ambaton Basmalah a cikin hadisan da suke bayanin siffar alwalarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai isa ya rage, ko ya sauya hukuncin hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ba. Domin kamar yadda malamai suka tabbatar: Rashin ambaton abu a cikin riwaya ba ilimi ba ne, ilimi yana cikin riwayar da take ɗauke da ambaton abin ne. To, ta yaya rashin ilimi zai soke ko ya kawar da ilimi!

A taƙaice dai

(i) Wajibi ne ga duk wanda ya zo yin alwala ya yi Basmalah.

(ii) Idan kuma ya manta a farko, to sai ya yi ta a duk lokacin da ya tuna.

(iii) Idan kuma a bayan gama alwalar ce shikenan babu laifi a gare shi.

Kamar dai wanda ya yi sallah da najasa a jikinsa ne, ko wanda ya fuskacin inda ba alƙibla ba a bisa mantuwa ko rashin iko. Babu komai a kansa a bayan ya yi sallama daga sallar.

Saboda hadisin Abu-Zarr Al-Ghiffaariy (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya ce: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

إِنَّ اللهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِي الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ

Haƙiƙa! Allaah ya yafe wa alummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta su a kansa. (Sahih Ibn Maajah: 1662).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdulaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments