Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Rike Hannu A Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam don Allah a warware mana abin da wannan matar take cewa : Ita maganar rike hannu a salla sunna ce ta shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam. haka nan sakin hannu kamar da yake a bukhari da muwadda duk sun nuna cewa Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam a farkon rayuwarsa ya saki hannunsa a Sallah, daga baya ya kama hannu daga Karshen Rayuwarsa ya cigaba da sakin hannu, to kunga sunnar da Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam yayi sau biyu tafi wadda yayi sau ɗaya. Imamu Malik Imamu Darul hijra a mazhabarsa rike hannu a Sallar Farilla Makruhi ne kuma shine Malamin sauran malaman mazhabar da Saudiyya take bi, don haka sakin hannu bazai zamo bidi'a ba, kuma ba zamu nunawa imamu Malik sanin Sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ba. Ya kamata jama'a musan cewar in mutum bai rushe mana abinda muke kai ba, be kamata mu, mu rushe masa nasa ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To 'yar'uwa rike hannu a sallah Sunnah ne kamar yadda Wa'il ɗan Hujr ya rawaito ya ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana yi a cikin sallah, kamar yadda ya tabbata a SAHIHI Müslim a hadisi mai lamba ta: 401.

Babu ko hadisi guda ɗaya Wanda ya tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana sakin hannu a sallah, ko da a kaddara ya saki a farkon musulunci daga baya ya rike, sakın ba zai zama Sunnah ba, tun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana aiki ne da wahayi, wahayi kuma a hankali yake zuwa, kamar yadda ba'a shar'anta sallah ba sai a daren Isra'i, babu kuma wanda zai ce barin sallah ya halatta tunda babu ita a farkon musulunci.

An rawaito riwayoyi daban-daban daga Imamu Mâlik akan rike hannu a sallah, daga ciki akwai riwayar Ibnul-kasim a Mudawwanah waccce take nuna hallacin rike hannu a Nafila da kuma karhancin rikewa a Farilla, akwai kuma riwayar Ashhabu da Muddarif da Abdulmalik da Ibnu Nafi'i daga Imamu Malik wacce take nuna halarcin rikewa a Farilla da nafila, kamar yadda Ibnu Abdul Barr ya ambata a Istizkar 2/291 da kuma kuma mai littafin Albayan wattahsi a l /394.

Imamu Mâlik ya rawaito hadisin rike hannu a sallah a cikin Muwadda, a lamba ta : 290, saidai wasu malaman suna cewa ya karhanta rikewa a cikin sallar farilla ne a riwayar Ibnul-Kasim saboda ya saɓawa aikin mutanan Madina.

Duk da kasancewar Imamu Mâlik bajimin malami mai tsoron Allah, saidai a matsayinsa na ɗan adam yana iya yın kuskure, sannan wasu hadisan da ayyukan sahabbai suna iya ɓuya gare shi, kamar yadda ya tabbatar da hakan a maganganunsa, wannan yasa lokacin da halifan zamaninsa ya so ya iyakance aikin mutane a hadisan da suka zo a Muwadda, Imamu Malik ya hana shi, ya kafa hujja da cewa: a wajan malaman Madina kawai ya yi karatu, akwai wasu malaman da bai haɗu da su ba.

Rike hannu a sallah Sunnah ce tabbatacciya daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam kuma hakan shi ne aikin mafi yawan sahabbai da tabi'ai da manyan malamai, ba za'a barta saboda wani malami ba, tare da cewa : wanda ya saki hannu a sallah, bai yi laifi ba, kuma sallarsa ta yi.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments