Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saduwa Da Matar Da Ba Kwananta Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam shin ya halatta na sadu da ɗaya daga cikin matana koda ba ranar kwananta bane?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

A'a bai halatta ba. Domin hakika yin hakan yana daga cikin  zalunci. Kuma Allah (SWT) ya wajabta yin adalci ga duk wanda zai zauna da mata. Allah yace :

 فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا

Ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'annan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka (baiwa). Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. (Suratun-Nisa'i 3)

Wato wajibi ne ka raba lokutanka a tsakanin matanka daidai da daidai. Kada ka sadu da wata daga cikinsu sai aranar girkinta. Kuma wajibi ne ka basu abinci, sutura, muhalli, bisa adalci gwargwadon damar da Allah ya huwace maka.

Haƙƙin miji ne kar ya sadu da wata daga cikin matansa sai wacce ita ce ke da kwana, ko kuma idan akwai amincewa da yarda daga wacce ta ke da kwanan. Yana iya shiga wurin matarsa da ba ita ce mai girki ba da rana idan akwai larura, kamar bayar da kuɗin cefane, ko binciken lafiyarta, ko warware wata matsala da makamatan haka. Bai halatta ya sadu da wacce ba kwananta ko girkinta ba a lokacin da ya shiga wurinta don wata buƙata daga cikin buƙatun da ambatonsu ya gabata. Haƙƙin mata ne kar ta yarda mijinta ya sadu da ita idan dai ba kwananta ba ne, ko in ba da izinin wadda ta ke da kwanan ba.

Idan har kasan ba zaka iya yin adalci atsakaninsu ba, to bai halatta ka Qara auren ba. Domin hakika Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: "Wanda ya kasance yana da Mata biyu, sai ya karkata zuwa ga ɗayar cikinsu, to zai zo aranar Alqiyamah alhali tsagin jikinsa ya karkace (wato ya shanye, yana tafiya a tazgade). Tirmidhiy da Nisa'iy da Abu Dawud da Ibnu Maajah ne suka ruwaitoshi.

A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce

كَانَ رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - لاَ يُفَضِّلُ بَعْضَنَا عَلَى بَعْضٍ فِى الْقَسْمِ ، مِنْ مُكْثِهِ عِنْدَنَا ، وَكَانَ قَلَّ يَوْمٌ إِلاَّ وَهُوَ يَطُوفُ عَلَيْنَا جَمِيعًا ، فَيَدْنُو مِنْ كُلِّ امْرَأَةٍ مِنْ غَيْرِ مَسِيسٍ ، حَتَّى يَبْلُغَ إِلَى الَّتِى هُوَ يَوْمُهَا ، فَيَبِيتُ عِنْدَهَا

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance ba ya fifita sashenmu a kan sashe wajen rabon-kwana, a iya zamansa a cikinmu; kuma da ƙyar wani yini guda ke wucewa face kuwa ya kewaya mu gaba-ɗaya, kuma ya kusanci kowace mace amma ba tare da saduwa ba, har sai ya kai ga mai girki a ranar, sai ya kwana a wurinta. (Abu-Daawud: 2137 ya riwaito shi).

Don haka mazaje masu yin irin wannan zalunci ga matayensu ana ji masu tsoron faɗawa cikin irin wannan mummunan hali, saboda Allah ba ya zalunci, kuma ya haramta a yi zalunci, don haka mu ji tsoron Allah mu yi adalci a tsakanin iyalanmu. Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6qgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments