Ticker

6/recent/ticker-posts

Sallah A Kan Kujera

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ba na iya lanƙwashe ƙafata saboda rashin lafiya, don haka nake yin sallah a kan kujera da nuni, amma sai aka ce wai sai dai in yi a ƙasa saboda sujada dole ce, kuma zan iya. Wanne ne daidai?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Dokokin Shari’ar musulunci an ɗora su ne a kan musulmi ya aikata su da gwargwadon ƙarfi da ikonsa. Allaah Taaala ya ce

فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُم 

Sai ku tsare dokokin Allaah daidai iyawanku. (Surah At-Taghaabun: 16).

Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَىْءٍ فَاجْتَنِبُوهُ ، وَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِأَمْرٍ فَأْتُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ »

Idan na hana ku wani abu, to ku nisance shi. Idan kuma na umurce ku da wani abu, sai ku zo da gwargwadon iyawarku daga cikinsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 7288; Sahih muslim: 6259).

Wannan a dunƙule kenan.

Amma a kan sallah a keɓance kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fayyace komai, a inda ya ce

« صَلِّ قَائِمًا ، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَقَاعِدًا ، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَعَلَى جَنْبٍ »

Ka yi sallah a tsaye, idan kuwa ba za ka iya ba, to a zaune. Idan kuma ba za ka iya ba, to a gefen jiki (a kwance). (Sahih Al-Bukhaariy: 1117).

Sannan kuma Abdullaah Bn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ya ce

 كَانَ النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - يُصَلِّى فِى السَّفَرِ عَلَى رَاحِلَتِهِ ، حَيْثُ تَوَجَّهَتْ بِهِ ، يُومِئُ إِيمَاءً ، صَلاَةَ اللَّيْلِ إِلاَّ الْفَرَائِضَ ، وَيُوتِرُ عَلَى رَاحِلَتِهِ .

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance yana yin sallah a cikin halin tafiya a kan taguwarsa duk ta inda ta fuskanta da shi, yana yin ishara da kansa, a sallar dare sai dai farilla. Kuma yana yin wutri a kan taguwarsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 1000).

Wannan ya nuna, idan mutum ba zai iya yin ruku’u ko sujada ba, to sai ya yi nuni da kansa a maimakon ruku’u da sujadar.

Kamar dai yadda Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) ɗin dai ya ƙara bayanin wannan abin a cikin wata riwayarsa mai cewa

عَادَ رَسُولُ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - رَجُلًا مِنْ أَصْحَابِهِ مَرِيضًا، وَأَنَا مَعَهُ فَدَخَلَ عَلَيْهِ، وَهُوَ يُصَلِّي عَلَى عُودٍ فَوَضَعَ جَبْهَتَهُ عَلَى الْعُودِ فَأَوْمَأَ إِلَيْهِ فَطَرَحَ الْعُودَ وَأَخَذَ وِسَادَةً فَقَالَ رَسُولُ اللهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -: «دَعْهَا عَنْكَ إِنِ اسْتَطَعْتَ أَنْ تَسْجُدَ عَلَى الْأَرْضِ، وَإِلَّا فَأَوْمِئْ إِيمَاءً، وَاجْعَلْ سُجُودَكَ أَخْفَضَ مِنْ رُكُوعِكِ»

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya je duba wani mutum mara lafiya daga cikin sahabbansa, alhali ina tare da shi a lokacin. Sai ya shiga wurinsa ya tarar da shi yana sallah a kan wata sanda, yana ɗora goshinsa a kan sandar. Sai ya yi masa ishara, sai ya jefar da sandar. Sai kuma ya ɗauki matashin kai. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Ka aje wannan shi ma: Idan za ka iya yin sujada a kan ƙasa, ka yi. Idan kuwa ba za ka iya ba, sai ka yi nuni (ishara). Ka sanya sujudarka ta fi rukuunka yin ƙasa. (At-Tabaraaniy ya riwaito shi a cikin Al-Muujamul Kabeer: 13082).

A cikin Al-Silsilatus Saheehah: (323) Al-Albaaniy ya ce

هَذَا إسْنَادٌ صَحِيحٌ رِجَالُهُ كُلُّهُمْ ثِقَاتٌ

Wannan isnadi sahihi ne, mazajensa dukkansu amintattu ne. (As-Saheehah: 1/577).

Shi kansa Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhu) ɗin ya yi aiki da wannan hadisin a lokacin da ya shiga wurin Hafs Bn Asim don duba shi a kan rashin lafiyar da ke tare da shi, kuma ya tarar ya shimfiɗa wani ƙyalle a kan matashin kai yana yin sujuda a kansa, sai ya ce

يَا ابْنَ أَخِي لَا تَصْنَعْ هَذَا ، تَنَاوَلِ الْأَرْضَ بِوَجْهِكَ ، فَإنْ لَمْ تَقْدِرْ عَلَى ذَلِكَ ، فَأَوْمِئْ بِرَأْسِكَ إيمَاءً

Ya kai ɗan gidan ɗan’uwana, kar ka aikata haka. Ka shafi kan ƙasa da goshinka, idan kuma ba za ka iya ba sai ka yi ishara da kanka. (Musnad Abi-Awaanah: 2/338).

Al-Albaaniy a cikin As-Saheehah ya ce

سَنَدُهُ صَحِيحٌ عَلَى شَرْطِ الشَّيْخَيْنِ

Isnadinsa sahihi ne a kan sharaɗin Al-Bukhaariy da Muslim.

Saboda waɗannan hadisai da atharai ne wataƙila malamai suka ce:

إِذَا تَعَذَّرَ عَلَى الْمُصَلِّي صِفَةٌ مِنْ صِفَاتِ صَلَاةِ الْعَلِيلِ الْوَارِدَةِ، أَتَى بِالصَّلَاةِ عَلَى صِفَةٍ أُخْرَى مِمَّا وَرَدَ، ثُمَّ يَفْعَلُ مَا قَدَرَ عَلَيْهِ وَدَخَلَ تَحْتَ اسْتِطَاعَتِهِ.

Idan mai sallah ya kasa yin sallah a kan wata siffa daga cikin siffofin sallar mara lafiya da suka zo a cikin riwayoyi, sai ya aikata sallar a kan wata siffa daga cikin waɗanda aka kawo a hadisai. Sai kuma ya aikata abin da yake da iko a kansa, kuma abin da ya shiga ƙarƙashin iyawarsa. (At-Taaleeqaatur Radiyyah: 1/312).

A ƙarƙashin waɗannan nassoshi da bayanai a taƙaice, za mu iya cewa ya halatta ga wanda ba ya iya lanƙwanshe ƙafarsa ya yi sallarsa ko dai a zaune a kan ƙasa, kamar yadda hadisin wanda aka hana shi sujada a kan matashin kai ya nuna. Ko kuma ya yi sallar a zaune a kan kujera, kamar yadda hadisin sallarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan taguwa ya nuna. A duk waɗannan halayen yana duƙawa da yin ishara ne da kansa a maimakon rukuu da sujada.

Kodayake sallar nafila ce kaɗai a halin tafiya hadisin yin sallah a kan taguwa ya nuna, amma dai malamai sun yarda cewa, idan larura ta kama mutum yana iya yin farillar ma a kan abin hawar, kamar idan ya ji tsoron ficewar lokaci, ko tsaron rasa abokan tafiya, ko kuma salwantar rayuwa ko dukiya idan ya tsaya don yin sallar a ƙasa.

Idan haka ne kuwa, ashe wanda larurarsa ta fi hakan, watau kamar wanda ba ya iya lanƙwashe ƙafarsa, watau wanda ba ya iya yin sujada daidai alhali yana zaune da ƙafarsa a miƙe, ko wanda ba ya iya zaman sallah daidai sai dai ya miƙe a kan gwiwoyinsa da ya kafa su a kan ƙasa, irin wannan shi ma ba za a hana shi yin sallarsa daga zaune a kan kujera ba, yana mai yin nuni da bayansa da kansa a maimakon rukuu da sujada, in shà Allâh.

Yin sallar a kan kujera kamar yadda muka bayyana a sama, shi ya fi kama da surar sallar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi a kan raƙumi. Wannan kuwa shi ya fi miƙewa a kan gwiwoyinsa a wurin zama a tsakanin sujuda biyu da zaman tahiya, kamar yadda yawancinsu suke aikatawa a masallatai.

Allaah ya ƙara mana fahimta a cikin addininmu.

WALLAHU A'ALAM 6

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments