"Sai ka bani mota 504 siteshin wagunu in shige ina ta bugun turu
Kuma ka bani mai tamfal ta d'auki kaya da sauran yara na
Furasdan Shehu Shagari nikam abin da yayyi man ya kyauta man
Ya bani mota 504 sitenshin wagunu, Dankwairo,
Sai nis shige can dag gaba
Nan baya ga y'an yara na
K'arshen ta ga kotsanni na
Duk garin da nid dosa an san makad'in mulki ne ni
Ga yanzu ni bani tsoron hanya sai dai hanya ta ji tsoro na
Ni Sarkin Makad'an NPN, Alhaji na kwan jin dad'i, mahassadan mu sun kwan jin haushi
Daga
Zauren Makaɗa da Mawaƙa
0 Comments
Post your comment or ask a question.