Ticker

6/recent/ticker-posts

Siffofin ’Yan Aljannah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wai waɗanne alamu ne suke tabbatar wa mutum cewa Aljannah ce makomarsa a bayan mutuwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh

Abin da muka sani dai shi ne siffofin ’yan Aljannah a dunƙule kawai. Allaah Taaala ya ce

۞ وَسَارِعُوۤا۟ إِلَىٰ مَغۡفِرَةࣲ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِینَ ٣٣١۝ ٱلَّذِینَ یُنفِقُونَ فِی ٱلسَّرَّاۤءِ وَٱلضَّرَّاۤءِ وَٱلۡكَـٰظِمِینَ ٱلۡغَیۡظَ وَٱلۡعَافِینَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ یُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِینَ ٤٣١۝ وَٱلَّذِینَ إِذَا فَعَلُوا۟ فَـٰحِشَةً أَوۡ ظَلَمُوۤا۟ أَنفُسَهُمۡ ذَكَرُوا۟ ٱللَّهَ فَٱسۡتَغۡفَرُوا۟ لِذُنُوبِهِمۡ وَمَن یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَلَمۡ یُصِرُّوا۟ عَلَىٰ مَا فَعَلُوا۟ وَهُمۡ یَعۡلَمُونَ ٥٣١۝ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ جَزَاۤؤُهُم مَّغۡفِرَةࣱ مِّن رَّبِّهِمۡ وَجَنَّـٰتࣱ تَجۡرِی مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَـٰرُ خَـٰلِدِینَ فِیهَاۚ وَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَـٰمِلِینَ ٦٣١۝

Kuma ku yi gaggawa zuwa ga samun gafara daga Ubangijinku da samun Aljannah faɗinta kamar faɗin sammai da ƙasa, an yi tattalinta domin masu taqawa. Waɗanda suke ciyarwa a cikin wadata da ƙuncin rayuwa, kuma masu kame fushi, masu yafewa ga mutane, kuma Allaah yana son masu kyautatawa. Kuma waɗanda idan suka aikata alfasha ko suka cuci rayukansu sai su tuna Allaah sai kuma su nemi gafara domin zunubansu, kuma wanene yake gafarar zunubai in ba Allaah ba, kuma ba su dogewa a kan abin da suka aikata alhali kuwa suna sane. Waɗannan sakamakonsu gafara ce daga Ubangijinsu da wata Aljannah wacce ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinta, suna madawwama a cikinta, kuma madalla da ladan masu aiki. (Surah Al-Imraan: 133-136).

۞ أَفَمَن یَعۡلَمُ أَنَّمَاۤ أُنزِلَ إِلَیۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰۤۚ إِنَّمَا یَتَذَكَّرُ أُو۟لُوا۟ ٱلۡأَلۡبَـٰبِ ٩١۝ ٱلَّذِینَ یُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا یَنقُضُونَ ٱلۡمِیثَـٰقَ ٠٢۝ وَٱلَّذِینَ یَصِلُونَ مَاۤ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦۤ أَن یُوصَلَ وَیَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَیَخَافُونَ سُوۤءَ ٱلۡحِسَابِ ١٢۝ وَٱلَّذِینَ صَبَرُوا۟ ٱبۡتِغَاۤءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُوا۟ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُوا۟ مِمَّا رَزَقۡنَـٰهُمۡ سِرࣰّا وَعَلَانِیَةࣰ وَیَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّیِّئَةَ أُو۟لَـٰۤىِٕكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ ٢٢۝ جَنَّـٰتُ عَدۡنࣲ یَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَاۤىِٕهِمۡ وَأَزۡوَ ٰ⁠جِهِمۡ وَذُرِّیَّـٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَـٰۤىِٕكَةُ یَدۡخُلُونَ عَلَیۡهِم مِّن كُلِّ بَابࣲ ٣٢۝ سَلَـٰمٌ عَلَیۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ ٤٢۝

Shin wai wanda ya san cewa: Duk abin da aka saukar maka da wurin Ubangijinka shi ne gaskiya yana yin daidai da makaho? Masu hankali ne kaɗai suke yin tunani. Waɗanda suke cika alƙawarin Allaah kuma ba su warware alƙawari. Kuma waɗanda suke sadar da abin da Allaah ya yi umurnin a sadar da shi, suke tsoron Ubangijinsu, kuma suke tsoron mummunar hisabi. Kuma waɗanda suke yin haƙuri don neman Fuskar Ubangijinsu, suke saida Sallah kuma suke ciyarwa daga abin da muka azurta su da shi, ko a ɓoye ko a bayyane, kuma suke tunkuɗe mummunan aiki da kyakkyawa. Waɗannan su ke da ƙarshen gida mai kyau. Aljannar Dawwama ce za su shige ta tare da duk wanda ya kyautata daga cikin iyayensu da matan aurensu da zuriyarsu, kuma malaiku suna shiga gare su ta kowace ƙofa. Suna cewa: Amincin Allaah ya tabbata a gare ku. Madalla da ƙarshen gida mai kyau! (Surah Ar-Raad: 19-24)

قَدْ اَفْلَحَ الْمُؤْمِنُوْنَۙ ١۝ الَّذِيْنَ هُمْ فِىْ صَلَاتِهِمْ خَاشِعُوْنَۙ ٢۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ عَنِ اللَّغْوِ مُعْرِضُوْنَۙ ٣۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ لِلزَّكٰوةِ فَاعِلُوْنَۙ ٤۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ لِفُرُوْجِهِمْ حٰفِظُوْنَۙ ٥۝ اِلَّا عَلٰۤى اَزْوَاجِهِمْ اَوْ مَا مَلَـكَتْ اَيْمَانُهُمْ فَاِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُوْمِيْنَۚ ٦۝ فَمَنِ ابْتَغٰى وَرَاۤءَ ذٰلِكَ فَاُولٰۤٮِٕكَ هُمُ الْعٰدُوْنَۚ ٧۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ لِاَمٰنٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُوْنَۙ ٨۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ عَلٰى صَلَوٰتِهِمْ يُحَافِظُوْنَۘ ٩۝ اُولٰۤٮِٕكَ هُمُ الْوَارِثُوْنَۙ ٠١۝ الَّذِيْنَ يَرِثُوْنَ الْفِرْدَوْسَۗ هُمْ فِيْهَا خٰلِدُوْنَ ١١۝

Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ. Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne. Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne. Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne. Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarwa ne. Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne. Sabõda haka wanda ya nmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarwar haddi. Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarwa ne. Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarwa. Waɗannan, sũ ne magãda. Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne. (Surah Al-Mu’minuun: 1-11)

وَعِبَادُ الرَّحْمٰنِ الَّذِيْنَ يَمْشُوْنَ عَلَى الْاَرْضِ هَوْنًا وَّاِذَا خَاطَبَهُمُ الْجٰهِلُوْنَ قَالُوْا سَلٰمًا ٣٦۝ وَالَّذِيْنَ يَبِيْتُوْنَ لِرَبِّهِمْ سُجَّدًا وَّقِيَامًا ٤٦۝ وَالَّذِيْنَ يَقُوْلُوْنَ رَبَّنَا اصْرِفْ عَنَّا عَذَابَ جَهَـنَّمَۖ اِنَّ عَذَابَهَا كَانَ غَرَامًاۖ ٥٦۝ اِنَّهَا سَاۤءَتْ مُسْتَقَرًّا وَّمُقَامًا ٦٦۝ وَالَّذِيْنَ اِذَاۤ اَنْفَقُوْا لَمْ يُسْرِفُوْا وَلَمْ يَقْتُرُوْا وَكَانَ بَيْنَ ذٰلِكَ قَوَامًا ٧٦۝ وَالَّذِيْنَ لَا يَدْعُوْنَ مَعَ اللّٰهِ اِلٰهًا اٰخَرَ وَلَا يَقْتُلُوْنَ النَّفْسَ الَّتِىْ حَرَّمَ اللّٰهُ اِلَّا بِالْحَـقِّ وَلَا يَزْنُوْنَۚ وَمَنْ يَّفْعَلْ ذٰلِكَ يَلْقَ اَثَامًاۙ ٨٦۝ يُضٰعَفْ لَهُ الْعَذَابُ يَوْمَ الْقِيٰمَةِ وَيَخْلُدْ فِيْهٖ مُهَانًاۖ ٩٦۝ اِلَّا مَنْ تَابَ وَاٰمَنَ وَعَمِلَ عَمَلًاصَالِحًـا فَاُولٰۤٮِٕكَ يُبَدِّلُ اللّٰهُ سَيِّاٰتِهِمْ حَسَنٰتٍۗ وَكَانَ اللّٰهُ غَفُوْرًا رَّحِيْمًا ٠٧۝ وَمَنْ تَابَ وَعَمِلَ صَالِحًـا فَاِنَّهٗ يَتُوْبُ اِلَى اللّٰهِ مَتَابًا ١٧۝ وَالَّذِيْنَ لَا يَشْهَدُوْنَ الزُّوْرَۙوَ اِذَا مَرُّوْا بِاللَّغْوِ مَرُّوْا كِرَامًا ٢٧۝ وَالَّذِيْنَ اِذَا ذُكِّرُوْا بِاٰيٰتِ رَبِّهِمْ لَمْ يَخِرُّوْا عَلَيْهَا صُمًّا وَّعُمْيَانًا ٣٧۝ وَالَّذِيْنَ يَقُوْلُوْنَ رَبَّنَا هَبْ لَـنَا مِنْ اَزْوَاجِنَا وَذُرِّيّٰتِنَا قُرَّةَ اَعْيُنٍ وَّاجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِيْنَ اِمَامًا ٤٧۝ اُولٰۤٮِٕكَ يُجْزَوْنَ الْغُرْفَةَ بِمَا صَبَرُوْا وَيُلَقَّوْنَ فِيْهَا تَحِيَّةً وَّسَلٰمًاۙ ٥٧۝ خٰلِدِيْنَ فِيْهَاۗحَسُنَتْ مُسْتَقَرًّا وَّمُقَامًا ٦٧۝

Kuma bãyin Mai rahama su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jãhilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salãma" (a zama lafiya). Kuma waɗanda suke kwãna sunã mãsu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu. Kuma waɗanda suke cwa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra. Lalle ne ita ta mũnana ta zama wurin tabbata da mazauni. Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, bã su yin ɓarna, kuma bã su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakãnin wancan da tsakaitãwa. Kuma waɗanda bã su kiran wani ubangiji tãre da Allah, kuma bã su kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da hakki kuma bã su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka, A riɓanya masa azãba a Rãnar kiyãma. Kuma ya tabbata a cikinta yanã wulakantacce. Sai wanda ya tũba, kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yanã musanya miyãgun ayyukansu da mãsu kyau. Allah Ya kasance Mai gãfara Mai jin ƙai. Kuma wanda ya tũba, kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tũba zuwa ga Allah. Kuma waɗanda suke bã su yin shaidar zur, kuma idan sun shũɗe ga yasassar magana sai su shũɗe suna mãsu mutumci. Kuma waɗanda suke idan an tunãtar da su da ãyõyin Allah, bã su saukar da kai, sunã kurame da makãfi. Kuma waɗanda suke cwa "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu sanyin idãnu daga mãtanmu da zũriyarmu, kuma Ka sanya mu shũgabanni ga mãsu taƙawa. " Waɗannan anã sãka musu da bne, sabõda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci. Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni. (Surah Al-Furqaan: 63-76)

اِنَّ اللّٰهَ اشْتَرٰى مِنَ الْمُؤْمِنِيْنَ اَنْفُسَهُمْ وَاَمْوَالَهُمْ بِاَنَّ لَهُمُ الْجَــنَّةَۗيُقَاتِلُوْنَ فِىْ سَبِيْلِ اللّٰهِ فَيَقْتُلُوْنَ وَ يُقْتَلُوْنَۗ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا فِى التَّوْرٰٮةِ وَالْاِنْجِيْلِ وَالْقُرْاٰنِۗ وَمَنْ اَوْفٰى بِعَهْدِهٖ مِنَ اللّٰهِ فَاسْتَـبْشِرُوْا بِبَيْعِكُمُ الَّذِىْ بَايَعْتُمْ بِهٖۗ وَذٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيْمُ ١١١۝ اَلتَّاۤٮِٕبُوْنَ الْعٰبِدُوْنَ الْحٰمِدُوْنَ السَّاۤٮِٕحُوْنَ الرّٰكِعُوْنَ السّٰجِدُوْنَ الْاٰمِرُوْنَ بِالْمَعْرُوْفِ وَالنَّاهُوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَالْحٰــفِظُوْنَ لِحُدُوْدِ اللّٰهِۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِيْنَ ٢١١۝

Lalle ne, Allah Ya saya daga mummunai, rãyukansu da dũkiyõyinsu, da cwa sunã da Aljanna, sunã yin yãƙi a cikin hanyar Allah, sabõda haka sunã kashwa anã kash su. (Allah Yã yi) wa'adi a kanSa, tabbace a cikin Attaura da Linjĩla da Alƙur'ãni. Kuma wãne ne mafi cikãwa da alkawarinsa daga Allah? Sabõda haka ku yi bushãra da cinikinku wanda kuka ƙulla da Shi. Kuma wancan shi ne babban rabo, mai girma. Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarwã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai. (Surah At-Taubah: 111-112)

وَاُزْلِفَتِ الْجَـنَّةُ لِلْمُتَّقِيْنَ غَيْرَ بَعِيْدٍ ١٣۝ هٰذَا مَا تُوْعَدُوْنَ لِكُلِّ اَوَّابٍ حَفِيْظٍۚ ٢٣۝ مَنْ خَشِىَ الرَّحْمٰنَ بِالْغَيْبِ وَجَاۤءَ بِقَلْبٍ مُّنِيْبِۙ ٣٣۝ ٱدْخُلُوْهَا بِسَلٰمٍۗ ذٰلِكَ يَوْمُ الْخُلُوْدِ ٤٣۝

Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba. Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa). Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali. (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama. " (Surah Qaaf: 31-34)

اِلَّا الْمُصَلِّيْنَۙ ٢٢۝ الَّذِيْنَ هُمْ عَلٰى صَلَاتِهِمْ دَاۤٮِٕمُوْنَۖ ٣٢۝ وَالَّذِيْنَ فِىْۤ اَمْوَالِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُوْمٌۖ ٤٢۝ لِّلسَّاۤٮِٕلِ وَالْمَحْرُوْمِۖ ٥٢۝ وَالَّذِيْنَ يُصَدِّقُوْنَ بِيَوْمِ الدِّيْنِۖ ٦٢۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِمْ مُّشْفِقُوْنَۚ ٧٢۝ اِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُوْنٍ ٨٢۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ لِفُرُوْجِهِمْ حٰفِظُوْنَۙ ٩٢۝ اِلَّا عَلٰۤى اَزْوَاجِهِمْ اَوْ مَا مَلَـكَتْ اَيْمَانُهُمْ فَاِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُوْمِيْنَۚ ٠٣۝ فَمَنِ ابْتَغٰى وَرَاۤءَ ذٰلِكَ فَاُولٰۤٮِٕكَ هُمُ الْعٰدُوْنَۚ ١٣۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ لِاَمٰنٰتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رٰعُوْنَۖ ٢٣۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ بِشَهٰدٰتِهِمْ قَاۤٮِٕمُوْنَۖ ٣٣۝ وَالَّذِيْنَ هُمْ عَلٰى صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُوْنَۗ ٤٣۝ اُولٰۤٮِٕكَ فِىْ جَنّٰتٍ مُّكْرَمُوْنَۗ ٥٣۝

Sai mãsu yin Sallah, Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne. Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne. Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon. Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako. Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro. Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincwaba ce. Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne. Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne. To, duk wanda ya nmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka. Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarwa ne. Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgwa ne. Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarwa ne. Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne. (Surah Al-Ma’aarij: 22-35).

Duk wanda ya tsare irin waɗannan ayyukan a cikin Imani da Tsoron Allaah da koyi da koyarwar Sunnar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) don neman kyakkyawan sakamako da tsoron azabar Ubangiji Ta’aal shi ne ake wa albishir da Gidan Aljannah a Lahira.

Amma tabbatar da samun Gidan Aljannah ko Gidan Wuta ga wani mutum guda daga cikin musulmi masu fuskantar Alqibla a cikin wannan rayuwar ta duniya ba abu ne mai sauƙi ba, kuma ma ba mai yiwuwa ba ne. Sai dai ga wanda nassi sahihi kuma sarihi ya tabbata a kansa daga Allaah ko Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Domin makomar mutane na Wuta ko Aljannah yana wurin Allaah ne.

 وَلِلَّهِ مَا فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تِ وَمَا فِی ٱلۡأَرۡضِۚ یَغۡفِرُ لِمَن یَشَاۤءُ وَیُعَذِّبُ مَن یَشَاۤءُۚ وَٱللَّهُ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ

Kuma duk abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa na Allaah ne kaɗai, Yana yin gafara ga wanda ya ga dama, kuma yana azabtar da wanda ya gadama, kuma Allaah mai yawan Gafara ne, mai yawan Rahama. (Surah Al-Imraan: 129).

Sannan kuma a ranar da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya je dubo Sahabinsa Ka’ab Bn Ujirah (Radiyal Laahu Anhu), da ya shiga wurinsa kuma ya ce: Ka’ab, albishirinka! Sai kuwa mahaifiyarsa ta ce: Kai Ka’ab! Ina maka murna da samun Aljannah! Sai Annabi (Sallal Laa Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Wacece wannan mai yanke hukunci da rantsuwa a kan Allaah?! Ka’ab ya ce: Mahaifiyata ce! Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

وَمَا يُدْرِيكِ يَا أمَّ كَعْبٍ ؟ ! لَعَلَّ كَعْباً قَالَ مَا لَا يَعْنِيهِ ، أَوْ مَنَعَ مَا لَا يُغْنِيهِ

Me ya sanar da ke ne, Ummu-Ka’ab?! Wataƙila fa Kaab ya faɗi wani abin da bai shafe shi ba, ko kuma ya ƙi bayar da abin da ba zai wadata shi ba! (Silsilah Saheehah: 3103)

Don haka, mutum ya ayyana wa kansa ko waninsa cewa shi ɗin nan ɗan Aljannah ne ko ɗan Wuta, kamar shiga gonar Allaah Ta’aala ne kawai. Shiyasa dole a nan sai kowa ya tsaya ga irin abin da Allaah ko Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) suka faɗa kawai.

Allaah ya tabbatar da shiga Wuta ga Fir’auna da Abu-Lahab da makamantansu daga cikin la’antattu.

Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tabbatar da samun Aljannah ga Manyan Sahabbansa guda goma

1. Abu-Bakar As-Siddeeq.

2. Umar Bn Al-Khattaab.

3. Uthmaan Bn Affaan.

4. Aliy Bn Abi-Taalib.

5. Sa’ad Bn Abi-Waqqaas.

6. Sa’eed Bn Zaid.

7. Abdurrahman Bn Auf.

8. Dalhah Bn Ubaidillaah

9. Zubair Bn Al-Awwaam.

10. Bilaal Al-Mu’azzin.

11. Abdullaah Bn Salaam.

12. Ukkaashah Bn Mihsaan.

13. Fatimah Bint Rasuulil Laah.

14. Al-Hasan, da Al-Husain Ibnai Aliy Bn Abi-Taalib.

15. Da baƙar matar nan wacce ta zaɓi yin haƙuri da matsalar farfaɗiya a kan samun waraka daga addu’arsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da sauransu dai masu yawa _(Radiyal Laahu Anhum). Waɗannan duk muna tabbatar musu da samun Aljannah kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa.

Waɗansu malamai kuma sun ƙara a cikin masu samun Aljannah akwai duk wanda jamaar musulmi na kirki suka haɗu a kan yi masa kyakkyawar yabo na kirki a bayan mutuwarsa. Sai dai kuma wannan maganar ba ta kai ta sama ƙarfi ba, domin samun haɗuwar mutanen kirki a zamunnan nan na ƙarshe abu ne mawuyaci. Sannan kuma ga yadda mutane suke amincewa da yarda wasu ayyukan mutum na rayuwar duniya kawai ba addini ba!

Wannan matsayar ta rashin yin shisshigi a kan ambata wa wani cewa shi ɗan Aljannah ne ko ɗan Wuta ita ce Aqidar Ahlus-Sunnah , saɓanin ’yan bidi’a daga cikin Mu’utazilah da Khawaarij da Raafidah da sauransu waɗanda suke shigar da wanda suka ga dama a cikin Aljannah, kuma suke shigar da wanda suka ga dama a cikin Wuta.

Al-Imaam At-Tahaawiy ya faɗa a cikin Littafin Aqidarsa (#70) cewa

وَلَا نُنْزِلُ أَحَدًا مِنْهُمْ جَنَّةً وَلَا نَارًا ، وَلَا نَشْهَدُ عَلَيْهِمْ بِكُفْرٍ وَلَا شْرِكٍ وَلَا نِفَاقٍ ، مَا لَمْ يَظْهَرْ مِنْهُمْ شَيْءٌ مِنْ ذَلِكَ ، وَنَذَرَ سَرَائِرَهُمْ إِلَى اللهِ تَعَالَى

Kuma ba mu shigar da wani ɗaya daga cikin masu duban Alqibla a cikin Aljannah ko Wuta, kuma ba mu yin shaida a kansu da kafirci ko shirka ko munafunci, matuƙar dai wani abu na hakan bai bayyana daga gare su ba, kuma muna ƙyale sirrinsu ga Allaah Taaala kawai.

Allaah ya shiryar da mu. Allah Yasa Aljannah ce makomarmu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments