𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Wai wanene ya
fara yin Tajweedin Qur’ani? Kuma mutum nawa ne suka yi Tajweedin Qur’ani a
bayansa?
𝐀𝐌��𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Ma’anar At-Tajweed a wurin
malamai, wani ilimi ne wanda da shi ake sanin yadda ake kyautata karatun
Alqur’ani, ta hanyar bai wa kowane harafi daga cikin haruffan Alqur’anin haƙƙinsa
da duk abin da ya cancance shi, kamar ta kula da mafitarsa da siffofinsa da
hukunce-hukuncensa da sauransu.
Yin aiki da ƙa’idojin At-Tajweed a wurin
karatun Alqur’ani
wajibi ne a kan duk mai karatun Alqur’ani,
kamar yadda malamai suka faɗa
وَالْأَخْذُ بِالتَّجْوِيدِ حَتْمٌ لَازِمٌ * مَنْ لَمْ يُجَوِّدِ الْقُرْآنَ آثِــمٌ
لِأَنَّــهُ بِــهِ الْإِلَـــهُ أَنْـــــزَلَا * وَهَكَـذَا مِنْهُ إِلَيْنَـا وَصَـلَا
Kuma yin aiki da Tajweed dole ne
lazimi, duk wanda ba ya Tajweedin Qur’ani mai zunubi ne.
Saboda da shi ne Allaah ya saukar,
haka nan daga gare shi zuwa wurinmu da sadaddun isnadai. (Al-Jazariyyah na
Al-Imaam Al-Jazariy)
Dalilai ko Hujjojin da suka nuna
wannan wajibcin suna da yawa a cikin Alqur’ani da Hadisi, kamar inda Allaah
Ta’aala ya ce
الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَتْلُونَهُ حَقَّ تِلَاوَتِهِ أُولَئِكَ يُؤْمِنُونَ بِهِ
Wanda muka ba su Littafi suna
karanta shi a bisa haƙƙin karatunsa, waɗannan
su ne suka yi imani da shi. (Surah Al-Baqarah: 121)
Daga cikin malaman da suka
fassara wannan ayar akwai Sahabi Abdullaah Bn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) wanda
ya ce
وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ ، إِنَّ حَقَّ
تِلَاوَتِهِ : أَنْ يَحِلَّ حَلَالَهُ وَيُحَرِّمَ حَرَامَهُ ، وَيَقْرَأَهُ كَمَا
أَنْزَلَهُ اللهُ ، وَلَا يُحَرِّفَ
الْكَلِمَ عَنْ مَوَاضِعِهِ ، وَلَا يَتَأَوَّلَ
مِنْهُ شَيْئاً عَلَى غَيْرِ تَأْوِيلِهِ
Na rantse da wanda rai na ke a
hannunsa! Haƙiƙa, haƙƙin karatunsa shi ne: Ya halatta abin da Alqur’ani ya halatta kuma ya
haramta abin da ya haramta, kuma ya karanta shi kamar yadda Allaah ya saukar da
shi, kuma kar ya sauya kalmominsa daga wuraren da aka ajiye su, kuma kar ya
fassara wani abu daga cikinsa ba da irin fassararsa ba.
Karanta shi kamar yadda Allaah ya
saukar da shi, shi ne a karanta shi da Tajweed. Wannan kuwa wajibi ne, tun da
dai yin hakan yana daga cikin siffar masu imani.
Kuma Allaah Ta’aala ya ce
وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتِيلًا
Kuma ka jera karatun Alqur’ani
daki-daki. (Surah Al-Muzzammil: 4)
Sannan kuma daga cikin malaman da
suka fassara wannan ayar akwai babban Tabi’in nan Al-Hasan Al-Basariy
(Rahimahul Laah). Al-Imaam Ibn Jareer At-Tabariy ya riwaito da isnadinsa
kyakkyawa daga gare shi, inda ya faɗa
a kan ma’anar wannan ayar cewa
اقرأه قراءة بينة
Ka karanta shi karatu a fili
bayyananne.
Wannan kuma ba ya samuwa sai ga
wanda ya bi ƙa’idojin
Tajweed a wurin karatunsa. Kuma bin wannan umurnin na Allaah Ubangijin Halittu
wajibi ne, kamar yadda yake a asali.
Yana daga cikin aikin da Tajweed
kyautata murya da karatun, kamar yadda Sahabi Al-Baraa’ Bn Azib (Radiyal Laahu
Anhu) ya riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
زَيِّنُوا الْقُرْآنَ بِأَصْوَاتِكُمْ
Ku ƙawata Alqur’ani da muryoyinku. (As-Saheehah: 772)
Kuma Sahabi Abu-Hurairah (Radiyal
Laahu Anhu) ya riwaito daga gare shi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya ce
لَيْسَ مِنَّا مَنْ لَمْ يَتَغَنَّ بِالْقُرْآن
Wanda ba ya kyautata muryarsa da
karatun Alqur’ani ba ya tare da mu. (Sahih Al-Bukhaariy: 7527)
Kuma daga cikin waɗanda suka yi fice da zaƙin
murya a wurin karatu tun a zamanin farko akwai sahabi Abu-Musa Al-Ash’ariy (Radiyal Laahu Anhu), wanda
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce masa
يَا أَبَا مُوسَى ، لَقَدْ أُوتِيتَ
مِزْمَاراً مِنْ مَزَامِيرِ آلِ دَاوُدَ
Abu-Musa, haƙiƙa an
ba ka murya mai zaƙin murya irin zaƙin muryar Annabi Daawud (Alaihis Salaam).
(Sahih Al-Bukhaariy: 5048; Sahih Muslim: 793)
Yana daga cikin Tajweed a cikin
karatun Alqur’ani a riƙa yin madda (tsawaita murya) a wurarensu. Saboda an tambayi
Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) a kan yadda karatun Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ke? Sai ya ce
كَانَتْ مَدّاً. ثُمَّ قَرَأَ بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ ، يَمُدُّ بِبِسْمِ
اللهِ ، وَيَمُدُّ بِالرَّحْمَنِ
، وَيَمُدُّ بِالرّحِيمِ
Karatunsa ya kasance mai madda
(tsawaitawa) ne: Sai kuma ya karanta: Bismil Laahir Rahmaanir Raheem. Sai ya
tsawaita: Bismil Laah, kuma ya tsawaita: Ar-Rahmaan, kuma ya tsawaita:
Ar-Raheem. (Sahih Al-Bukhaariy: 5046)
Yana daga cikin kyakkyawan
Tajweed a Sunnah a riƙa tsayawa a ƙarshen kowace aya, domin haka
Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) ta siffata karatun Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), cewa
يَقْطَعُ قِرَاءَتَهُ آيَةً آيَةً
Yana yanke karatunsa aya-aya. (Sahih
At-Tirmiziy: 3/13; 2927)
Sakamakon mai kyautata karatun
Alqur’ani shi ne samun Gidan Aljannah A Lahira. Sahabi Abdullaah Bn Amr
(Radiyal Laahu Abhumaa) ya riwaito daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) cewa:
يُقَالُ لِصَاحِبِ الْقُرْآنِ : اقْرَأْ وَارْتَقِ وَرَتِّلْ كَمَا كُنْتَ تُرَتِّلُ فِي الدُّنْيَا ، فَإِنَّ مِنْزِلَكَ
عِنْدَ أَخِرِ آيَةٍ تَقْرَؤُهَا
Za a ce wa makarancin Alqur’ani:
Karanta ka ƙara hawa, kuma ka kyautata karatun daki-daki kamar yadda kake
yi a duniya. Domin masaukinka yana a aya ta ƙarshe ce da kake iya karantawa. (Sahih
At-Tirmiziy: 2329)
Daga waɗannan bayanan a taƙaice ya fito fili cewa
1. Wanda aka saukar masa da
Alqur’ani, watau Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shi ne
wanda ya fara yin Tajweedin Alqur’ani.
2. Daga bayansa kuma sai
Sahabbansa musamman irin su Abu-Musa Al-Ash’ariy (Radiyal Laahu Anhum). Sai
kuma waɗanda suka bi
hanyarsu daga cikin Taabi’ai da mabiyansu da kyautatawa har zuwa yau, kuma har
zuwa Tashin Ƙiyama.
Allaah ya datar da mu ga bin
hanyarsu har zuwa ƙarshenmu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.