Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Buɗe Gidan Kwallo ⚽

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun alaykum ya shykh antashi lafiya? Mallam tambayata itace menene hukuncin sana'ar buɗe gidan kallon kwallo.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Sana'ar buɗe gidan kallon ƙwallo baya halatta ga musulmi a yau, saboda abin da muke gane ma idanun na irin abin da sana'ar ke haifarwa na caca, gaba da ƙiyayya tsakanin musulmi, faɗa tsakanin ƴan club, da zagi-zage, wani lokaci har ya kai ga ji ma juna ciwo ko kisa a tsakanin su. Bayan haka akwai tozarta sallah daga barin lokacin ta. Sannan, galibi, wuri na lalata tarbiyar musulmi ne. Bayan haka yana hana musulmi zikirin Allah da kuma sallah. Don haka ne ya zamo haramun.

Don haka musulmi a ko da yaushe, ya nemi arziki, ta hanyar da zata gyara al'umma da ɗora ta a kan abin da zai amfanar da ita bin Allah da Manzonsa, kar ya nemi arziki ta hanyar da za ta rusa ko ta lalata tarbiyar al'umma, ko kuma ta taimaka wajen lalacewarta ba. Allah Yace:

وَتَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَ ٰ⁠نِۚ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِیدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku taimaki juna a kan alheri da taqawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi, kuma ku ji tsoron Allaah. Haƙiƙa Allaah mai tsananin uƙuba ne. (Surah Al-Maaidah: 2)

Sana'a hanya ce ta taimakon al'umma, don haka wajibi ne, musulmi ya zaɓi sana'ar da zata kai shi ga samun alkhairin duniya da lahira a lokaci guda.

WALLAHU TA'AALA A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments