Shin Dole Sai Na Tsefe Gashi Na Yayin Wankan Haila

    TAMBAYA (52)

    Dan Allah malam ayimin Karin bayani game da idan mace zatayi wankan haila sai ta tsefe gashin kanta

    AMSA

    Alhamdulillah

    Bai wajabta ga macen da take wankan janaba ta warware gashinta gaba daya ba to amman ya zama wajibi ruwa ya ratsa ko wanne lungu da saqo na jikinta, har gashin kanta

    An tambayi Shaikh Abd al-Azeez ibn Baaz (Rahimahullah), wasu matan suna tufke gashin kansu kuma idan sunzo wankan janaba basa warwarewa. Shin wankansu yayi ? A kula cewar ruwan bai ratsa ko ina a cikin gashinta ba. Don Allah a bamu shawara. Allah ya saka da alkhairi

    Sai ya bada amsa kamar haka; "Idan har mace ta zuba ruwa a gashin kanta ya wadatar mata, saboda hadisin Umm Salama (RA) cewar ta tambayi Annabi SAW akan hakan. Tace: Ni mace ce mai yalwar gashi akaina, shin zan warware gashi na a lokacin da nake wankan janabah ?

    Sai Annabi SAW ya ce: "A'a, ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, bayan haka sai ki kwara ruwa ajikinki, silar haka kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahih Muslim

    Don haka idan mace ta zuba ruwa a kanta sau uku ya wadatar mata kamar yanda wannan sahihin hadisin ya nuna

    Majmoo' Fataawa al-Shaykh Ibn Baaz 10/182

    Shaykh Bin Baaz ya ce: A bangaren wankan janabah (ghusl) anfi son a zuba ruwa sau uku akai, amman shafar gashin bazai wadatar ba saboda wancan hadisin dake cikin Sahih Muslim

    Majmoo' Fataawa al-Shaykh Ibn Baaz 10/161

    Ibn al-Qayyim a cikin Tahdheeb al-Sunan:

    Wannan hadisin na Umm Salamah ya nuna cewar bai wajaba mace ta warware gashin kanta ba bayan janabah. Malamai sun yarda da wannan riwayar saidai akwai hadisin da aka rawaito daga Abdullahi ibn Amr da kuma Ibrahim al-Nakha'i wanda ya ce: zata warware gashin. Saidai bamu ji wani wanda ya goyi bayan wadannan malaman ba

    Shaykh al-Uthaymeen ya ce: mafi karancin abinda zatayi shi ne ta tabbatarda ruwa ya ratsa ko'ina a jikinta, har karkashin gashinta. Zaifi kyau mace tayi hakan kamardai yanda aka rawaito daga Annabi SAW cewar lokacin da Asma' bint Shakl tayi tambaya akan wanka bayan janabah

    Annabi SAW ya ce: "Dayanku zata dauki ruwanta tareda ganyen lotus ta tsarkake kanta ta tsarkake jikinta sosai. Sai ta zuba ruwa akanta ta cuda sosai ta yanda zai ratsa koina akanta daganan saita kwarara ruwan a jikinta. Sai ta dauki kaya (ko towel) wanda yakeda almuski ta tsane jikinta" Asma' tace: "Ta yaya zata tsarkake kanta da shi ?" Sai Annabi SAW ya ce: "Subhanallah, ta tsarkake jikinta da shi"

    Sai Nana Aisha (RA) ta kara da cewar: "Ta bi duk inda jini ya bata a jikinta ta goge"

    Bukhari da Muslim ne suka rawaito hadisin

    Ba wai dolene sai mace ta kwance gashinta ba har saidai indai ya zamana ta daureshi ne tamau-tamau saboda gudun kada ruwa ya qi shiga gashin gaba daya, saboda wancan hadisin na Umm Salamah

    Sai Shaykh al-Uthaymeen ya kawo hujjar wancan hadisin wanda muka kawo a baya

    Majmoo' Fataawa Ibn 'Uthaymeen, 11/318, 319

    Domin karin bayani sai a duba amsar tambaya ta: 34,776 da 27,065 da 9,755 da kuma tambayata 2,648

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa

    Usman D. Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.