𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam, wanda ya
yi alwala zai je masallaci sai wata mace kirista ta taɓa shi, kamar a hanu ko a kafaɗarsa, to yaya hukuncin ya
ke?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Da farko, wajibi ne musulmi ya
kare kansa daga duk abin da ka iya zubar masa da mutunci. Bai halatta ba
musulmi baligi mai hankali ya bari har wata macen da ba muharramarsa ba ta
shafi jikinsa hakan nan ba tare da wata larura ba, kuma ko ita musulma ce ko ba
musulma ba ce. Wanda ya fi tsanani kuma shi ne mace musulma baliga mai hankali
ta bari wani namijin da ba muharraminta ba ya shafi jikinta. Dalili kuwa shi ne
maganar Allaah Ubangijin Halittu cewa
وَلَا
تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا
Kuma kar ku kusanci zina, haƙiƙa
ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa’: 32)
Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« كُتِبَ عَلَى ابْنِ آدَمَ نَصِيبُهُ مِنَ الزِّنَى مُدْرِكٌ ذَلِكَ لاَ مَحَالَةَ ، فَالْعَيْنَانِ زِنَاهُمَا
النَّظَرُ ، وَالأُذُنَانِ زِنَاهُمَا
الاِسْتِمَاعُ ، وَاللِّسَانُ زِنَاهُ
الْكَلاَمُ ، وَالْيَدُ زِنَاهَا
الْبَطْشُ ، وَالرِّجْلُ زِنَاهَا
الْخُطَا ، وَالْقَلْبُ يَهْوَى
وَيَتَمَنَّى ، وَيُصَدِّقُ ذَلِكَ
الْفَرْجُ وَيُكَذِّبُهُ »
An ƙaddara wa kowane ɗan Adam rabonsa na zina, kuma babu makawa
sai ya riske shi. Su dai idanu zinarsu ita ce: Kallo; kunnuwa kuma zinarsu ita
ce: Sauraro; harshe kuma zinarsa ita ce: Magana; hannu kuwa zinarsa ita ce:
Kamawa; ƙafa
kuwa zinarta ita ce: Takawa, kuma zuciya ita ke sha’awa kuma take buri. Farji kuma shi ke gaskata hakan ko
kuma ya ƙaryata
shi. (Sahih Muslim: 2657)
Bayar da sunan zina ga kamawa ko
shafa jikin wanda ko wadda ba ta halatta ba da hannu ya nuna shi zunubi ne,
kodayake ba babban kaba’irin zunubi ba ne. Allaah ya kiyaye.
Kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
«لَأَنْ يُطْعَنَ فِي رَأْسِ رَجُلٍ بِمِخْيَطٍ مِنْ حَدِيدٍ ، خَيْرٌ لَهُ
مِنْ أَنْ يَمَسَّ امْرَأَةً لَا تَحِلُّ لَهُ»
A soka wa mutum allura ta baƙin ƙarfe
(misilla) a tsakiyar kansa, shi ya fiye masa alheri da a ce ya shafi jikin
macen da ba ta halatta gare shi ba. (Silsilah Sahihah: 226)
Allaah ya ƙara kiyaye mu.
Amma game da hukuncin alwalarsa a
bayan hakan ya auku, akwai mahanga guda biyu
1. Idan babu wani abu da ya fito
masa kamar maziyyi ko maniyyi a sakamakon hakan, to alwalarsa ba ta ɓaci ba. Domin hadisi ya
tabbata daga A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) cewa, Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
كَانَ يُقَبِّلُ
بَعْضَ أَزْوَاجِهِ ، ثُمَّ يُصَلِّى
وَلاَ يَتَوَضَّأُ
Ya kasance yana sumbantar wata
daga cikin matan aurensa, sannan ya yi sallah ba tare da ya sake alwala ba.
(Sahih An-Nasaa’iy: 170; Sahih Ibn Maajah: 502).
Kuma abu ne sananne cewa, a
galibi sumba irin wannan tana tare da sha’awa ne.
