𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Na ji audio
clip na wani malami da yake karatun Iziyya yana cewa, haram ne miji ya sadu da
matarsa idan akwai wani a tare da su a ɗakin,
ko da kuwa ɗansu ne ƙarami,
kuma ko da yana barci. To, waɗanda
ɗakin na su ƙarami
ne kuma shi kenan musu, yaya za su kauce wa aikata wannan haram ɗin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul
Laah:
Gaskiya ne, haka As-Shaikh
Abul-Hasan Aliy Al-Maalikiy ya faɗa
a cikin Iziyyah, ya ce
وَلَا يُصِيبُ
الرَّجُلُ زَوْجَتَهُ أَوْ أَمَتَهُ وَمَعَهُ أَحَدٌ فِي الْبَيْتِ صَغِيرًا كَانَ أَوْ كَبِيرًا يَقْظَانَ أَوْ نَائِماً
Kuma kar namiji ya sadu da
matarsa ko kuyangarsa alhali akwai wani tare da shi a cikin ɗakin, ƙaramin
yaro ne ko babban mutum, kuma a farke ya ke ko yana barci.
A nan bai faɗi matsayin wannan hanin
ba.
Amma Al-Abbiy Al-Mutee’ Saalih
Abdussamee’ mai sharhin littafin shi ne ya bayyana hukuncin hanin, inda ya faɗa a sharhi, ya ce
فَيُكْرَهُ مَعَ
النَّائِمِ وَالصَّغيرِ، وَيُمْنَعُ مَعَ الْيَقْظَانِ الْكَبِيرِ
Don haka, an karhanta shi tare da
mai barci da ƙaramin yaro, kuma an hana shi tare da babban da ya ke a farke.
(Al-Muqaddimatul Iziyyah Lil Jamaa’atil
Azhariyyah, shafi: 206).
Wato, ya raba wannan mas’alar
gida biyu ne:
1. Idan akwai yaro ƙarami
a farke a cikin ɗakin,
ko babban mutum mai barci, to saduwar makaruhiya ce.
2. Idan kuma akwai babba ne wanda
ya ke a farke, to sai kawai ya ce: ‘An hana.’
Bai bayyana nau’in hanin ba: Na
haramci yake nufi, ko kuwa na karhanci ne? Amma ganin yadda ya raba mas’alar
gida biyu, ya rabe magana ta-biyu daga ta-farko, kuma har ya ba waccan ɗin hukuncin karhanci,
wannan kamar ishara ce ga cewa hani na haramci yake nufi da maganarsa ta-biyu.
Domin idan ba haka ba, to da rarrabewar ba ta da wata fa’ida kenan. Wallahu
A'alam.
Ɗaukar hanin a matsayin na haramci shi ya
fi natsar da zuciya, domin dalilai daga nassoshin shari’a abin da suka nuna
kenan, kamar maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa
»احْفَظْ
عَوْرَتَكَ إِلاَّ مِنْ زَوْجَتِكَ أَوْ مَا مَلَكَتْ يَمِينُكَ «
Ka tsare al’aurarka sai dai daga
matarka ko kuyangarka. (Sahih Abi-Daawud: 4017, Sahih At-Tirmiziy: 2794,
Sahih Ibn Maajah: 1920).
Sannan kuma da maganarsa cewa
»لاَ
يَنْظُرُ الرَّجُلُ إِلَى عَوْرَةِ الرَّجُلِ وَلاَ تَنْظُرُ الْمَرْأَةُ إِلَى عَوْرَةِ الْمَرْأَةِ «
Kar wani namiji ya kalli al’aurar
wani namiji, kuma kar wata mace ta kalli al’aurar wata mace. (Sahih Muslim:
338, Sahih Abi-Daawud: 4018, Sahih At-Tirmiziy: 2793).
Malamai sun haɗu a kan cewa: Wannan
hanin na haramaci ne. Wato, haram ne a wurin dukkan malamai: Namiji ya kalli
al’aurar wani namiji, ko mace ta kalli al’aurar wata mace. Kuma wanda ya fi
tsanani shi ne: Namiji ya kalli al’aurar wacce ba matar aurensa ta Sunnah ba,
ko mace ta kalli al’aurar wani namijin da ba mijin aurenta na Sunnah ba.
