An Yabawa Tsohuwar Mai Shari'a Justice Amina Adamu Augie Bisa Ga Zumuncin Da Ta Rike Da Mutanen Masarautar Kabin Argungu Tun Bayan Rasuwar Mai Gidanta Sen Adamu Baba Augie
Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alh Samaila Muhammad Mera CON Ne Yayi Wannan Yabon Lokacin Da Ya Karbi Tawagar Tsohuwar Mai Shari'a a Kotun Kolin Najeriya Justice Amina Adamu Augie a Ziyarar Godiya Da Ta Kawo Na Sarautar Gargajiya Da Aka Bata Ta Jarumar Kabi
Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Yace Ba Shakka Justice Amina Adamu Augie Ta Chanchanci Yabo Bisa Ga Yadda Ta Soma Aikin Shari'a Tun Daga Matakin Karamar Mai Shari'a Har Zuwa Kotun Kolin Najeriya Inda Tayi Murabus Cikin Mutunci Da Mutuntawa
Basaraken Ya Kuma Yabawa 'Yayan Jarumar Kabi Bisa Ga Yadda Suka Taimakawa Yayan Talakkawa a Makarantu Daban Daban Inda Yanzu Haka Wasun Su Suna Jami'a Sanadiyar Su
Alh Samaila Muhammad Mera CON Yace Justice Amina Augie Itace Macce Ta Farko Da Ta Rike Wannan Matsayi Na Jarumar Kabi Inda Jayo Hankalin Mata Dasu Zo a Dama Dasu Wajen Basu Sarautun Gargajiya Don Bada Tasu Gudummawa
Tun Farko Da Yake Jawabi Amadadin Jarumar Kabi Mai Girma Kundudan Kabi Alh Ibrahim Hasan Kwaido Yace a Shirye Suke Wajen Bada Gagarumar Gudummawa Masarautar Kabin Argungu Don Ciyarda Ita Gaba
Ya Kuma Ce Ina Fatar Wannan Soma Tabi Ne Wajen Baiwa Mata Wani Matsayi a Masarautar Don Suma Su Bada Tasu Gudummawa Wajen Kawo Ci Gaban Masarautar
Ya Kuma Godewa Mai Martaba Sarki Da Yan Majalisar Shi Bisa Ga Wannan Karramawa Da Aka Yiwa Yar Uwar Su Na Bata Wannan Sarauta Ta JARUMAR KABI
Jama'a Da Dama Ne Suka Rako Jarumar Kabi Ciki Hadda Tsohon Mataimakin Gwamnan Jahar Kebbi Alh Bello Dantani Magajin Rafin Kabi, Wazirin Kabi Alh Sani Ango , Uwayen Kasar Augie , Kwaido Da Sauran Yan Uwa Da Masoya
Allah Ka Daukaka Masarautar Kabin Argungu Da Mutanen Ta
Kakakin Cikin Gida Zager
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.