2. Amma idan wani abu ya fito
masa a sakamakon shafan, to a nan ne malamai suka ce alwalarsa ta ɓaci, saboda dalilin abin
da ya fito amma ba domin shafar ba. A nan malamai sun kafa dalili ne da hadisin
Aliyu Bn Abi-Taalib (Radiyal Laahu Anhu) da ya ce: Na kasance mutum ne mai
yawan fitan maziyyi, sai na umurci wani mutum ya tambayi Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan haka saboda matsayin ’yarsa a wurina. Sai ya ce
« تَوَضَّأْ وَاغْسِلْ ذَكَرَكَ »
Ka wanke al’aurarka, ka sake
alwala. (Sahih Al-Bukhaariy: 269; Sahih Muslim: 303)
Sannan kuma abin da ya inganta
daga Abdullaah Bn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce
الْمَنِيُّ وَالْوَدْيُ
وَالْمَذْيُ ، فَأَمَّا الْمَنِيُّ
فَفِيهِ الْغُسْلُ ، وَأَمَّا الْمَذْيُ
وَالْوَدْيُ فَفِيهِمَا الْوُضُوءُ ، وَيَغْسِلُ ذَكَرَهُ.
Maniyyi da wadiyyi da maziyyi ne.
Shi dai maniyyi shi ne wanda ake yin wanka saboda shi, su kuwa maziyyi da
wadiyyi sai ya wanke al’aurarsa ya sake alwala. (Ibn Abi-Shaibah: 989)
Amma maganar da waɗansu malamai suka yi
cewa, shafar mace yana karya alwala, saboda maganar Allaah Ta’aala cewa
أَوۡ
لَـٰمَسۡتُمُ ٱلنِّسَاۤء
Ko kuma idan kun yi shafar juna
da mata. (Surah Al-Maa’idah: 6)
Wannan ba daidai ba ne. Domin ma’anar
maganar a nan ita ce: Saduwar jima’i kawai. Haka Ibn Abi-Haatim ya riwaito ta
daga Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) da wani isnadin da Al-Haafiz Ibn Hajr
(Rahimahul Laah) a cikin Fat-hul Baariy: 8/272 ya ce: Sahihi ne.
Sannan kuma a cikin (Fat-hul
Baariy: 8/158, 372) ya sake ambatowa sannan ya inganta riwayar da Abdurrazzaaq
ya kawo daga Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ɗin
dai cewa
إِنَّ اللهَ
حَيِّيٌ كَرِيمٌ يُكَنِّي عَمَّا شَاءَ ، الدُّخُولُ وَالتَّغَشِّي
وَالافْضَاءُ وَالْمُبَاشَرَةُ وَالرَّفَثُ وَاللَّمْسُ: الْجِمَاعُ
Haƙiƙa Allaah Mai Kunya ne Mai Karimci: Yana
yin kinaya a kan duk abin da ya so. Ad-Dukhuulu, da At-Taghasshiy, da Al-Ifdaa’u, da Al-Mubaasharah, da
Ar-Rafthu, da Al-Lamsu duk ma’anarsu
kenan: Saduwar Jima’i.
Haka nan kuma maganar Ubangiji
Ta’aala cewa
إِنَّمَا ٱلۡمُشۡرِكُونَ
نَجَسࣱ
Kaɗai
su mushirikai najasa ne kawai. (Surah At-Taubah: 28).
Wannan ma ba dalili ne a kan
cewa, idan kirista ya shafi jikin mutum to ya shafa masa najasa ne ba. Domin
ingantacciyar fassarar ayar a wurin malamai ita ce: Su najasa ce ta ma’ana
kawai saboda mummunar aƙidarsu, amma ba najasa ce ta haƙiƙa ba. Shiyasa ba a taɓa ji ko ganin inda Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi umurni da a zuba ruwa a
wanke inda mushirikai ko Yahudawa suka zauna ko suka shafa a cikin masallacinsa
mai alfarma ba, irin yadda ya bayar da umurni da a zuba ruwa a kan fitsarin da
baƙauye
ya yi a masallacinsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 219).
Allaah ya ƙara mana fahimta a
cikin addininmu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.