(Al-Imaam Abu-Zakariyya Yahya Bn Sharf An-Nawawiy a cikin Sharhu Muslim:
(4/30), da Abut-Tayyib Muhammad Shamsulhaqqil Azeem Abaadiy a cikin Aunul Ma’buud:
(11/40) sun ambato wannan ijma’in).
A taƙaice dai tun da kallon
al’aura haramun ne,
wannan ya nuna kallo ko sauraron yadda ma’aurata - ko waɗanda
ba su ba - suke aikata saduwar, shi ne yafi tsanani wurin haramci. Ko da kuwa
yara ƙanana
ne suke ji da ganin hakan, balle kuma manya.
Dole ne iyaye su san cewa: Yana
da matuƙar
hatsari su riƙa bari yaransu ƙanana suna ji ko ganin yadda ake aikata
hakan, ko daga ko’ina
ne ma ba wai daga gare su kaɗai
ba. Kuma ba wai sai a lokacin da yaran suke tare da su a cikin ɗaki ba. A’a, ko da ba a
cikin ɗakin su ke
ba, kamar ta hanyar leƙe daga nesa, ko ta hanyar na’urar ɗaukan
hoto da makamantan hakan! Domin sakaci a kan wannan na iya haifar wa yaran da
mummunan sakamako a cikin rayuwarsu.
Kwanan baya a cikin social media
an tattauna da wani wanda masifar aikata fyaɗe
ta yawaita daga gare shi. A cikin maganganunsa ya bayyana cewa, matsalarsa ta
fara ne daga yadda mahaifiyarsa take barin tsiraicinta a buɗe a gabansa a lokacin da
take wanka ko kwalliya tun yana ƙaramin yaro! Wai daga nan ne ya zama yana
sha’awar ganin
tsiraicin mace a lokacin da ya girma!
Mu kuwa - Alhamdu Lil Laah - an
kare mu daga irin waɗannan
masifun tun tuni. Domin Manzon Allaah Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya koyar da mu kyawawan ladubba na musulunci, kamar waɗannan
»مُرُوا
أَوْلاَدَكُمْ بِالصَّلاَةِ وَهُمْ أَبْنَاءُ سَبْعِ سِنِينَ وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا وَهُمْ أَبْنَاءُ عَشْرِ سِنِينَ وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِى الْمَضَاجِعِ «
Ku umurci ’ya’yanku da yin sallah
a lokacin suna ’yan shekaru bakwai, kuma ku buge su a kan ta a lokacin da su ke
’yan shekaru goma, kuma ku rarrabe a tsakaninsu a wurin kwanciya. (Sahih
Abi-Daawud: 495).
Malamai sun ce: An ɗauki wannan mataki mai
tsanani ne a kan yaran da ba su kai lokacin balaga ba, duk kuma da kasantuwar
su ’yan uwa ne, domin a kare su daga sharrin muguwar sha’awar jima’i tun suna ƙanana.
(Aunul Ma’buud:
2/115).
Tun da kuwa haka abin ya ke, ashe
ya zama dole iyaye su ɗauki
dukkan matakan kare ’ya’yansu daga wannan masifar, kamar ta hana su ganin hakan
daga ko’ina ma, balle kuma daga gare su su da kansu.
Kamar yadda wani malami ya taɓa cewa ne: Duk wanda ya
tashi a wannan yankin na Arewa a cikin gidaje irin na musulmi kuma har ya kai
kamar shekaru arba’in a yau, abu ne mawuyaci ya iya shedar cewa ya taɓa ganin lokacin da ɗaya daga cikin iyayensa
ya ɗauki buta ya
kewaya domin yin wankan janaba, balle kuma ya ce ya taɓa ganin lokacin da suke aikata saduwar! Duk
kuwa da kasantuwa a tare da su yake rayuwa, kuma - a galibi - tare da sauran
yayyi da baffanni da ’ya’yansu a cikin gidan. Ga kuma irin ƙuncin
rayuwar da kowa ya san ya fi na yau nesa ba kusa ba.
To, meyasa a lokacin suka iya
kare waɗannan
abubuwan daga idanu da kunnuwan ’ya’yansu, mu kuma a yau muka kasa?
Me yake hana mu iya koyi da irin
waɗannan kyawawan
halayen na musulunci daga iyayenmu da magabatanmu?
Allaah ya faɗakar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.